Saturday 6 July 2019

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BASASAR NIGERIA: ZA KU JI ABUBUWAN DA BAKU TABA JI BA A YAKIN BASASAR NIGERIA

Tura Wannan Zuwa Ga
Ga ‘yan Najeriya da basu san Ojukwu ba har suke zaton bashi da hannu a aika aikar janairun 1966 su sani cewar rahoto ya inganta, cewa Ojukwu ya fita kasashen waje ba da sanin ofishin sa ba a 9 zuwa 13 ga janairu.

Tarihin Yakin Biyafra



Marubuci: Lawal Ali Reseacher


Wani jami’ain soja dake aiki a kano ya tabbabar da haka; Domin ya bayyana cewa a jirgi daya suka fita daga kasar tare da shi Ojukwu. A 14 ga wata kuma Ojukwu ya shiga garin Kaduna daga yamma zuwa farkon dare tare da wata mata da ya ajiye a Hamdala Hotel ya gana da wasu mutane.

Wanda ya fitar da maganar ya ce ya san matar; Ya tambayeta bayan nan kuma ta tabbatar masa da hakan. Awoyin farko na 15 ga wata ya mamaye filin jirgi da Gidan radiyo a kano bisa tunanin manyan Arewa zasu sulalo don gudun hijira… duba littafin Let Truth be Told na David Muffett.

Chif Christian Onoh, shima, tsohon gwamnan Anambara ne, amini kuma suruki ga Ojukwu cewa yake “tun Disambar 1964 zuwa Janairun 1965 Ojukwu yaso yin juyin mulki. Da hakan bata samu ba sai ya yaudari wasu yara 5 masu mukamin Manjor don cimma burin sa a 1966. Bayan matasan sun kwace kasar sai wasu manyan soja bisa jagorancin Ironsi Mai-kada suka murkushe su (juyin mulki cikin juyin mulki). Ganin haka sai Ojukwu ya juya wa wadancan kananan sojoji baya da yin biyayya ga Ironsi. Bai’ar da yayi tasa Ironsi nada shi gwamnan jihar gabas. Samun wannan matsayi ya sanya shi wulakanta Azikiwe da yake ganin ya zame masa kadangaren bakin tulu ga kasancewar sa shugaban kasa. (C.C Onoh yaci gaba da cewa) ta kai ga Azikiwe rubuta takardar koke ga Ironsi don ya tsawata wa Ojukwu.

Wannan Fada ya faro ne daga lokacin da Ojukwu ya roki Azikiwe daya bashi hadin kai don kawar da Tafawa Balewa a 1964, shi kuma wancan tantirin jahili (kamar yadda yake kwatanta Ironsi) watau Birgediya Ironsi suyi masa ritaya. Da yin haka sai Azikiwe ya zama shugaban wucin gadi ko Piraminista shi kuma ya zama shugaban sojoji. A cewar sa hakan zai kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

A matsayin Azikiwe na wanda ya san harkokin dimokaradiyya, yaki yarda da bukatar Ojukwu. Daga nan basu kara zama inuwa daya da Ojukwu ba.

Hadin kan da Zik bai bayar ba yasa Ojukwu yaudarar wadancan tsageru. Ya tsara yadda zasu kawar da Ironsi a matsayin Shugaban Hafsan-hafsoshin sojojin Najeriya da Tafawa Balewa Prime-Minister a Lagos da yadda zasu kame Gidan radiyo da bayyana shi a shugaban gwamnati kuma jagoran sojojin Najeriya gaba daya. (C.C Onoh ya kara da cewa) kashe Ironsi dai bai samu ba, karshe ma ya amshe ragamar gaba daya. Dole Ojukwu ya mika wuya, shi kuma ya saka masa da gwamnan yankin gabas…

Wannan bayani yana nan cikin wani karamin littafi da Farfesa Tom Forsyth ya rubuta mai suna The Heroes Of Change.

Ga mai neman sanin abin da ya faru a janairun 1966 lallai dole ya shiga duhu ya kuma shiga haske. A Arewa Magana daya ce, saboda hadamar mulki aka zabi madaukakan ta aka kashe da gangan, Hasken kenan. Amma a inda duhun yake shi ne a kudu musamman yankin gabas inda makasan suka fito. kowa so yake ace shi gwani ne, shi ne mafifici cikin inyamurai. Tahsabuhum jami’an, wakulubuhumut-shaattah, sun hada baki amma zuciyar su a rarrabe. Ojukwu ya kitsa juyi don zama shugaban kasa, akayi juyi shugabanci bai samu ba. Ironsi ya zama shugaban kasa ba da son Ojukwu ba.

shi kuma Ojukwu daya kafa Biafra, Nzeogwu bai so ba. Dalili kenan ma ya ra’ba ya harbe shi a wani artabu kusa da garin Nsukka. Bayan nan ya hallaka Ifeajuna wai suna shirin yi masa juyin mulki a kasar Biafra. A dunkule Ojukwu da mutanen sa sun so danne yan Arewa ne, Allah bai basu dama ba.

Yakin Biafra


A shekarun baya irin wancan ra’ayi na bayar da kariya ga Ojukwu da mutane irin sa na fitowa ne daga kudu bangaren gabas. Ko a 1987 a wani littafi nasa mai suna “Nzeogwu” Chif Obasanjo ya bayyana Nzeogwu da mutumin kirki, mai saukin kai, mai hangen nesa da tausayi. To a yau gashi ‘yan Arewa sun fara, Sai muce Allah ya sauwaka. Don haka dalilan da zasu sa wani koyi da marigayi Ojukwu, koda kuwa ibo ne, marasa tushe ne. Balle kuma ace dan Arewa da yakai matsayin gwamnan jiha kuma jagoran wamnonin jihohi 19 da a baya suke karkashin kulawar Sardauna.

