Saurayi: Tun farko fara buɗewar ƙwayar hasken ganin idanuwana ban yi tozali da kyakkyawar fuskar da ta ɗimautar da zuciyata ba sai da na fara haɗuwa da ke.
Budurwa: Wane ne?
Saurayi: Wani ɗan saurayi ne wanda ki kai ma sata.
Budurwa: Sata kuma? Satar me na yi maka? Kuma Wane ne kai?
Saurayi: Ni kaina ban san kaina ba sai da zuciyata ta fara ganinki, shiyasa na zo domin ki ba ni bayanan yadda nake.
Budurwa: Bayanan yadda kake kuma? Ta ya za ka ce ba ka san kanka ba kuma kana so ka sani daga gare ni?
Saurayi: Yauwa tambayar da nake buƙata kenan daga gare ki, yanzu sai ki tsaya ki saurari batuna.
Ta ya zan iya gane kaina bayan ainihin suffar jikina ina kallonta akan tsakiyar fuskarki.
Ta ya zan iya gane kaina bayan kin tafi da dukka tunanin raina.
Ta ya zan iya gane kaina bayan gangar jikina kaɗai take yawo amma ainihin ruhina yana bin ki a duk inda kike.
Ta ya zan iya gane kaina bayan dukkan ƙofofin saduwar jini suna tare da ke.
Budurwa: Ɗan dakata da zanceka haka, na ji ka ce na yi maka sata shin wai me ne ne na satar maka ne da kake ta faman bi na a duk inda na yi?
Saurayi: Ehmmm kin saci abu mafi girman daraja da tsada a wajena.
Kin sace abu mafi saurin maida mutum rago duk tsananin jarumtar shi.
Budurwa: Kai Malam dakata haka nan ka zo ka cika ni da surutunka. Ni har yanzu na kasa gane abin da na sace maka ka ga idan ba za ka yi bayani ba ni zan shige gida.
Saurayi: Wayyo Allah na ɗan dakata mana kar ki saka rauni da rashin kuzari a jikina ta hanyar hana ni kallon wannan fuskar taki.
Da ma ba komai ba ne kika sace mun sai zuciyata. Na yi zaton za ki fahimta tun farkon da na fara furta bayanaina a kanki to amma sai kika yi mun bazata dole sai da kika sa na fallasa sirrina gare ki.
Budurwa: Ta ya za ka ce na sace maka zuciya bayan ga ka kana magana da kanka kuma?
Hmm naku har kullum Abdul'aziz Hamza KKR.
Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.