Thursday, 1 May 2025

Gajerun Sakonnin Soyayya Irin Na Sarakai

Tura Wannan Zuwa Ga

Ranki shi daɗe hannuna a sama cikin aminci nake miki gaisuwar ban girma ga gimbiya sarautar mata, matsayinki ya kai a yaba miki.


Gajerun Sakonnin Soyayya Irin Na Sarakai
Hoto: Antonio Guillem/Dreams time

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR

Furucin furta sallama cikin karamci zuwa ga ma'abociyar kyawun suffa da kyawun diri. Ina motsawa ne da motsin da son ki yake matsar da ni cikin tsakiyar tekun ƙaunarki.


Kin hori zuciya da horon da ruhi yake hora ƙwaƙwalwata bisa irin yadda tunaninki yake yawan kawo ziyara cikin tsakiyar birnin masarautar zuciyata.


Gyara kintsi da kyau dole ne a cika miki fada yake sarauniyar da ke mulkin masarautar zuciyata. Taka a sannu yake jigon da ke jawo jerin farin cikin ruhina.


Ƙauna da son ki sun mamaye ruhina shiyasa zuciyoyinmu suke numfasawa a tare da junansu.


Sarauniya na zo gare ki da gaske zuciyata a makance, kalaman bakin ki su ne sinadarin ƙara ruruwar wutar son ki wadda ta mamaye zuciyata.


Akwai amana ni da ke babu ranar rabuwa, zahirin gaskiya ke ce wadda na zaɓa domin ki zamto ummin yarana.


Sannunki 'yar gaban goshin zuciyata. Na yi jinjina kuma na gaisheki. Burina ki zamto cikin farin ciki da tarin annashuwa, a daidai lokacin da kike karanta saƙonnina.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user