Tuesday 26 November 2019

DARIYA DOLE: KARANTA LABARIN WANI MATASHI DA MATSAFA

Tura Wannan Zuwa
Wani gaye ne yayi kuskuren tura ₦200,000 zuwa wani account, balance ɗin da ke cikin account ɗin na shi gaba ɗaya ₦205,000 ne.

Dariya Dole

Sai wata dabara ta zo masa, nan da nan ya ɗauko waya ya turawa mai account din wasiƙa kamar haka:-

Dafatan ka wuni lafiya, ka duba account ɗinbka zaka ga kuɗi na turo maka
Somin tabi ne aka baka domin ka sami karfin guiwar shiga kungiyar mu ta matsafa.

Hakan ne zai baka damar keta hazo cikin dare domin samu damar zagaya duniya ka more rayuwar ka amma fa hakan zai kasance bayan ka sadaukar mana da wasu daga cikin danginka ciki har da babanka da babarka domin muyi tsafi da su.

Amma in baka bukata ga account nan ka dawo da kudin.

Bayan kamar minti biyar sai yaga an dawo masa da reply.

Abokina ma yace, ga account ɗinsa nan a tura masa 089X396XX36 shima yace yanason shiga kungiyar taku ta matsafa.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA LABARIN WANI DIREBA DA ALHAJI A TSAKIYAR DAJI

Karanta Labarin Wata Kyakkyawar Budurwa da Samari Guda Biyu

KARANTA LABARIN WANI BAFULATANI DA BATURE

Ni ma inason a ƙaramin matsayi a kungiyar, kafin nan inason a ƙaro min wasu kuɗaɗen domin na ƙara janyo wasu zuwa kungiyar.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user