1. Nasara da faɗuwar sana’ar ka sun dogara da jama’a ne. Bincike ya nuna cewa sana’o’i na karyewa kaso 36 cikin 100 saboda rashin kasuwa, ko rashin lissafi mai inganci, ko rashin daraja. Kaso 64 cikin ɗari na dalilan da sana’o’i ke karyewa saboda jama’a ne. Ta yiwu rashin jituwa ne tsakanin waɗanda suka yi haɗaka wajen fara sana’ar, ko neman ƙarfin iko, ko kuma samun mai sana’a wanda ba ya ɗaukar shawara.
Marubuci: Bello Galadanchi
2. A rubuta yarjejeniyar ƙulla alaƙa da abokan sana’a a karon farko. Wannan zance da na yi na iya saka jama’a jin banbaraƙwai, amma akwai matuƙar muhimmanci a yi ta kafin ku fara samun kuɗi, har ku gano inda ribar ku ta fi fitowa.
Kar ku yi saurin yin raba daidai, ku fahimci gudummuwar da kowa zai iya kawowa tukunna. Idan an fahimci haka, to a saka hannu akan takarda domin kowa ya samu shaida. Za’a iya tsara wannan yarjejeniya ta yadda za’a iya dawowa a yi mata garambawul.
3. Ka fahimci mene ne sana’ar ka, sannan ka iya tallata ta. Talla shi ne muryar sana’a, kuma sana’ar da ba ta da murya kamar tsuntsun da ba shi da fuffuke ne, ba zai iya tashi ba.
4. Ka fara da sana’ar hannu, kafin kai wa ga saye da sayarwa. Yawanci za ka iya farawa babu jari, kuma zai ba ka horo na riƙe sana’a yau da gobe. Abin da ka tara sai ka yi amfani da su wajen bunƙasa sana’ar ka ta yin talla da ma saye da sayarwa.