Thursday 11 July 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 7: LABARIN YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa
Kashegari Majalisa ta cika makil, sai Fada ya tafo, kamar yadda ya roki Sarki arziki aka yi masa. Mutane sai kallonsa su ke suna cewa, “Kai wannan mutum kuma ko so ya ke a daure shi." Ba wanda ya kalle shi balle magana. Da ko in ya tafo mutane na biye da shi di, sai a tarye shi ana gaida shi. kafin ya shiga Majalisa gun Sarki. Fada ya shiga ya yi gaisuwa, ba wanda ya ce ci kanka, sai ya tashi ya je kusa da Sarki ya sunkuya kamar Sarki zai fada masa wata magana, Sarki ya tuna maganarsu ta jiya, sai ya rika ce masa, "Allah wadanka," Shi ko yana cewa, “To, Allah ya baka nasara." Sarki ya zazzage shi, ko da aka gama zaginsa, sai ya yiwo waje da sauri, kamar wanda aka fada wa wani asiri, ya je ya aikata.


Tauraruwar Hamada



MarubuciBukar Mada

+2348021218337



Na Sa'idu Ahmed Daura


Ko da mutane suka ga haka sai suka yi zaton an huce da shi, har ga shi an yi maganar asiri da shi kamar da. Kafin a ce haka gidan Fada ya cika makil abin har ya fi da, kuma kowa na fadin ta bakinsa, duk gari ya dauka ai an maida Fada, mutane sai duruwa su ke gidansa, ana yi masa barka, shi ko, tun da ya san gobe ma za shi a zage shi sai amsawa ya ke.

Da Sarki ya gane dabarar da Fada ya yi, sai ya sa aka kira shi, ya ce, “To, na ji gidanka ya cika, ana yi ma barka wai na maida ka, wa ya ce na maida ka ?“ Fada ya ce, “Allah ya ba Sarki nasara, zaginka da ka ce in ka yi mini masifa zata auka mini, to ita ce yanzu, ta auka mini, tun da mutane don izgili sun ga ka zage, sun ce ka maida ni, ko da ya ke dai ba su san zagina ka yi ba, abin da ya sa suka zo yi mini barka, don ka ce na yi ma karya ne kurum, kuma zuciyarka ta kara baci, to mai sonka ya bata ma rai ne ?" Da Sarki ya ji haka sai ya ce, “To, tun da ya ke an yi ma ne don ba’a, to shi ke nan, na maida ka, kuma su je su yi ba'ar mu gani". Fada ya koma kamar da, ya gode wa Allah da Ma'aikinsa da haka ta faru, don ya kara sanin yadda zai zauna da mutane. Da Fada ya ga sabo da M.'Danye haka ta auku gare shi, sai kuma ya yi kamun kafa ga M.’Danye, kullum wurinsa za shi hira. Ta haka M.‘Danye ya san asirin kasar kaf.

Da fa M.'Danye ya ga garin ya zama nasa, sai abin da ya ce, ga shi kuma ya san abin da duk ke cikin fadar Sarki, sai fa ya shiga cikin sha’anin mulki sosai ya yi ta tara abin duniya, gama shi da ya ke abin duniya ya ke so kurum, to ko Sarkin ba ya samun abin da ya ke samu.

Labarin yarinya kuma soyayya sai gaba ta ke har ya zama dare da rana tana gun sa. To, da fa M.‘Danye ya ga ya tara abin duniya ya ga kuma in ya sake zai bata lokacinsa a wannan gari, sai ya bar yi wa yarinya ko maganar aure, ta ga duk dai ya canza mata hali. Yarinya fa hankalinta ya tashi, har ta fad'a wa uban, ita gara a yi, a yi bikinsu.

Ganin hankalin yarinya ya tashi, sai Sarki ya aika wa M. ‘Danye a fada masa ya kamata ya yi shiri a yi biki. M. 'Danye dame ya cire kan bawo, ya sami hanyar gudu cikin arziki da sutura, sai ya aika a fad’a wa Sarki, shi yanzu kam ba shi da sukuni, amma yana so Sarki ya ba shi lokaci ya koma gida ya shiryo don bikin zai fi armashi. Kuma ga shi ubansa ya sani. Sarki jin haka sai ya ce gaskiyar M . 'Danye, ya ce, “To, sai ka shirya na ba ka wata shida, ka tafi ka shiryo ka dawo". Sarki ya yi masa kyauta mai yawa, ya kawo doki taka ka hau ya ba shi. M. 'Danye ya shirya ya tafi shi da Dabo.

Labarin Zulkaratu ko, tana can ita da Yarima soyayya sai abin da ya yi gaba, sun daidaita ba abin da a ke jira sai biki kurum. Masoya ko, abin ba a magana, daga ko ina sarakuna sai aikowa su ke, wad'ansu jin ba za a ba su ba, suna ta shirin su zo su ci Langeri, su amshe ta.

An Yi Bikin Zulkaratu Da Yarima.

Ganin irin aike da kullum Nakowa ke samu kan ana son Zulkaratu sai ya ba Sarki uban Yarima shawara ya kamata a yi musu biki, ko ya huta da maganar mutane, kada wani tashin hankali ya same su, ko ita yarinyar. Sarki ya yarda aka sa ranar biki ashirin ga wata. Sarki ya sa aka rubuta takardu duk aka aikewa Hakiman kasarsa da kuma Sarakunan da su ke abin arziki, kan su halarci bikin.

Kafin ranar bikin ta zo da kwana bakwai Langeri ta cika makil. Ranar biki da ta zo mutane tilas wad'ansu sai bayan gari suka sauka, don dai Sarkin dansa ke nan Yarima, balle kuma Nakowa.

Shagalin da aka yi a Langeri, abin ya wuce a rubuta. Bayan an yi sallar azahar, sai aka hangi kura daga kudu kamar hadari. Sarki na zaton wani Sarki ne ya tafo gun biki, ya aiki 'yan tarye, ashe wani Sarki ne da ya ke wa Zulkaratu mugun so, Nakowa ya ki ba shi, ya ji ranar d‘aurin aure ya tafo ya ci garin, ya kwace ta da karfi. ’Yan tarye da suka tafi, ba wanda ya dawo Sarkin nan ya kama su duk.

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa da karfe 9 na dare, insha Allah.

Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Shida ba to gashi nan mun kawo Muku..

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 6


MU KALOLI MASU ALAKA:

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN FADAR BEGE

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA

TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BA



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user