Friday 5 July 2019

KARANTA HIKAYAR WATA RANA A KASAR HAUSA KASHI NA DAYA: HIKIYA MAFI NISHADANTARWA A TARIHIN DUNIYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Shekaru daruruwa da suka gabata, tarihi ya nuna cewa qasar hausa na karbar baquncin fararen fata wadanda akasarin su Larabawa ne, da kuma mutanen hadaddiyar daular Ottoman, wadanda ake kira da Turkawa, masu zuwa siye da siyarwa.

Wata Rana a Kasar Hausa



Marubuci: SADIQ TUKUR GWARZO


A wani lokaci irin haka, anyi wani shahararren Falke wanda yake tasowa daga Birnin Ankara izuwa kasashen hausa, sunan sa Mehmet. Sana'ar sa itace fatauci, don haka a wannan lokacin Mehmet yana zuwa kasashen hausa ya siyarwa da sarakuna kayan sawa na alfarma, kayan fada da kayyakin Alatu. Shi kuma yana siyen bayi daga wurin su ya taf da su kasashen larabawa ya siyar.

Mehmet yana da wani da matashi mai suna Abdulkarem, wanda yake matukar kauna. Har ma shi yake dorawa akan duk wani abu nadukiyarsa. Rannan kaddara Abdulkarem ya kamu da wata cuta, ashe cutar ajali ce, babu jimawa rai yayi halin sa.
Hakika, mutuwar Abdulkarem tayi matukar dugunzuma Mahmet, amma kasancewar sa musulmi, sai ya dangana ga Sarki Allah. Daga nan kuma sai ya jawo wani bawa mai suna Ishaqa wanda yake amini ne na qut da qut ga marigayi Abdulkarem ya maisheshi tamkar da. Duk wani abu da Abdulkarem yake yi masa, sai Ishaqa ya zamo yana kamantawa.

A Wata shekara, Mehmet kamar yadda ya saba, ya keto ta Libiya daga Ankara, ya sauka a Damagaran, sai dai jikin sa na masa nauyi, wannan yasa yaji tsoron qarasawa cikin kasar hausa, ya yanke shawarar zai tura Ishaqa ya wakilce shi a kasuwancin da suka saba, shi kuma zai huta anan damagaran, in yaso idan yaji dama-dama sai ya gangara Kukawa dake Masarautar borno ya taba kasuwanci ya dawo Damagaran ya jira su.

Haka kuwa akayi, Ishaqa ya zamo jagora, ya taso da tawaga suka biyo ta qasar sakkwato, yana tare da turkawa abokanan mehmet, da dakaru masu yi musu rakiya da kariya, wadanda suke dauke da bindigu, takubba da sauran kayan fada don gudun Mahara da 'yan fashi. Duk da dai suna da kyakkyawar alaqa da sarakunan kasar hausa, amma 'yan ta'adda na iya yi musu kwanta-kwanta su karbe dukiyoyin su.

A kwana a tashi, Ishaqa da tawagar sa ta Iso birnin Kano. Daman bisa al'adar su sukan tsaya a babban gari suci kasuwa su kuma baiwa sarkin garin kyauta. Amma da yake Mehmet yana da babbar alaka da Sarkin kano na lokacin, kyautar sa tana zamowa ta musamman, kuma sau tari, daga kano kukawa suke qarasawa, amma da yake sun raba tafiyar da mai gidansa, wannan na nuna cewa a bana iya kacin tafiyar su Kano.
Da isar su birnin kano, suka aika wani baran su domin yayi musu iso. Babu jimawa kuwa akace Sarki na maraba dasu, don haka suka dunguma izuwa cikin gari.
Tun daga kofar gari Ishaqa da mutanen sa suka lura da sauyi a garin. Gashi dai an qawata gari kamar ana wani qwarya-qwaryan biki, amma kuma gidaje da rumfunan kasuwa duk a rufe, ba kuma a ganin mutane a garin. A haka har suka isa fada.

Fadar ce suka gani cike da mutane. Ashe sarkin garin ne ya tara al'ummar sa duka yana musu jawabi.

Isar su keda wuya aka basu wuri a fadar, aka kuma shaida musu cewar su dan jira sarki ya kammala wani uzuri sannan ya saurare su.

Akan idon su Ishaqa Sarki keta zazzagawa al'ummar garin fada. Yana ta cika da batsewa. Su kuma al'ummar gari kowa yayi tsit, babu mai cewa kanzil. Ko da gyaran murya baka ji. Wanda hakan ke fayyace irin tsoron da jama'ar garin kewa sarkin nasu. Daga bisani bayan ya gama fadan, aka gabato da wani mutumi. Sarki ya umarci hauni ya sare kansa. Ai kuwa kafin kace kwabo sai ga jini yana tsartuwa, hauni ya raba kan mutumin da gangar jikin sa.
Wannan abu yayi matukar kidima turkawan dake tawagar ishaqa.

