Sunday 14 July 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 8

Tura Wannan Zuwa Ga
Shagalin da aka yi a Langeri, abin ya wuce a rubuta. Bayan an yi sallar azahar, sai aka hangi kura daga kudu kamar hadari. Sarki na zaton wani Sarki ne ya tafo gun biki, ya aiki 'yan tarye, ashe wani Sarki ne da ya ke wa Zulkaratu mugun so, Nakowa ya ki ba shi, ya ji ranar d‘aurin aure ya tafo ya ci garin, ya kwace ta da karfi. ’Yan tarye da suka tafi, ba wanda ya dawo Sarkin nan ya kama su duk. 

Tauraruwar Hamada


MarubuciBukar Mada

+2348021218337Na Sa'idu Ahmed Daura

Sarkin Langeri ba shi da asirin komi, kafin a ce haka Sarkin nan ya kewaye Langeri da dawakai da rakuma, babu shiga babu fita. Duk mutanen da ke bayan gari sun dad'e a hannu. Nan da nan da Sarkin Langeri ya ji yaki ne, ya sa aka yi gangami, duk dakaru suka shiga d’amara, suka hawo. Da Nakowa ya ji gangami, sai ya kasa hakuri, ya san dai wannan biki ya jawo ko menene, ya nufi fada a kasa, ya iske Sarki ya ce, “Ko lafiya?" Sarkiya ce, “Ina lafiya, yaki ne ya zo mana daga kudu“. Ko da Nakowa ya ji ya san abin da ya faru, Sarkin nan ne ya zo ya amshi Zulkaratu. Sai ya koma gida da sauri ya shirya ya d'auki takobinsa da abokinsa Aljani ya ba shi, ya hau doki ya doshi inda yaki ya ke. Ya iske mutanensa ba wanda ya iso. Bai yi wata wata ba, sai ya fada rundunar nan shi d'aya, in ya yi d'auki gabas na yamma su biyo shi, ya juya ya ce da ku Allah ya gama mu, su dare, inda duk ya nufa sai ka ga mutane falas kasa. Kafin a ce haka ya fara ba maza kashi, can mutanensa suka iso. Da zuwan mutanen Langeri, suka iske irin barnar da Nakowa ya yi, sai fa jikinsu ya yi karfi, suka fada fage da murna sun tabbata za su yi nasara. Kafin a ce haka mutanen waccan Sarki duk Nakowa ya shanya manyan dakarun a kasa. Sarkin ko yana gindin wata itaciya an girka masa karaga ya harde, dakaru sun kewaye shi. Sarkin Langeri ko zuwa bai yi ba, sai Yarima ango ya wakilce shi.

Sarkin nan yana gindin itaciya, ana yi masa fita bai san ba yaki ya bace masu, sai ya ga Nakowa ya nufo su. Dakaru suka zabura suka tarye shi, kowa suka gamu da Nakowa sai dai a sake haihuwar wani. Kafin a ce haka sai Sarki ya ga Nakowa ya nufoshi gadan-gadan da takobi tsirara, Sarki ya zabura daga karaga, ya ramci ta kare a kasa, Nakowa ya bi shi ya banke ya kama shi da ya ke baya son kashe shi. Ya daure shi da asawalin dokinsa, ya tuso shi gaba, yana cewa kai zaka rika wankewa Zulkaratu akusa, shi ya sa na ki kashe ka.

Da Sarki ya zo hannu, sai yaki ya tsaya. Aka kama mutanen Sarkin nan da dawakansu da duk dukiyar da suka zo da ita. Mutanen gari ko da duk bakin ciki ya rufe su, sai kuma cewa suke wannan amarya da sa’a take, ban da ganimar yaki, har ta sami Sarkin duniya zai rika wanke mata akusa.

