Saturday, 3 May 2025

Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari

Tura Wannan Zuwa Ga

 1. AIKIN ƘARFI 


Muna da misalai da yawa na mutanen da suka yi arziki, kuma sun fara neman kuɗi ba tare da wani ya ba su jari ba.


Za ka iya fara aikin ƙarfi, tun da ba ya buƙatar wani jari sai lafiyarka, idan ka adana wani adadin kuɗi, sai ka tsunduma cikin kasuwa.


Yadda Za Ku Fara Sana'a Ba Jari
Hoto: Deposit photos

Marubuci:- Abubakar Abba


Amma idan ka zauna ka ce kana jiran wani ya ba ka ko kana jiran gwamnati ta ba ka jari, to alama ce da take nuna ba ka shirya rufawa kanka asiri ba.


2. NEMI UBANGIDA


Kowace sana'a tana buƙatar a koye ta a wajen wanda suka ƙware a cikinta, hakan yana ba wa mutum sani mai yawa, wanda idan ya zo ya samu jarin farawa da kansa, ba zai sha wahala ba.


Don haka, ka nemi wani mutumin ko abokinka wanda yake wata harkar kasuwar, ka zama yaronsa, koda aiken ka za'a yi  ko dakon kayan kwastoma a kasuwa, ko sayo kayan aiki ko wani abu makamancin haka, babu laifi.


Idan ka yi haƙuri mutane suka san ka a kasuwar, ko wajen aikin, lokaci zai zo da za ka iya samun 'yanci.


Zama yaron wani ba ya buƙatar sai kana da jari, hasali ma ita ce hanya mafi sauƙi ma wajen fara sana'a.


Sai dai ba kowa ne yake da wannan alfarmar ba.


3. SIYAR DA KANKA


Koda ba ka san kowa ba, ko ba ka da 'yan uwa a kasuwa, wannan ba zai zama uzurin da za ka ce ka rasa abin yi ba.


Yi amfani da Shafukan Sada Zumunta, ka zama mai ƙirƙirar maƙala wanda zai ja hankalin mutane, ka tara mabiya.


Yi amfani da wannan mabiyan ka je ka samu wasu 'yan kasuwar ka nuna musu cewa kana da mutane, su dinga ba ka talla, ko tsarin affliate ne, kai kuma kana samun wani abu.


Da yawan 'yan kasuwa za su ba ka wannan damar, domin zai kawo musu kwastomomi.


Ka je ka ɗauki hotuna da kanka, ka zo Shafukan Sada Zumunta ka fara tallatawa.


Wannan ma ba ya buƙatar sai kana da jari za ka fara.


4. KA YI AMFANI DA BASIRA


Wanda Allah ya sa yana da wata ƙwarewa ko wata baiwa, shi wannan nasa mai sauƙi ne.


Abin da ya rage maka shi ne, ilimin da kake da shi, da basirar da kake da ita, da wata ƙwarewa da kake da ita, ka fito da ita duniya ta sani, ka sanya farashin kuɗi mutane su biya ka koya musu.


Da haka za ka iya samun jarin fara duk sana'ar da kake buri.


Kuma sakamakon ilimin da kake bayarwa, wasu damarmakin za su zo maka, wasu Network ɗin za su ƙullu, da haka sai ka ga ka wuce wajen.


5. KA YI KARATU


Sau da yawa rashin bincike yake hana mutane da yawa samun wasu damarmakin. Don haka ka yi ƙoƙari ka inganta iliminka, da kuma mu'amalarka.


Ka yi ƙoƙari ka dinga halartar guraren ƙara ilimi, kamar tarukan kasuwanci, da taron ƙarawa juna sani, ka dinga halartar Online Classes, daga nan za ka iya samun wata fikira da za ka iya amfani da ita wajen rufawa kanka asiri.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user