Showing posts with label Sirrin Kasuwanci Da Na Sana'a. Show all posts
Showing posts with label Sirrin Kasuwanci Da Na Sana'a. Show all posts

Saturday, 25 October 2025

Sirrika 5 Da Masu Kudi Da Kwararru Ba Sa Bayyanawa

Sirrika 5 Da Masu Kudi Da Kwararru Ba Sa Bayyanawa

Babban abin da yakamata mu fara la'akari da shi shi ne, yawan jari ko kalar sana'a ba shi zai tara maka kuɗi ba. Da yawan mutane suna gabatar da wani aiki ko sana'a, amma kuma ba sa samun irin kuɗaɗen da suke buƙata na rayuwa.


Sirrika 5 Da Masu Kuɗi Da Kwararru Ba Sa Bayyanawa 
Hoto: Albert shakirov/Dreams time

Marubuci:- Bello Ado Hussaini



To yaya kuma ga wanda zai fara sana'ar yanzu, har yake tsammanin da zarar ya fara sai kuɗi su yi ta shigowa?


Duk wanda ya gina sana'a ko kasuwanci, ya san irin ƙalubalen da ya fuskanta, kuma idan kasuwancin nasa ya tsaya yana kawo riba, ya san hanyoyin da ya bi, da kuma wasu dabaru da ya riƙe, a matsayin sirrin neman sa.


Sai dai bisa ɗabi'ar mutanen mu, da wuya mutum ya gaya ma irin dabarun nasa, musamman idan ya zama sana'ar ku iri ɗaya ce, ko kuma kasuwa ɗaya kuke ci.


Masu kuɗi da waɗanda suka samu nasara a kasuwanci da sana'a, sun fahimci cewa, babu wani wanda yake son rabuwa da kuɗinsa haka kawai.


Sai dai akwai wasu buƙatu da domin su ma yake tara kuɗaɗen sa, kuma a shirye yake ya biya kuɗi domin biya masa waɗannan buƙatu.


Masu kuɗi sun gane cewa, zuba kuɗin su a irin waɗannan buƙatu na al'umma, ko kuma samar da sana'a wacce za ta magance matsalolin waɗanda suke da kuɗin biya, hanya ce miƙaƙƙiya ta gina arziki.


Sun gane cewa akwai buƙatun da dole a zo neman su, kuma da zarar ka shirya yadda za ka magance waɗannan buƙatu, mutane za su yi ta layi suna biyan ka kuɗade, domin warware musu damuwarsu, ko kuma buƙatar su.


Abin da yakamata mai sana'a ko kasuwanci ya fahimta shi ne, wacce irin matsala ko buƙata yake iya warwarewa a cikin aikinsa, saɓanin abokanan kasuwancin sa.


Akwai abubuwa da yawa da za'a iya duba zuwa gare su, amma bari mu kawo kaɗan daga ciki;


1. ƘARANCI


Wannan yana nufin wani abu na buƙatar rayuwa ya yi ƙaranci ko wahala, kai kuma sai ka nemo shi duk inda yake, ko kuma ka samar da shi.


Hakan zai zama dole mutane su biya ka ladar ka, domin ka samar da abin da suke buƙata, yayin ƙaranci.


2. LOKACI


Mutane suna da buƙatu, amma a mafi yawa, buƙatun nasu suna da lokaci.


Matsawar ba za ka iya biya musu buƙatunsu akan lokacin da suke buƙata ba, tabbas za su rabu da kai da kayan ka, ka yi ta hamma ba ciniki.


Wannan ce tasa yanzu da yawa, za ka ga ana yawan tallata kaya, tare da cewa za mu iya kawo maka kayan inda kake, kuma sai ka gani sannan ka biya.


Akwai kuma abubuwan da suke da kaka, wato ƙayyyadadden lokaci, duk wanda ya kawo kayan sanyi cikin tsananin zafi, ya san sai dai ya kai su ma'ajiya.


3. FARASHI


Kusan duk abin da mutum zai saya, kafin ya zo kasuwa ya ƙulla a zuciyar sa farashin da zai iya biya.


Saɓanin wannan zai iya fasa buƙatar, ba don ba shi da kuɗin ba, sai dai buƙatar ba ta kai wannan farashin ba a gurin sa.

Wajibi ne ka warware matsala a farashin da masu buƙata za su iya biya.


Idan farashin ka ya zarta waɗanda kake tare da su, ya zama wajibi ka nemi sabbin abokan hulɗa. 


Wannan shi zai kai mu ga mataki na gaba a ƙasa.


