Monday, 5 May 2025

Ka Tashi Matashi

Tura Wannan Zuwa Ga

Kai Matashi! Ka tashi!


Kai matashi! Me ya sa kake zaune da jajayen idanuwa, da hawaye akan kumatunka? Zuciyarka cike da tunanin cewa wai ka haƙura ba za ka yi nasara ba.


Shin don ka kasa yau, sai ka daina mafarkin gobe?


Ka tashi matashi
Hoto: Dreams time

Marubuci:- Abdallah Aliyu Saint


Kai dai ka sani, rashin nasara ba ƙarshe ba ne, kuma nasara ba ta zuwa idan ka tsaya kana jajen gobe da jin tausayin kanka.


Ka kalli rana, kullum tana faɗuwa, amma sai gobe ta dawo da haske.


Ka kalli tsuntsaye, kullum suna fita neman abinci, kuma ba duk rana suke samu ba.


Amma har yau, ba su daina shawagi ba.


Wannan ya nuna cewa tsayawa ba mafita ba ce. Ci gaba shi ne mafita.


Idan ka faɗi yau, ka tashi gobe da ƙarin ƙarfin zuciya.


Ka ƙara tunani, ka gyara kuskure, ka rungumi sabuwar dama.


Rayuwa tana wa mai juriya albarka.


Ba sai ka yi sauri ba, sai dai kada ka tsaya.


Ka riƙe burinka da gaskiya kamar amana.


Ka dinga cewa: “Na faɗi yau, amma gobe zan tashi.”


Domin wanda ba ya tsayawa, shi ne ya kan isa inda sauran suka gajiya.


Ka tashi matashi! Ka tashi! Ka ci  gaba da gina burinka a zuciya.


Ka san cewa: gobe taka ce, idan ka daina tsoron kuskuren jiya.


A hankali wahalhalun da kake tsoro za su dawo suna ba ka dariya.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user