Kasancewar basa jin hausa sosai, sai suke tambayar ishaqa abin dake faruwa. Sai shima ya kusanci wani bafade da wannan tambayar.

Bafaden cikin tsoro murya kasa-kasa ya baiwa Ishaqa amsa da cewa "Ranka ya dade, akwai sarkin yaki gashi can Azaune, shine yayiwa sarki bajinta ta cinye wani Gari da yaqi. Wannan yasa Sarki ya yaba masa kuma yace ya zabi duk abinda yakeso sarki zaiyi masa. Sai sarkin yaqi yace babu abinda yakeso sama da a aura masa diyar wannan mutumi da aka sare kansa. Ita kuwa wannan yarinya duk garinnan babu kyakkyawa irinta. Sarki kuwa yace tilas haka ta yiwu, don haka yaune ranar da akasa za'a daura aure, amma kuma sai aka nemi amarya qasa ko bisa aka rasa.

Wannan yasa sarki yayi fushi yace ubanta ne ya boyeta, don haka ya yanke masa hukuncin kisa. Ita kuma gobe zai tura da rundunoni, yasha alwashin indai tana doron qasar nan sai an kamo ta"
Ishaqa ya girgiza kai alamar baiji dadin abin ba. Ya kalli mutumin da ake cewa shine sarkin yaqi, ya ganshi wani bijimi ne maras kyan gani. Gashi baki wuluk, da jajayen idanuwa sai muzurai yakeyi. Tabbas shima ya hango dalilan da zasu hana kyakkyawar budurwa ta auri wannan basumuden mummunan kato, ya tabbatar babu soyayya a lamarin, amma kasancewar tarbiyar da Mehmet ya basu itace kada su yarda su sanya baki cikin sha'anin mulkin wani sarki, sai kawai ya labartawa turkawan abinda ke faruwa sannan ya
gargade su da kada wanin su yace uffan.

Bayan sarki ya kammala ne, sai ya fuskanto su. Yayi musu lale marhabin yana mai tambayar ina abokin sa Mehmet ya shiga?
Ishaqa ya labarta masa halin daya baro Mehmet da kuma shawarar daya yanke. Daga nan kuma ya gabatarwa dasarki kayayyakin da mehmet din ya aiko su dashi wadanda suka hadar da manyan riguna da shimfidu na alfarma, da wasu dogayen bindigu tare da alburusan su, da tasoshi nacin abinci wadanda akayisu da azurfa, da dai makaman tansu. Sarki ya dube su cikin farin ciki yayi murna sosai. Sannan shima ya bada umarnin a hada musu bayi wadanda zasu tafidasu.

A wannan Rana dai 'yan tawagar ishaqa hutawa kurum sukayi. Kashe gari kuma suka shiga kasuwa. Anan ne kowa yake siyar da kayan dayake tafe dashi, tare da siyo abinda yake ganin yana da daraja a kasashen larabawa.

Bayan kwana biyu suka yi bankwana da Sarki, sannan suka hau dawakan su tare da yin haramar komawa Damagaran.

Basu jima suna tafiya ba sai wani baturke wanda yake aboki ne ga Mehmet mai suna Ottoman, ya matso kusa da Ishaqa yana cewa "Ishaqa Mujde, mujde ishaqa". Ma'ana "Inada wani kyakkyawan labari ishaqa" sai kuma ya gabatarwa da Ishaqa wata mace wadda ta lullube fuskarta da bakin mayafi.

Ishaqa ya tambayi Ottoman menene labarin? Kuma wacece haka? Shine ottoman din yake sanar dashi cewa ai wannan macen itace wadda ake nema a kano, kuma kawai ganinta sukayi acikin tawaga ba tare da sun san yadda akayi ta shigo ba. Don haka kasuwa tayi riba kenan, domin ya tabbatar da cewa ba qaramar daraja matar zatayi ba.

Nan take Ishaqa ya tsaida dokinsa, abinda ke nuni da kowa ma ya tsaya. Ransa a bace, ya kalli macen gami da daka mata tsawa, yace "yi maza ki fita daga ayari na, ba zaki janyo min masifa ba".

