Idan wata matsala tana yawan faruwa da kai, akwai wani darasi da ka kasa koyo a cikin ta. Misali idan ana yawan cutarka a kasuwanci da ciniki, hakan yana nuna ba ka tantance abokan hulɗar ka, kuma ba ka nazari da bincike kafin ka ƙulla ciniki.
Marubuci:- Bello Ado Hussaini
Idan kana yawan samun saɓani da iyalinka ko abokin ka, hakan yana nuna abubuwa guda biyu musamman;
Kodai akwai wata daɓi'a da kake musu cikin mu'amala kuma ba sa jin daɗin ta, kai kuma ka kasa ganewa ka daina.
Ko kuma su suna da wani hali da ka kasa fahimtar yadda za ka mu'amalance su, ko kuma ka yi haƙuri da shi.
Idan kana yawan shiga matsala da jami'an tsaro, hakan na nufin ba ka tantancewa da doka, ko kuma gane iyakokin ta.
Idan kana yawan shiga matsalar kuɗi ko bashi, hakan na nufin ka kasa tsayawa ka tantance samun ka, da kuma irin buƙatun da ya kamata ka yi, da wanda za ka haƙura har matsayin ka ya sauya, samun ka ya ƙaru.
DARASI
Da yawan lokaci mutane kan ɗauka al'amura suna faruwa ne haka kawai, ko kuma rashin sa'a ne ko ƙaddara. Amma fa da yawa akwai abubuwan da muke yi, ko muke barin su, waɗanda ke ba mu irin sakamakon da muke samu.
Don haka idan abubuwan ka suna tafiya daidai, sai ka zage damtse, ka ci-gaba da addu'a.
Idan kuma akasin haka ne, sai ka yi nazarin abubuwan da suke buƙatar sauyi, domin samun sauyin sakamako.
Allah ya sa mu dace Amin.