4. MUHALLI


Wannan kamar yadda na zayyana a sama yana da alaka da irin matsalar da za ka warware, su wa za ka warwarewa, kuma a wane farashi.


5. GAMSARWA


Kamar yadda kowa ya sani, duk wanda zai rabu da kuɗinsa, so yake kuma ya rabu da matsalar da ta sa shi kashe kuɗin.


Don haka dole ne ka samar masa da abin da yake buƙata, har ya gamsu cewa biyan ka da ya yi bai yi kuskure ba.


RUFEWA


Wato gaba-ɗaya shi nema, ɗaukar ƙafa ne da kuma ɗaukar dama, abinda ake kira LEVERAGE.


Dole ne kake la'akari da buƙatun al'umma na ƙashin kansu, sai kuma yanayi da wani salo wanda ba kowa ya fahimce shi ba.


Wannan ce tasa za ka ga mutane masu sana'a iri ɗaya, wani lokacin a waje ɗaya, amma wani yana ta bunƙasa, wani kuma sai a hankali kawai.


Masu magana suna cewa, kowa ya ci Zomo, ya ci gudu tukunna.


Allah yasa mu dace Amin.

Saturday, 3 May 2025

Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari

Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari

 1. AIKIN ƘARFI 


Muna da misalai da yawa na mutanen da suka yi arziki, kuma sun fara neman kuɗi ba tare da wani ya ba su jari ba.


Za ka iya fara aikin ƙarfi, tun da ba ya buƙatar wani jari sai lafiyarka, idan ka adana wani adadin kuɗi, sai ka tsunduma cikin kasuwa.


Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Abubakar Abba


Amma idan ka zauna ka ce kana jiran wani ya ba ka ko kana jiran gwamnati ta ba ka jari, to alama ce da take nuna ba ka shirya rufawa kanka asiri ba.


2. NEMI UBANGIDA


Kowace sana'a tana buƙatar a koye ta a wajen wanda suka ƙware a cikinta, hakan yana ba wa mutum sani mai yawa, wanda idan ya zo ya samu jarin farawa da kansa, ba zai sha wahala ba.


Don haka, ka nemi wani mutumin ko abokinka wanda yake wata harkar kasuwar, ka zama yaronsa, koda aiken ka za'a yi  ko dakon kayan kwastoma a kasuwa, ko sayo kayan aiki ko wani abu makamancin haka, babu laifi.


Idan ka yi haƙuri mutane suka san ka a kasuwar, ko wajen aikin, lokaci zai zo da za ka iya samun 'yanci.


Zama yaron wani ba ya buƙatar sai kana da jari, hasali ma ita ce hanya mafi sauƙi ma wajen fara sana'a.


Sai dai ba kowa ne yake da wannan alfarmar ba.


3. SIYAR DA KANKA


Koda ba ka san kowa ba, ko ba ka da 'yan uwa a kasuwa, wannan ba zai zama uzurin da za ka ce ka rasa abin yi ba.


Yi amfani da Shafukan Sada Zumunta, ka zama mai ƙirƙirar maƙala wanda zai ja hankalin mutane, ka tara mabiya.


Yi amfani da wannan mabiyan ka je ka samu wasu 'yan kasuwar ka nuna musu cewa kana da mutane, su dinga ba ka talla, ko tsarin affliate ne, kai kuma kana samun wani abu.


Da yawan 'yan kasuwa za su ba ka wannan damar, domin zai kawo musu kwastomomi.


Ka je ka ɗauki hotuna da kanka, ka zo Shafukan Sada Zumunta ka fara tallatawa.


Wannan ma ba ya buƙatar sai kana da jari za ka fara.


4. KA YI AMFANI DA BASIRA


Wanda Allah ya sa yana da wata ƙwarewa ko wata baiwa, shi wannan nasa mai sauƙi ne.


Abin da ya rage maka shi ne, ilimin da kake da shi, da basirar da kake da ita, da wata ƙwarewa da kake da ita, ka fito da ita duniya ta sani, ka sanya farashin kuɗi mutane su biya ka koya musu.


Da haka za ka iya samun jarin fara duk sana'ar da kake buri.


Kuma sakamakon ilimin da kake bayarwa, wasu damarmakin za su zo maka, wasu Network ɗin za su ƙullu, da haka sai ka ga ka wuce wajen.


5. KA YI KARATU


Sau da yawa rashin bincike yake hana mutane da yawa samun wasu damarmakin. Don haka ka yi ƙoƙari ka inganta iliminka, da kuma mu'amalarka.