Kashegari Sarki ya tara duk hakimai da manyan fadawansa a Majalisarsa, ya ce, “To, kun ga ni na tsufa, ga shi kuma na ga Yarima ya kawo hankali, ina tsammani zai dauki hakurin zama da ku, ina so zan huta shi ya zama Sarkinku, ko da ya ke dai muna tare, don in na ga ya yi ba daidai ba, zan rika ba shi shawara ina nuna masa hanya mai kyau ta rike jama'a. Jama'a duk suka yarda. Aka shirya sai kashegari za a nada sarauta. Ga irin taron biki ba a fashe ba, wannan dare duk mutumin da ke Langeri ba wanda ya yi barci. Gidan su Zulkaratu ko sai shiga da fita a ke. Sarkin nan kamamme yana can an ajiye shi a Kurkuku ba wanda ya kara komawa ta kansa.

Kashegari fada ta cika mutane abin ba a magana. Sarki ya sa aka girka karaga a waje, hakimai duk sun kewaye wurin. Sa’an nan Sarki ya tashi ya yi jawabi, kan yau ne ya ke so zai bar sarauta don tsufa ya kama shi, Yarima ya kama, ko da ya ke yana tare da Yarima, zai kuma rika ba shi shawara kan duk al’amura da ya ga ya kamata. Duka jama’a suka amsa sun yarda. Sai Wazirin Sarkin ya tashi, ya kama Yarima ya dora kan karaga.

Shagali fa ko ba a fad’a ba ka san inda aka ce an nad'a sabon Sarki ba a magana. Bayan an natsa, sai Sarki ya sa aka kawo Sarkin nan da ya kawo masa yaki, don matarsa. Da Sarkin ya zo, sabon Sarki ya ce, “Na yi murna da ya zamana ka iske ni, ina mukamin Sarki, kuma ina Sarki, zan yi ma abin da duk da na so" Ka sani, ba mu taka ma ba ba mu zubar ma ba, kurum sabo da yarinya ka taso ka haddasa barnar rayuka masu yawa, suka hallaka, to, da na yi niyya, in kashe ka, to, amma yanzu, zan barka da hakkin da ke bisa kanka, in kuma dora ma fansa, ka biya in maida ka garinka, don ina fata wannan ya zamamma ishara, ka kuma kara ilmin yadda za ka tafi da jama'arka nan gaba". Sarkin ya yi godiya. Aka d‘ora masa fansa, ya ce, “To, a gama ni da mutane in sun kai ni garina zan ba su biya". Aka gama shi da mutane cikin karama tamkar yana cikin sarauta ba a ci shi ba.

Kwanci tashi har Allah ya kai su kusa da birnin garin da ya ke sarauta. Da Sarkin ya ga sun zo kusa da birninsa, sai ya sauka tare da ’yan rakiyarsa, ya aiki mutum a sanad da mutanen gari ga shi ya dawo, su hawo a zo a taryensa. To, ka san labari ya dad'e da isa kan an kama shi kuma ba a shakka an kashe shi, sabo da haka har an nada babban dansa ya zama Sarki. Sabo da haka da labari ya isa kan a zo a tarye shi, ka san abin sarauta, sai dansa, watau sabon Sarki, ya fara cewa wannan ai zancen banza ne, wani ya taba mutuwa ya dawo har a ce za a je taryen gawa, fadawa suka ce koko fatalwa ya ke dai, aka dai ki zuwa a tarye shi.

Ko da Sarki ya ga shiru ba wanda ya zo, sai ya fahinta da abin da ya auku, watau an nad‘a sabon Sarki, sabo da haka sai ya tafi shi da 'yan rakiyarsa suka shiga birnin. Da shigarsu, mutane sai kallonsu su ke suna mamaki, kowa kuma ya nufi fada ya ga abin da zai auku. Shi ko da ya shiga gari, bai zame ko ina ba sai fada watau gidansa na da, ana ko cikin fadanci.

Da dai dansa wato sabon Sarki nan ya ganshi, sai ya ce, “Ashe maganar nan gaskiya ce, wato baba fatalwa ya ke, to ai ba zan kara jin kunya ba, ka mutu, amma zuciyarka har yanzu tana duniya." Sai ya tambayi Waziri maganin fatalwa, Waziri ya ce, “Maganinta ai sai a raba ta biyu da takobi, to ba zata kara komowa ba."

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa da karfe 9 na dare, insha Allah.


Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Shida ba to gashi nan mun kawo Muku..

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 7


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user