Monday 8 July 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 6: LABARIN YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa
Bayan zakara ya ba su sa'a sun bar wannan gari da suka yi samu mai yawa, sai suka kama wata hanya ba su san inda za su ba. Suna cikin tafiya, Dabo ya ce da M. 'Danye, “Ashe dai hanyar sata yawa gare ta, da a banza mu ke bin dare, ka ga ta hanyar tsubbu, har gida, mu sace mutum ya kuma rika yi mana godiya, wai mun taimake shi.” 


Tauraruwar Hamada



MarubuciBukar Mada

+2348021218337



Na Sa'idu Ahmed Daura


M. 'Danye ya ce, “Ko da ya ke akwai abin da ya fiddo ni daga gida, amma duk da haka, kafin mu samu biyan bukata zan koya ma hanyoyi masu yawa wanda zaka ci abinci." Dabo ya ga sun sami dukiya mai yawa kan hanyar tsubbu, sai ya ce, “Ai hanyar nan ta tsubbu ta fi ko wace.” M.‘Danye ya ce “Kai dai ita ka gani, sa ido mana, ka kuma yi aiki da abin da na ce maka.”

A kwana a tashi rannan suka isa wani babban birni wanda ya fi duk birnin da suka wuce. Da suka shiga garin ba su zame ko ina ba sai fada. Aka yi masu iso gun Sarkin suka shiga. Bayan sun gaida Sarki aka tambaye su ko daga ina suka fito. M. ‘Danye ya ce shi dan Sarkin Damas ne ya ji labarinsa ya tafo don ya gan sa su yi zumunci. Da Sarki ya ji haka sai ya ce, "Don me ka tafo a kasa ?" M. Danye ya ce rakuminsa a  hanya ya mutu. Sarki ya amshe su da murna, ya sa aka kai su masauki. M. 'Danye ya ce da Dabo, “Kai dai in za ka shiga yawo irin wannan, kada ka yarda ka rabu da sutura mai kyau, to ko ina ka shiga duk karyar da ka yi da hannu biyu za a ansa, ka yi samu mai yawa, duk ko albarkar sutura mai kyau ce."

Sarki ya sa aka yi ta kai kayan sauka iri-iri, sai ka ce wani gawurtaccen Sarki ya sauka. Gogan naka komi aka kai masu in ya tashi ba da tukuici, sai ya ba da fiye da abin da aka kai. Sarki ya ce, “Af, haka bakon ke yi, ashe abin na yi ne." Aka yi ta kashe masu gara abin ba a magana. M.’Danye ya samu shiga gun Sarki sosai, har ya zama da dare tare su ke hira, su biyu, Dabo na can bakin kofar gida yana rike da takalman M.'Danye.

Ran nan suna hira da dare, sai M.‘Danye ya ga 'yar Sarki ta fito, ya cewa Sarki, “Wannan fa ?" Sarki ya ce, “Af, baka santa ba. ai ’yata ce.” Sarki ya kirawo ta, ya ce, “Zo ki gaida wani wanki." Yarinya ta zo ta gaida M.’Danye. Da. M.'Danye ya koma gida sai ya sa aka kira masa babban bafadan Sarkin wanda komi ya ce kansa za a tsaya, ana kiransa Fada. Da Fada ya zo, M. 'Danye ya fad‘a masa yana son ’yar Sarki da aure. Fada ya ce, “Ranka ya dad'e, wannan ai ba abu ba ne mai wuya M. Danye ya kawo fam hamsin ya ba shi ya kai wa Sarki, ya kuma ba shi fam biyar nasa. Fada ya kunshe kud'i ya fita, bai zame ko ina ba sai gidan Sarki. Ya isa gun Sarki, ka san shi ba sai an yi masa iso ba, ya kai masa kudi, ya ba shi labarin bukatar M. 'Danye, sa’an nan ya shiga gyara magana. Sarki ya yarda, amma zai shawarci uwar yarinya.

Fada ya koma ya sanad da M .'Danye, Sarki ya yarda amma, zai shawarci uwar yarinya da yarinya. M. 'Danye ya ce, “Bai yarda ba ke nan, da ya yarda ai ba sauran shawara, tun da su duka mulkinsa ne." Sai ya sake kawo fam ashirin ya ce a kai wa Sarki fam goma, uwar yarinya fam goma. Fada ya amshi kudi ya koma. Ya sanad da Sarki, ga kuma abin da M.'Danye ya ce, ga kuma abin da ya bayar. Ko da Sarki ya ga kudi fam ashirin ga waccan fam hamsin ka san a zamanin nan fam hamsin daidai ta ke da jaka hamsin a yau, ya ga kuma M.‘Danye d’an Sarki ne, ga shi da halin karama, sai ya ce da Fada, “Ai ba abin da zai hana tun da ya ce yana so, amma za a tum ta don su shirya tsakaninsu." Fada ya koma ya fada wa M. Danye jawabin Sarki, don murna M.'Danye ya ga hanyar samu ta bud'u, sai ya sa wa Fada wata katuwar riga ta kwakwata.

