Monday 29 July 2019

DARIYA DOLE: KARANTA LABARIN SHAROTA DA ZUKOTA

Tura Wannan Zuwa Ga
Wata rana SHAROTA na zaune a bakin hanya sai ga wani mutum yazo yana kuka rike da ledar cefa ne.

Mu sha Dariya


SHAROTA ya dube shi yace kai
malam lafiya?

Mutumin yace wallahi yau aka haifeni ina zuwa duniya aka aike ni siyen cefa nen daza'ayiwa yan barka abinci.

Ina tafiya ina girma ina tafiya ina girma gashi yanzu na kai shekara ashirin da biyar naman ta hanyar gidan mu.

SHAROTA yace kai amma
ya sunan ka?

yace ZUKOTA.

SHAROTA yace to zauna a nan
tukun saboda nima gidan mu
ne yayi dauda nayi

gammo na dauko shi na kawo nan dry cleaning a wanke mana idan angama sai mu tafi kila hanyar gidanmu daya.

ZUKOTA yace to amma dai yau naga abin mamaki.

SHAROTA yace ya akayi?

ZUKOTA yace ina tafiya kan hanya akayi accident har kan wani ya cire ana nema ba'a ganshi ba can sai aka yiwa gangar jikin cakulkuli sai akaji kan yanata dariya.

SHAROTA yace ai kafin kazo nan wani jirgin kasa yalike yaki gaba yaki baya da aka leka karkashi sai akaga ashe jaririn sauro ne ya rike tayar ya hanata motsawa!!!!!

LABARAI MASU ALAKA:


DARIYA DOLE LABARIN WANI YARO DA MAHAIFINSA AKAN JARABAWAR JAMB

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user