Ka yi ƙoƙari ka dinga halartar guraren ƙara ilimi, kamar tarukan kasuwanci, da taron ƙarawa juna sani, ka dinga halartar Online Classes, daga nan za ka iya samun wata fikira da za ka iya amfani da ita wajen rufawa kanka asiri.

Saturday, 26 April 2025

Dalilin Rashin Cinikin Ka

Dalilin Rashin Cinikin Ka

Na  farko a kasuwancin ka shi ne ka tabbatar ana buƙatar abin da kake kawowa kasuwa. Na biyu ka tantance masu buƙatar da yadda suke son kayan ka.


Dalilin rashin cinikin ka
Hoto: Flickr

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Mutane da yawa suna kukan rashin ciniki, wani lokacin sai a gaya musu wai ba su kaɗai ba ne, ai babu kuɗi a gari.


Amma mafi yawan lokaci kai ne ka kawo abin da kasuwa ba ta buƙata.


Wani lokacin kuma, rashin tantance masu buƙatar kayan ka (Target customers) da yadda za ka same su, shi ne babban dalilin rashin cinikin ka.


Me ya kamata ka yi?


Ka tabbatar akwai buƙatar abin da za ka kawo kasuwa, kuma ka tantance masu buƙatar, da ƙarfin aljihunsu, da kuma yadda za ka same su.


Don haka kana buƙatar ka yi nazari akan abubuwa guda 5;


1. Kaya ko sana'a.


2. Abokan ciniki.


3. Ƙarfin ajihun abokan hulɗa.


4. Wajen kasuwancin.


5. Talla da jan hankali.

Monday, 21 April 2025

Hanyoyi 12 Na Zuba Babban Jari Ga Mai Ɗaukar Albashi

Hanyoyi 12 Na Zuba Babban Jari Ga Mai Ɗaukar Albashi

Hanyoyi 12 na zuba jari ga mai aikin albashi, ko kuma mai son ƙarin kuɗin shiga daga gefe. Dukkannin waɗannan sana'o'i ana gudanar da su a ƙauyuka da biranen mu. Masu yi kuma suna samun alkhairi.


Hanyoyi 12 Na Zuba Babban Jari Ga Mai Ɗaukar Albashi
Hoto: Entrepreneur

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


1. Gidan haya ko Rumfa


Mutane suna ɗauka sai kana da maƙudan kuɗi sannan za ka shiga harkar gidan haya ko rumfa da sauran su.


Akwai gurare da dama da za ka mallaki gida na ƙasa da miliyan 5, kuma ake biyan ka haya, sannan darajar gidan tana ƙaruwa.


Bayan gida akwai rumfar kasuwa a ƙananun kasuwanni da za ka mallaka a ƙasa da miliyan 1, kuma ita ma a karɓi hayar ta.


Banda ƙananun shago-shago a guraren da ake sana'o'i.


Na ƙarshe akwai gurare da Gwamnati ke bayarwa tamfurare, wanda za ka biya kuɗi kaɗan, ka gyara kuma ka ba da shi haya.


2. Hayar kayan amfani


Akwai abubuwan amfani na yau da kullum, kamar kayan taron biki ko na siyasa. Irinsu kujeru da tebura da tantuna da kayan sauti. 


Na biyu akwai kayan gini kamar tsani (ladder) da sukafur (Scaffold) da wilbaro da shebur da kayan haƙa da sauran kayan Engineering.


Duka waɗannan kana iya samar da su ka ɗauki ma'aikaci wanda zai tafiyar da harkar.


Akwai arziki mai yawa a ciki, idan ka samu guri mai kyau, da kaya masu inganci.


3. Kiwon dabbobi na nama


Musamman kiwon shanu idan ka fahimce shi, kuma kana da guri da mai kulawa, hanya ce mai kyau ta samun kuɗaɗe baya ga sana'ar ka ko aikin da kake gabatarwa na kullum.


Kawai idan za ka fara ka tuntuɓi ƙwararru da wanda suka jima a harkar.


4. Lambun kayan marmari


Wannan wani nau'i ne na noma a sauƙaƙe, inda za ka samu gona ko fili, ka dasa 'ya'yan itace masu gajeren zango (Hybrid).


Irin waɗannan kayan marmari sukan ba da 'ya'ya sau biyu a shekara, kuma sukan zo da daraja.


Misalin irin su shi ne kamar gajeriyar gwanda (Dwarf papaya) da lemon tsami da sauran su.


A waje ɗaya akwai noman kankana da kokumba, duka ba su ɗaukar lokaci, kuma mai aikin albashi musamman zai iya gabatar da su a kwanakin ƙarshen mako, tare da abokin kulawa.