A dan haka, a bisa bayanan da suka gabata a baya, zamu fahimci cewar Ojukwu wani irin mugun mutum ne maketaci mai son tashin hankali da rashin san zaman lafiya, kuma Ojukwu zaka iya kwatantashi da wani irin mugun makiyin Arewa na bugawa a Jarida, duk da irin waccan mugunta da kiyayya da keta ta Ojukwu da bata bar ‘yan kabilar Ibo ba, to wai har wani mutimin Arewa da yake takama da cewa shi ne magajin Sardauna a yanzu domin shi ne yake jagorancin Gwamnonin Arewar su Sardauna zai dinga maganganun kariya ga Ojukwu da nuna cewa shi mutumin kirki ne. Anya kuwa wannan mutumin ba Inyamuri bane da rigar Hausawa? Ko kuma irin inyamuran nan ne da aka Haifa a Arewa kamar yadda shi kansa Ojukwu din a jihar Neja inda Babangida Aliyu yake Gwamna aka haifar, Lallai ina mai cike da shakkun cewar da kyar idan Babban Hadimin jihar Neja kamar yadda ya kira kansa shi ma ba Inyamuri bane haihuwar Arewa. Amma dai komai daren dadewa tarihi baya karya.

Akwai da yawa daga cikin Inyamurai da suke da waccan muguwar Aqidah ta kakkabe mutanan Arewa daga harkar Gwamnati kamar yadda Ironsi da Ojukwu suka nuna aiwatarwa, domin sojojin da suka kashe su Balewa da Sardauna da Zakariya Maimalari dasu Akintola daga Bangaren Yamma ai duk sai da Ironsi ya yi musu Karin girma, sannan ya zabge sojojin Musulmi ‘yan Arewa da kuma Musulmi daga bangaren Yamma na Yarabawa, sannan ya yi Karin girma ga mutum 25 kamar yadda muka bayyana a baya amma mutum 3 ne kcal Musulmi ‘yan Arewa a yayin da mutum 1 ne kacal daga yankin Yamma na Yarbawa.

To, tarihi fa shi yake maimaita kansa. Yanzu irin waccan muguwar Aqida ta su Ojukwu da Ironsi, ita shugaban sojojin Najeriya na yanzu Laftanar Kanar Azubuike Ihejirika yake aiwatarwa a kaikaice. Inda, idan bamu manta ba, a kwanakin baya ya zabge manya-manya sojojin kasarnan Musulmi gaba dayansu Hausawa da Yarabawa kuma, ya maye gurbinsu da Inyamurai gabaki daya babu kunya babu tsoron Allah, Shugaban kasa kuma yana ji yana gani ya kashe kunnensa domin dadawa Inyamurai kamar yadda a kullum yake nuna cewar shi fa nasu ne.

Haka kuma, a irin yadda ake kwashewa ‘yan Arewa Musulmi kafafu a dibar sojoji a makarantar horon soji ta NDA dake Kaduna zaka kara fuskantar akwai wasu boyayyun lamura a harkar tafiyar da al’amarin soja a kasarnan, domin a mafiya yawancin jihohin da suke da Kiristoci sai da aka fifita su akan Musulmi a wajen daukar adadi; Duk wannan fa yana faruwa bayan irin yadda ake yi mana kisan Mummuke da sunan farautar ‘yan Ta’adda a yankin Arewa maso gabas, wanda rahotanni sun nuna cewar galibin sojojin da aka jibge a wannan yanki Inyamurai ne ‘yan kabilar Ibo, suke ta karkashe mana mutane babu ji babu gani da sunan ta’addanci, wanda ko a baya-bayannan sai asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri ya bayar da sanarwar cewar sojojin rundunar JTF sun kawo gawarwakin mutane sama da 3000 asibitin a cikin kasa da shekara daya! Lallai akwai lauje a cikin kunshin rundunar sojojin Najeriya.

A saboda haka, ya zama dole Mu ‘yan Arewa mu yi karatun baya mu tuna abubuwan da suka faru a baya, sannan mu kalli abubuwan da suke faruwa a yanzu da wadanda zasu iya faruwa a nan gaba, dan tunanin Makomarmu, idan kuwa ba haka ba, muna ji muna gani Ojukwu zai dawo da wata rigar daban ya kashe na kashewa iya san ransa, wadan da suka yi saura kuma ya tarwatsa zuwa kasashen Nijar da Chadi da Kamaru kamar yadda a bayyane take cewar da yawan ‘yan Jihar Borno suna samun mafaka a wadannan makotan kasashe.


ME YA FARU BAYAN WANNAN RAWA DA OJUKWU YA TAKA TA KIFAR DA GWAMNATIN SU BALEWA DA KARKASHE SU?

SHI NE  YA TAYAR DA KURAR YAKIN BASASA A TSAKIYAR SHEKARAR 1967 BAYAN DA GOWON YA ZAMA SHUGABAN KASA.

YAKIN DA YA YI SANADIYAR HASARAR RAYUKA MASU DIMBIN YAWA.

MAI SON SANIN YADDA AKAI YAKIN SAI  YA KARANTA LABARIN A NAN KASA.


KARANTA MUKALOLI MASU ALAKA:

KARANTA CIKAKKEN TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN BIAFRA

KARANTA TAKAITACCEN TARIHIN YAKIN DUNIYA NA DAYA

TAKAITACCEN TARIHIN ATTAJIRIN DA YAFI KOWA KUDI A DUNIYA

KARANTA YADDA RAYUWA TA KASANCE A AREWACHIN NAJERIYA KAFIN ZUWAN TURAWA



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user