Monday, 28 April 2025

Mutane Nau'i 3 Ne A Rayuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

Mutane iri 3 ne, akwai masu ƙaunar hikima, da masu ƙaunar daraja, da masu ƙaunar riba. Idan kana cikin na 3, za kai asarar biyun. Idan kana cikin na 1 za ka samu 2.


Mutane nau'i 3 ne a rayuwa
Hoto: People Images/iStock photo

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Plato ya ce;


1. Wasu mutane suna ƙaunar hikima wato Wisdom. Duk abin da za su yi suna neman iliminsa, tare da fahimtar dukkan abubuwan da ke kewaye da shi.


Suna yi wa rayuwa kallo na fahimta da neman dalili tare da hasashen sakamakon kowanne aiki.


2. Wasu mutanen kuma suna neman daraja da mutunci, wato Honor. Komai za su yi wannan shi ne ma'aunin su, cewa hakan zai sa su samu daraja da mutuntawa idan sun aikata abin da suke son aikatawa.


Sai dai irin waɗannan mutanen a wani lokaci, za su iya aikata wani abu wanda ba hikima a cikinsa, matsawar mutane za su girmama su idan sun yi hakan.


3. Su ne masu neman riba kawai, wato Profits. Duk abin da za su yi riba ce a gaban su, ma'ana dukiya ko wani amfani na duniya.


Irin waɗannan mutane babu ruwansu da hikimomin rayuwa, ballantana maganar mutunci ko kuma a gan su da daraja.


Idan har za su samu kuɗi, za su iya yin komai ba komai.


FA'IDA


Idan ka kasance a cikin mutane masu ƙaunar riba ko dukiya kawai, tabbas za ka rasa hikima da daraja.


Za ka iya samun kuɗin, amma a ƙarshen rayuwa, za ka gane ka yi asara babba, domin ka siyar da kanka ne, ka karɓi abin da zai ƙare ko ya zama mara amfani wata rana.


Amma idan ka zama mai hikima da bin rayuwa cikin tsari, tare da fahimtar dalilai da hasashen sakamakon ɗabi'un ka da ayyukan ka, tabbas za ka samu riba, ta kuɗi da kuma abubuwa masu amfani a rayuwa.


Hakazalika za ka samu daraja da mutunci a tsakanin al'umma, domin ɗabi'un ka da ayyukan ka, za su dinga nuna wani mutum mai cikakken hankali da hangen nesa, tare da kiyaye doka da sunnar rayuwa.


Allah ya sa mu dace Amin.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user