5. Harkar Gwangwan


Harkar Gwangwan ana yin ta ta wucin gadi, misali ka ƙulla alaƙa da masu samun kaya, wanda a mafi yawan lokaci ba kowa ke da wadataccen jari ba. 


Duk lokacin da aka samu kaya sai ka siya, ka samu sito ka ajiye.


Idan aka samu mai son irin wannan kayan za su neme ka, kuma ana samun alkhairi.


6. Sufuri


Wannan ba ta buƙatar fassara, akwai irinsu ƙurƙura ko keke nafef da kanta kanta da sauransu daidai jarin ka.


Abin da harkar sufuri take buƙata kawai abokan neman arziki na ƙwarai, da kuma tsari mai kyau.


7. Hannun Jari


Wannan yana buƙatar masana harkar wato Brokers, tare da fahimtar yadda hada-hadar hannun jari take.


Mafi muhimmanci a ciki shi ne, mai hada-hadar hannun jari, baya jiran sai ƙarshen shekara kamfani ta biya Dividend.


Yana bibiya ne idan ya sauka ya siya, idan ya hau kuma ya siyar kamar Forex Trading.


8. POS


Wannan ma ba shi buƙatar fassara. Sai dai da yake ba kai z aka zauna ba, akwai buƙatar ka fahimci harkar, kuma ya zamana kai kake ganin irin hada-hada (Transaction) din da ake yi ta wayarka, ma'ana alerts. 


Ta haka za ka riƙa sanin cinikin da aka yi a kullum, da kuma ribar da aka samu.


9. Kayan sanyi


Shi ma wannan a fayyace yake, magana ce ta ka san me ka siyo, kuma me aka siyar.


Sai wuri na jama'a mai kyau da tsari.


Sannan ka samu abokin neman arziki mai amana, ku yi tarayya.


10. Saye domin riba


Wannan wata hanya ce ta siyawa masu buƙatar kayayyaki kowanne iri ne, daga baya su biya ka, kamar yadda bankuna ke yi.


Idan mutum na son wayar hannu misali, sai ka siya masa, kuma ka ɗora riba.


Shi kuma ya biya ka daga baya.


Irin wannan ya haɗa da kayan amfanin gida kamar TV da Fridge da kayan sawa da na gini kamar siminti da kwanon rufi da sauransu.


Shi ma yana buƙatar shawarar ƙwararru da tsari kafin farawa.


11. Sayen kayayyaki


Wannan ya ƙunshi kamar kayan sana'a wanda za a siya wa mutum ya dinga amfani da shi wajen sana'ar sa, yana biya a hankali.


Misali kamar keken ɗinki (Sewing machine) ko Generator ko Mixer ta gidan burodi da sauransu.


12. Sayen kayan da aka tallata


Wannan ma wata hanya ce ta zuba jari da juya kuɗi domin riba.


Yadda ake yin ta kamar Gwangwan ne, sai dai ba ta da gefe.


Duk wani abu na amfani, mai rai ko mara rai, idan ka ji ana neman mai siya, kana iya biya, bayan ka binciki darajarsa a kasuwa, da kuma yanayin buƙatar sa ga jama'a.


Lokacin da farashi ya yi maka daidai ka siyar.


Allah ya sa mu dace.

Saturday, 15 March 2025

Mai Kasuwancin Yanar Gizo-gizo Lura Da Wannan

Mai Kasuwancin Yanar Gizo-gizo Lura Da Wannan

1. Idan ka na kasuwancin yanar gizo-gizo, ka kiyayi ajiye kaya ga wanda bai ba ka ko sisi ba, ƙarshe za su iya zama maka asara.


Mai kasuwancin yanar gizo-gizo lura da wannan
Hoto: Patrick George/Getty Images

MarubuciAnas Darazo


2. Ba kowane kwastoma ke bambamce taya kaya da sayan kaya ba, wani tayawa ce ta kawo shi amma zai ce ya saya, kai ɗan kasuwa kai ne za ka bambamce su.


3. Lallai za a ɓata maka rai a kasuwa, ka yi haƙuri gwargwadon yadda za ka iya amma ka ƙwaci kanka iya wuya, ta tsaya a bacin rai ban da asarar kuɗi.


4. Kwastomomi su gane 'yan kasuwa su ma mutane ne, tsoka ce a zuciyarsu, yadda ranku ke ɓaci idan an ɓata muku haka nan su ma nasu ke ɓaci, ku nuna tarbiyya kada ku ɓata mana, haka idan mun kasa jurewa mun ɓata muku ku yi haƙuri mu ma mutane irin ku ba daga wata duniya mu ke ba.