Matar nan ta rugo da gudu ta duqursa a gabansa tana magiya, ya taimaka ya kyale ta, yayi mata rai, saboda komawarta kano azaba ce. Har tana cewa "ya kai wannan shugaba mai adalci kaji tausayi na, kayi mini rai, bani da kowa a duniyar nan, sun kashe mini mahaifina, sun karbe duk abinda muka mallaka, idan na koma hannun su mutuwa zanyi.."

Ishaqa yace ai sam bazai yiwuba. Saboda matsawar Sarkin kano yaji labarin sun tafi da ita zai iya biyo sawu, ko kuma zai iya yanke duk wata alaqar kasuwanci dake tsakanin sa da maigidansa Mehmet, shikuma ba zai taba son ya batawa ubangijin saba. Don haka sai ya umarci wasu dakarunsa da suyi gaggawar ciccibarta su mayarkano.

Tana kuka da birgima haka suka fincike ta, suka dora bisa wani ingarman doki, suka fita aguje zasu kaita kano.

Ana haka kuma sai Ishaqa ya fahimci hukuncin da ya dauka bai yiwa 'yan tawaga dadi ba, saboda duk tausayinta ya kamasu. Yayi jim yana tunanin mafita, shima kansa tausayin nata ya kamashi, sai kuma ya yanke shawarar canzatunani.

Saboda haka da kansa yabi bayan dakarun yana kwalla musu kira har saida ya tsayar dasu, sannan ya umarci a kyaleta a tawagar, amma da sharadin zata rinqa boye kanta don gudun kada a ganta akaiwa Sarki labari ya biyo bayansu. Daga nan sai suka ci gaba da tafiya.

Tun daga wannan lokacin, wannan matar take ta yunkurin zantawa da ishaqa. Shi kuwa sam bata gabansa, har kar sa kawai yakeyi. Daman mutum ne wanda bai cika son surutu ba.

Rannan kuwa sai akayi sa'a, tawaga ta yada zango, Ishaqa da Ottoman sun kebe suna fira, sai yaji ottoman yana magana da harshen turkanci, yana cewa "Guzellik Guzellik, ya subhanallah" Ma'ana, 'Kyakkyawa kyakkyawa, tsarki ya tabbata ga Allah'.

Ashe matar nan ce ta yaye fuskarta ta tunkaro inda suke domin tayi magana da Ishaqa. Da isowar ta tagaishe da ottoman, sannan na roqeshi izinin ganawa da Ishaqa. Don haka sai ya tashi ya basu wuri.

Ta dubi ishaqa, suka hada ido, ta sakar masa wani murmushi lallausa, sannan ta dukar dakai ta fara magana cikin ladabi, tana mai cewa "Ya shugaba, ina maka godiya bisa tausayi na da kaji har ka kyaleni acikin tawagar ka, kuma idan ka amince, inason labarta maka halin da nake cikine"

Ishaqa ya kura mata ido, saboda ya tsinci kan sa ne a wani yanayi wanda har yanzu bai san sunan saba. Ya gyada kai, alamar ya amince. Ita kuma sai ta cigaba da cewa "Da fari dai sunana Randiyya, mahaifina attajirine babba abirnin kano, wanda babu attajiri irinsa. Ni kuma nice kadai 'yarsa, mahaifiyata ta rasu tun ina karama.

Rannan sai gaba ta hadosu da Sarki a dalilin haraji. Sarkin yaqi ke zuwa karbar haraji wajen mahaifina. Shi kuma kamar yadda ya saba,bayan ya biya harajin, yana yiwa Sarkin yaki alheri mai yawa. To lokacin da yazo sai akayi rashin sa'a ya hangoni, ai kuwa sai ya kamu daso na. Yace idan har mahaifina zai yarda ya aura masa ni, to ya bar kara biyan haraji, kuma sai yaga bayan makiyansa duka. Shi kuma mahaifina yace gaskiya lokacin dazai aurad dani bai karasa ba, kuma zumunci yake so ya hadani da dan-dan uwansa.

Daga nan fa Ran sarkin yaki ya baci, yayi rantsuwa da cewa sai ya bakantawa mahaifina, kuma ko bayaso sai ya aureni. Daga nansai ya tafi ga sarki, ya shirya qarairayi wadda ta sanya Sarki yaji ya tsani mahaifina.

Sarki ya aiko gidan mu da cewa baya son zaman mu a garinsa. Don haka ya bamu kwana daya, mu hanzarta bar masa gari.
Cikin tashin hankali mahaifina ya nufi fada, yayi juyin duniyar nan, sarki yace sam bazai saurareshi ba, dole ne ya bar gari. Tilas mahaifina ya shiga hada kayan sa don fita daga garin.

