Friday 13 September 2019

DARIYA DOLE: KARANTA LABARIN WASU MATAFIYA DA ALJANI A SAHARA

Tura Wannan Zuwa
Wasu mutane ne su uku, suna tafiya a sahara kowane daga cikin su ya galabaita da yunwa da kishirwa sun wahala matuka.

Labaran Matafiya da Wani Aljani a Sahara

Gashi ko alamar gari basu gani ba basu san lokacin fitar su daga wannan saharar ba don haka harsun fara tunanin mutuwa kwatsam sai ga wata kwalba a gaban su sunyi tunanin ruwa ne acikin ta Amma ina...

Suna bude kwalbar wani hayaki ya tashi sama, hayakin nagama fita sai ya hade waje daya, sai ga wani Aljani kato agaban su.

Nan take aljanin yayi wata mahaukaciyar dariya yace kowanne acikinku yafadi bukatarsa kowacce irice zan biya masa sakamakon budeni da kukayi daga wannan kwalba.

Aikuwa sai farin ciki ya rufesu gaba daya.

Sai aka tambayi na farko mai kake so?

Sai yace inaso akaini “DUBAI” abudemin kasuwanci sannan acikamin katuwar kwantena da kudi kusa da shagwan kasuwanci na.

Sai aljani yace ba wata….?

Yace Eh

Sai Aljani yace to shikenan rufe idonka yana budewa ya ganshi Adubai da dukkan abubuwan da ya bukata.

Sai da akazo kan nabiyu Me kake so…?

Sai yace a kai Ni America ayimin katon gida da motoci da kudi masu yawan da bazan iya karar dasu baAljani yace bawani…?

Yace Eh

Aljani yace rufe idonka yana budewa ya ganshi a America da duk abinda yake bukata.

Sai akazo kan na karshe Me kake so?

Yace Akawo masa ruwa, aka kawo yasha ya wanke jikin sa.

Sa aljani yace sai mai kake so?

Sai yace bukata ta karshe Adawomin da ‘yan uwana mu cigaba da tafiya.

Aljani yace itace bukatar ka ta karshe?

Yace Eh

Yana rufe bakinsa sai gasu kowanne an dawo dashi ciki sahara.

Aljani yabace yatafi abinsa.

LABARAI MASU ALAKA:

KARANTA LABARIN WANI BAFULATANI DA BATURE

KARANTA LABARIN SHAROTA DA ZUKOTA

KARANTA LABARIN AKU DA WANI MUTUM A SAUDIYYA

Idan Da Kai acikin matafiyan nan me zaka fara yiwa abokin tafiyar ku na uku? Domin ka huce takaicin ka.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Complete Tafseer, Complete Qur'an Audio, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user