Saturday 6 July 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 5: LABARIN YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa
Ran nan da dare, sai wata mace ta zo, ta ce, “Gafarta Malam, mijina ne ya mutu tun shekara bakwai, amma na rasa manemi, ina so ka bani laya ta samin bazawari, in ya samu ko wane iri ne zan baka fam ashirin". M.’Danye ya dauki alkalami da takarda da tawada yana rubutun karya, sai ga wani kure kisim-kisim ya biyo ta kusa da gidansu, yai tsaye ya yi kuka, wuu-wuu. Sai kurum M.'Danye ya ajiye alkalami ya ce, “Ai sai biya, don kin ce ko wane irin bazawari, to wannan kukan da ya yi cewa ya yi, ina bazawarar ga shi.”

Tauraruwar Hamada



MarubuciBukar Mada

+2348021218337



Na Sa'idu Ahmed Daura



Mace ta ga M.'Danye da gaske ya ya ke, sai ta ce, “Allah gafata Malam rabu da wancan bazawari, ni yi mani layar in samu in je gida lafiya". M. 'Danye ya ce, “Na fa rabu da shi, na yi maki aiki ya ko ci, ba ki biya ba" Mace ta ce, “Ai sai ka yi mani layar komawa gida lafiya tukuna" Da M.'Danye ya ji ta samu, ya ce, “To ai sai ki biya ni, sa'an nan in shiga sabon aiki." Bazawara, don tsoron kada ya bar ta da Kure, ta biya shi fam ashirin chif. Sa’an nan ya ce, “To nawa za ki biya ni, in taimake ki, ki koma gida lafiya ?” Suka yi tsada fam goma, ta biya. Sai ya ce da ita ta tsaya, ya shiga bukkarsu, dama akwai wata katuwar ganga, sai ya buga, gan-gan-gan-gan-gan. Ko da Kure ya ji karar ganga, sai ya zabura a guje, ya tsere. Bazawara ta samu ta tsere.

Ran nan wani Bafilatani ya zo gun su M.'Danye, ya ce, “Gafarta Malam “Na zo ka taimake ni, ka ba ni magani in yi shanu', M. 'Danye ya ce, “Waiya, wannan ai babbar magana ce, sai munga Sarkin Aljannu". Ya tambayi Bafilatani yaushe za ka zo, muje mu gan shi. Bafillace ya ce “Ai gafarta Malam ni ko yanzu ka ce mu tafi sai mu tafi". M.'Danye ya ce, “To ka zo ne da gaisuwar Sarkin Aljannu, don ba a ganinsa, sai da jaka". Bafilatani ya ce, yanzu bani da jaka, amma zan je in saida shanu in kawo jibi." Suka yi sallama sai jibi.

Da Bafilataniya fita, sai M. ‘Danye ya kira Dabo ya ce, “To jibi idan Bafilatanin nan ya dawo, za mu bayan gari, gun tabkin nan, da ma akwai wani tabki gabas da gari. Kai za ka shiga sagagin ciyawa na bakin tabkin, idan na ce, “Yo Sarkin Aljannu, ka rika yin wata irin magana wanda ba za a fahinta ba". Komi dai na ce kai dai rika maganar da ba za a fahinta ba". Dabo ya ce, “To,".

Bayan kwana biyu Bafilatani ya zo da jaka guda. M.'Danye ya amshi jaka ya adana, sa‘annan ya dauko wata jakar dabam ya saka dutse, sa'annan ya ce da Bafilatani, “To tafiya, sai fa dare ya yi don ba a ganin Sarkin Aljannu sai da dare”. Bafilatani ya ce, “To."

Da suka ci abinci, sai Dabo ya fara tafiya. Bayan an jima can sai M.'Danye da Batilatani suka bi shi. Da suka isa sai M. 'Danye ya ce da Bafilatani, “To dakata can, zan je in jefa masa kudin, in yi masa sallama. Bafilatani ya dakata, M. 'Danye ya tafi bakin tabki ya ga inda Dabo ya ke cikin sagagin hakukuwan bakin tabki, sai ya saka jaka cikin ruwa, abin nauyin dutse, sai ji ka ke kundum. Sa'an nan ya komo gun Bafilatani ya ce, “To matso". Bafilatani ya matsa. M. 'Danye ya ce, “Ka ji na ba shi kudin ?" Bafilatani, yana rawar jiki duk tsoro ya kama shi zai ga Sarkin Aljannu, ya ce, “E, na ji fadawarsu". Sa'an nan M.'Danye ya ce, “To saurara", Bafilatani ya yi shiru kamar wanda ya mutu ko motsi ba ya yi, ya kura wa M.'Danye idanu. Sai M.'Danye ya ce, “Yo Sarkih Aljannu !" Sai Bafilatani ya ji an ce “Mo', M.'Danye ya ce. “Ranka ya dad‘e, baki mai sarautar duniya, wanda ka so da arziki ya samu, wanda ko ka ki ya lalace, ka ga jaka guda ta kudi?" Sai Bafilatani ya ji an ce, “Bo, nafofato waja kudi.’ Sai M.'Danye ya ce, “Ya ce a gaya ma ya ga kud'i, ya kuma gode, ka kuma fad’i wai bukatarka ko wace iri ce a duniyar nan." Bafilatani da rawar jiki, ya ce “Shanu ni ke so ya taimake ni in samu". M.'Danye ya ce, “Ran Sarki ya dad'e, yana so ka taimake shi da shanu daga taskarka ta shanu”. Sai Batilatani ya ji an ce daga cikin tabki, “Kaliyori fem ma juma'a wakawari Kurunzun-zum." M. 'Danye ya ce da Bafilatani ranar Juma’a in an fito daga Masallaci ya ce ka je yamma da kasuwa ka rika cewa Kurumzunzum, za ka ga shanu sun kewaye ka, sai ka kora ka tafi, don sai ran Juma‘a a ke bude taskarsa ta shanu, ya kuma ce a fad’a ma komi yawansu ya ba ka, kada ka ga yawansu ka d'ebi kadan. To ran Juma'a ko kasuwar ke ci. Ka san Bafilatanin daji da shanu da jin an ce masa komi yawansu nasa ne, kada ya bar wad'ansu, sai ya ce da M. 'Danye, “Ka fad’a masa komi yawansu, a sako su duk na iya kore su.” M.‘Danye ya ce," Ai dama ba za’a koro yadda za su yi ma kadan ba." Bafilatani ya ce", to na gode, amma yanzu ba ni da goron da zam baka." M .‘Danye ya ce, “Ai ni ba komi, sai lokacin da shanun suka zo hannunka, ka sallame ni". Suka yi sallama a nan suka rabu.

