Saturday 13 July 2019

MU SHA DARIYA: KARANTA LABARIN WATA MATA MAI ABINCI DA 'YAR AIKI

Tura Wannan Zuwa Ga
Akwai wata mai abinci data kware wajen iya girki matsalar ta kawai masifa da ruwan bala'i.

Mu sha Dariya


Rannan sai wani Ustaz yazo cin abinci, da ya kammala cin abinci sai mai karbar kudi tace malam kudin ka dubu daya da dari daya ₦1100.

Anan fa Ustaz ya kafe yace bazai biya ba domin kudin yayi yawa.

Yarinya da taga abu yafi karfin ta sai taje ta gayawa Hajiya.

Tun daga wajen shago Hajiya ke danna zagi da masifa tace bari inga wane shege ne zai kawomin iskanci da raini.

Tana shiga shagon sai ta hada ido da Ustaz sai kawai tayi shuru ai sai takoma kan mai karbar kudi da masifa kefa baki da lissafi ai sai kiyi min bayani kice Mallam ne ai.

Sai tace kara mar Special Pack biyu ki hada masa da ruwan Swan guda biyu.

Mai aiki tayi shiru tana mamakin Hajiya.

Sai da Hajiya ta daka mata tsawa sannan ta dawo hankalinta.

Ta hada abinci tabawa Ustaz.

Hajiya sai ta fara cewa an gode Mallam, Allah yasaka da alheri.

Ustaz na fita Hajiya ta fadi kasa tana hada uban gumi tana wani irin nishi.

Sai mai aiki tace Hajiya lafiya kuwa?

Hajiya tace baki gane shi ba?

Eh

SHEKAU ne ai DAN Ubanki...

LABARAI MASU ALAKA:





Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode










TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user