Aka fada wa yarinya ta rika zuwa gun M. 'Danye, sabo da haka hira tsakanin Sarki da M.‘Danye ta mutu. Kullum da magariba, sai a gama yarinya da Jakadiya su tafi gun M.'Danye. In yarinya ta shiga, sai Jakadiya ta komo kofar daki ta zauna, wani Iokacin M.‘Danye kan ce da Jakadiya ta d'auko mafici ta rika yi masu fita, su yi ta hira har sai dare ya raba. Ka san duk inda mutum mai hila ya kai, to M. 'Danye ya kai, sannu ya shirya wa yarinya hanyoyi masu yawa wadanda za su sa ya samu shiga gun Sarki, a sakam masa komi, yadda zai samu ya farke abin da ya bayar. Sabo da hilarsa ya zamana yarinya tana sonsa kamar ta hadiyeshi, kuma duk abin da ya shirya mata, in ta koma gida sai ta yi ta rikici gun ubanta, nan da nan a aikata. Wannan fa ya sa fadar M. 'Danye ta karu, ba'a jin maganar kowa duk garin sai tasa.

Da Fada ya ga shi ya yi wa M.'Danye hanya, ga shi kuma ya kwace masa fada, sai ya shiga sukar M. ‘Danye gun Sarki. To ka san wanda aka ce har ga shi za a ba, ’ya, komin sukar da aka yi ta banza ce, har ma kai mai sukar sai a ga bakinka. Sabo da haka Sarki sai ganin bakin Fada ya ke, yana cewa ashe ba ya kaunarsa, tun da ba ya son dansa. Abu kuma fa duk ya yi wa Fada zafi, kai har ran nan Sarki ya ce kada ya kara ganinsa, ko Majalisarsa, Fada ya yi tubar duniyar nan, Sarki ya ki ji. Fada ya komo gida abin duniya duk ya yi masa zafi. Da dare ya yi, sai Fada ya tuno wata dabara, sai ya tashi ya tafi gidan Sarki. Da ya isa, aka yi masa iso, Sarki ya ce, “Ba shi na ce kada ya kara zuwa gidana ba. ?" Jakadiya ta ce, “Allah ya ba ka nasara, ai sai a bar shi ya zo a ji irin jawabinsa. Sarki ya ce ta tambayo shi, me ya kawo shi. Jakadiya ta tambayo Fada, ya ce, magana gare shi. Sarki ya ce “Ya shigo ya fada". Da ya shiga ya yi gaisuwa, Sarki bai ko amsa ba, sai ya ce, "Fadi maganar taka." Fada ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ina so cikin yardar ka, kullum in ka zo majalisa in zo in gaida ka, sa‘annan in zo kusa da kai, kamar zan fada ma wata magana, kai ko ka rika zagina. Domin ka sani tun da na tashi mu ke tare, to, na saba da kai, a yanzu ka ce ba zan zo gare ka ba, lalle sai dai in tashi daga garin. Ina ko tsammani, idan kana zagina kullum, har wata rana sai ka huce, idan ko ba ni zuwa, kullum kana nan da fushina, ba abin da ka ke mani na fucewa." Sarki ya ce da Fada, “So ka ke kullum da safe in zageka, ba ka tsoron kada wata masifa ta same ka ?" Fada ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ba komi, ni dai bukata ta ke nan." Sarki tsammanin wata masifa zata afkawa Fada idan yana zaginsa kullum sai ya ce, “Na yi ma."

Nan ko cikin gari magana ta bazu an kori Fada, duk inda ya nufa ba mai ko son ya ganshi bare ya yi masa magana. Gidansa, da kullum a cike ya ke, da baki da mutanen gari, masu neman abin tuwo da masu shari‘a, amma da wannan ta afku ko kare bai kara gani ba daga shi sai matansa da ‘ya‘yansa. Fada ya ce, “Ko da su mutanen duniya haka su ke, sai ana yi da kai a ke son ka". Bugu da kari, sai Fada ya yi ta ji a gari ana ta fadin laifukan da bai ji bai gani ba, anacewa duk shi ya yi, abin duniya duk ya rude masa, ya maida abin ga Allah, don dai ya tabbata, ba wani abu da ya yi mugu, wanda har ya sa a ke yi masa wannan maganganu.

Kashegari Majalisa ta cika makil, sai Fada ya tafo, kamar yadda ya roki Sarki arziki aka yi masa. Mutane sai kallonsa su ke suna cewa, “Kai wannan mutum kuma ko so ya ke a daure shi." Ba wanda ya kalle shi balle magana. Da ko in ya tafo mutane na biye da shi di, sai a tarye shi ana gaida shi. kafin ya shiga Majalisa gun Sarki. Fada ya shiga ya yi gaisuwa, ba wanda ya ce ci kanka, sai ya tashi ya je kusa da Sarki ya sunkuya kamar Sarki zai fada masa wata magana, Sarki ya tuna maganarsu ta jiya, sai ya rika ce masa, "Allah wadanka," Shi ko yana cewa, “To, Allah ya baka nasara." Sarki ya zazzage shi, ko da aka gama zaginsa, sai ya yiwo waje da sauri, kamar wanda aka fada wa wani asiri, ya je ya aikata.

Za mu ci gaba ranar Laraba da karfe 9 na dare, insha Allah.

Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Biyar ba to gashi nan mun kawo Muku..

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 5


MU KALOLI MASU ALAKA:

KARANTA CIKAKKEN TARIHIN FADAR BEGE

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA

TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BA


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode







TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user