Saturday 16 November 2019

DARIYA DOLE: Karanta Labarin Wata Kyakkyawar Budurwa da Samari Guda Biyu

Tura Wannan Zuwa
Wasu samari biyu LUKMAN da SURAJO su na tafiya akan hanya, sai suka zo wucewa ta gaban wani gida mai bene.


Labaran Nishadi


Wata kyakkyawar budurwa ta leko daga Window tana masu murmushi.

LUKMAN: Kai SURAJO dubi wata kyakkyawar yarinya can tana mana murmushi.

SURAJO: Hmm kyale ta kawai, zo mu tafi.

Har sunyi gaba sai LUKMAN ya kara waigowa, sai ta yi masa alamun zo da hannu.

LUKMAN: SURAJO tana kirana fa?

SURAJO: Ka kyale ta nace, zo mu tafi.

LUKMAN: Kai ko anya ba bakin ciki kake min ba? Gaskiya sai naje.

Sai LUKMAN ya nufi gidan su yarinya, ta shigar dashi falo suka gaisa, ta kawo masa abinci da abinsha.

Kafin ya fara cin komai sai suka ji mota ta tsaya.

Budurwar ta leka Window tace "Ga mijina ya dawo".

LUKMAN ya tashi a tsorace yana neman hanyar fita sai yarinyar tace "Zo ka ɗauki kayan nan ka fara guga, in ya shigo zance mai guga ne na kira".

LUKMAN ya kwashi tulin kaya ya Ci gaba da guga, ya kwashe ranar gaba ɗaya yana gugan kaya sunƙi ƙarewa kuma mijin bai fita ba.

Da safe sai LUKMAN da SURAJO suka haɗu a hanya.

MAKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA LABARIN WANI LECTURER DA WATA DALIBAR SA

KARANTA LABARIN WANI DIREBA DA ALHAJI A TSAKIYAR DAJI

KARANTA LABARIN WASU MATAFIYA DA ALJANI A SAHARA

LUKUMAN: Hmm SURAJO kasan jiya wuni nayi ina guga a gidansu yarinyar nan kuwa?

SURAJO: Ba nace maka kar kaje ba, duk kayan nan daka gani ni na wankesu shekarana jiya.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku.

Isar da bayanai akan lokaci ba tare da son
zuciya ba shine muradin Mu.

Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.


Mun kudiri aniyar tsage gaskiya dalla-dalla , sharhi mai gansarwa da suka hada da
harkokin yau da kullum da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user