Ina fatan kin kasance lafiya kamar yadda nake a yanzu, na ji dukkanin saƙonnin zuciyarki zuwa ga tawa zuciyar. Ki sani tuni na daɗe da ganin wannan saƙon a cikin rubututtukan ki na baya gare ni.
Marubuci: Abba Rabi'u Matallawa
Da a ce kin ɗora sashen saƙonnina gun ki kan mizani da kin gano makamancin hakan a cikin su.
Manufar nawa saƙon gare ki domin na tonawa tawa zuciyar asirin da take ɓoyewa, amma fa ki sani ɓoyon ya faru ba don tsoro ba sai domin kwarjinin da wannan kyakykyawar fuskar taki ke yi mini.
Ina sanar da ke na daɗe da kamuwa da soyayyar ki fiye da yadda zan faɗa miki yanzu.
Na rantse miki da iyakar gaskiyata ina san ki fiye da yadda kifi ke son ruwa. Idan da babu soyayya tsakanina da ke babu dalilin da zai saka na nemi hoton ki har kala biyu, amma fa ba anan matsalar take ba idan muka tsunduma soyayya ina za ta kaimu? Na barki lafiya.