Wednesday, 7 May 2025

Sakonnin Barka Da Maraice Masu Sa Budurwa Natsuwa

Tura Wannan Zuwa Ga

A cikin almurin maraicen ranar da idona ya fara ganinki tun daga lokacin ban ƙara iya aikata komai ba tare da na sanyo tunaninki cikin raina ba.


Saƙonnin Barka Da Maraice Masu Sa Budurwa Natsuwa
Hoto: Peak PX

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Aikin da ke cikin zuciyata shi ne sonki. Raina ya kasantu cikin dausayin ni'imar begenki, sai tunaninki ya zamto wani ɓangare na jikina.


Na zauna tsaf domin nazarin samun dama cikin dama irin wadda na samu a lokacin da Allah ya fara haɗa mu tsakanin ni da ke.


Zuciyata tana son ki hakan ne yake ba wa idaniya damar isar da saƙonta a lokacin da na so na gan ki sai kuma ban samu damar ganin naki ba hawaye su ne matakin farko.


Barka da yamma dukkan wani tarin farin ciki ina murnar ganin ya riske ki domin ya yo silar bayyanuwar murmushin fuskarki.


Tasirin kallon fararen idanun ki sun yi nasarar ƙara dawwamar da zuciyata bisa kan alƙiblar son ki hakan shi ne ya haifar min da yawan tunaninki.


Ni dai da ke zan rayu, da son ki zuciyata ta soyu. Mun fi ta cikin sahu na marayu. Sannunki mai sufar 'yan gayu.


Jarumtakar girman haƙiƙar sonki ta yi sanadin kafa daular ɗaruruwan begenki dare da rana, da son ki nake rayuwa.


Ban son kallo ko kuma jin wani sautin zancen da ba ya tuna min da zuwanki cikin raina.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user