Bayan M.’Danye ya zo gida kadan sai ga Dabo. Dabo ya ce da M. 'Danye, “To ai sai mu gudu don kada a gane mu". M. 'Danye ya ce, “Haba Dabo, ai Bafilatanin nan ko yana tsafi da bakar jaka, ya rabu da kudin nan, ba ko abin da zai same mu, shin kai ba ka iya duba ba, ai dama tilas ne, mai yin irin wannan kada ya yi fargaba, ya ko shiryi bakinsa, ai sai mu jira mu ga abin da zai faru ran Juma'a".

Ran Juma‘a Bafilatani don doki, tun da hantsi ya yi ya je yamma da kasuwa ya zauna. Masayar shanu ko a kasuwar, yamma da kasuwar ta ke, sabo da haka sai gani ya ke shanu na wucewa, shi duk zato ya ke nashi ne suka fara zuwa, in ya ga mai kiba sai ya ce yauwa, irin wadannan na ke so a rika kawowa, in ya ga ramammiya sai ya yi tsaki, Mts. Yana nan ya ki ko cin abinci don murna, har aka fito daga Masallaci. Ko da gogan ya ji an fito daga Masallaci, sai ya tashi ya zabi fili babba wai don kada wadansu su rasa wurin tsayawa. Sai ya fara fad’i, 'kurunzun-zum, kurunzunzum, kurunzun-zum ya yi ta fad'i, ko kaho bai ga ya nufo shi ba, ya yi zaton ko ba aji ba, sai ya yi ta fad’i da karfi, har ya fara gajiya, shiru ka ke ji. Da Bafilatani ya ga haka, sai ya tafi masayar shanu, yana cewa, “Kai ku koro mini su nan, ku shanu ba ku ji ina kiranku, ko so ku ke in fada wa Sarkin Aljannu". Mutane da suka ga haka sai suka zata tabuwa ya yi, sabo da haka ba wanda ya kula da shi. Yana nan, in za a tafi da shanu, sai ya tsare, ya ce, “Ina zaku kai mini.' A ture shi har ya fad'i, a wuce, har magariba aka watse aka bar shi a masayar shanu, ba bu sanuwa ko daya.

Da iyalinsa suka ga shiru suka biyo shi, suka same shi a masayar shanu yana hauka, suka lallabe shi suka kai shi gida. Abu dai ya kai Bafilatani ga turu, ga shi ya tabbata lafiyarsa lau, amma mutane har da iyalinsa sun ce shi mahaukaci ne. Da ya ga wahalar turu ga ba kudi ba shanu, sai ya ga gara ya bar zancen shanu, ko ya sami lafiyar turu. Sabo da haka ya yi shiru, aka ce ya warke, aka fitar da shi, ya hakura. Da M. 'Danye ya sami labarin abin da ya faru ga Bafilatani, sai ya ce da Dabo, “Da ma na gaya ma, ka ce wai mu gudu, to kan me, ba mu kai shi gun Sarkin Aljannu ba, bai ga an jefa kud'in shi a tabki ba, bai kuma ji maganar Sarkin Aljannu ba, to mi nene laifinmu ciki, ko kana zato ya san kai ne ka ke magana ba Sarkin Aljannu ba ?" Dabo ya ce, “Wallahi gaskiyarka”. Sa’an nan suka yi shiri suka bar wannan gari.

M.’Danya Ya Shiga Neman Auren Yar Sarki

Bayan zakara ya ba su sa'a sun bar wannan gari da suka yi samu mai yawa, sai suka kama wata hanya ba su san inda za su ba. Suna cikin tafiya, Dabo ya ce da M. 'Danye, “Ashe dai hanyar sata yawa gare ta, da a banza mu ke bin dare, ka ga ta hanyar tsubbu, har gida, mu sace mutum ya kuma rika yi mana godiya, wai mun taimake shi.” M. 'Danye ya ce, “Ko da ya ke akwai abin da ya fiddo ni daga gida, amma duk da haka, kafin mu samu biyan bukata zan koya ma hanyoyi masu yawa wanda zaka ci abinci." Dabo ya ga sun sami dukiya mai yawa kan hanyar tsubbu, sai ya ce, “Ai hanyar nan ta tsubbu ta fi ko wace.” M.‘Danye ya ce “Kai dai ita ka gani, sa ido mana, ka kuma yi aiki da abin da na ce maka.”

Za mu ci gaba ranar Litinin mai zuwa, da karfe 9 na dare, insha Allah.

Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Huɗu  ba to gashi nan mun kawo Muku..


KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 4


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user