Abin bakin cikin ma shine, sarki ya hana kowa daga mutanen garin amsar ajiya ko tsaron wani abu na daga dukiyar mahaifina. Ya kuma ba da shelar cewa idan kwana daya ta cika, kowa na iya zuwa gidan mu duk abinda ya samu ya zama ganima.

Mahaifina ya hada abinda zai iya dauka bisa dawakai, ba shiri yasa ni agaba da wasu amintattun bayin sa muka bargarin muna kuka. Fitar mu keda wuya sai muka mufi wani gari Marke inda Sarkin garin aboki ne ga mahaifi na.

Bayan kwana biyu, sarkin yaki ya kara zuga sarki akan cewa dole abi bayan mahaifina a kamo shi a daure, idan ba haka ba zai tara sadaukai yazo daukar fansa ga sarki. Don haka sarki ya baiwa Sarkin yaqi izinin aiwatar da wannan aiki, da nudin idan har sarkin Marke yayi turjiya, ya qone garin duka da abinda ke cikinsa.

Hakan kuwa akayi, Sarkin Marke yace bazai sallama muba sai dai ayi duk wanda za'ayi. Sadaukan sarkin yaqi suka rufarwa garin da fada, suka shiga kisa ba babba ba yaro, suna kone gidaje. Akarshe sarkin Marke ya gudu mu kuma suka samu nasarar kama mugami da komar damu kano.

Ala dole mahaifina yace ya gamsu ayi aurena da sarkin yaqi domin a zauna lafiya. Sarki yace to zai yafe masa laifin sa idan har akayi auren lafiya, amma idan wani abu mummuna ya auku, to tilas sai ya halaka shi a gaban dumbin jama'a.

Daga baya mahaifina ya yanke shawarar daya hada jinin sa da azzalumi irin sarkin yaki, gara ya mutu. Don haka ya nemi wani bafade wanda ya shirya sace ni tare da shigar dani tawagar ku. Da ranar daurin auren kuma tazo sarki bai ganniba, shine yasa aka sare kan mahaifina.

Ta kare da cewa " a yanzu haka na mika wuya a gareka, ina rokon taimakonka. Ba ni da wani gata idan ba kaiba. Ka taimakeni na isa Damagaran, akwai dan uwan mahaifina da yake fatauci acan, wajensa nake son komawa.

Ishaqa yayi ajiyar zuciya yana mai tausawa Kyakkyawa Randiyya. Ya kalleta cike da jimami, yace "Hakika na tausaya halin da kika shiga. Kuma ina sanar miki da cewa a shirye nake na taimake ki dom ki tsira daga sharrin wadannan azzalumai. Amma fa ki sani, wannan lamri yana da matujar hatsari. Kinga dai ni yaron gida ne, wakilci nakeyi, don haka nake kaffa-kaffa da rayukan wadanda nake jagoranta gami da dukiyoyin su. A yanzu kuma muna cikin wani lokaci, sarakunan mu basu da tausayi.

Akan ki yaki zai iya barkewa
tsakanin Damagaran da kano, duk da daman nasan sukan fafata jefi-jefi.. Gashi kuma labari baya buya, ina tsoron kada aje a sanar da Sarkin kano cewa kina cikin tawagar mu, nasan tabbas sai ya biyo bayan mu.."
"Ni dai ka zama gatana" Randiya ta fada.

"Allah shine gatan mu Randiyya.." inji Ishaqa. Sai ya qara da cewa " Amma ki kwantar da hankalinki, da yardar mai duka zaki kubuta" itama Randiyya ta nemi sanin tarihin sa amma yace kada ta damu, zai sanar da ita.

Sannu a hankali tawaga na cigaba da tafiya tana kusantar Birnin damagaran,
Shaquwa ta fara aukuwa tsakanin Ishaqa da Randiyya, har ya kasance kusan koda wanne lokaci suna tare da juna. Ayi raha ayi firar duniya. Wannan ne ya fara daukewa Randiyya bacin ran da take ciki, hankalinta ya fara kwanciya.

Wata rana suna tare, sai Randiyya take cewa "Ya shugabana, naga kamar kai ba bahaushe bane, wataqila baka san rike zumunta ta hausawa ba.. Idan ka shirya, zan baka wani labari"

Ishaqa yayi murmushi, yace "na gane wayon ki ay, so kikeyi kibugi ciki na na baki tarihi na, ni kuma nace miki lokaci baiyi ba, kawaidai idan kina da labari mai dadi ki bani"

Randiyya ta kyalkyale da dariya tana mai rufe fuskarta don kunya, sannan ta soma bashi labarin da cewa " A wani gari, anyi wasu abokan juna su biyu, wadanda suka amince da juna. Sai suka yanke shawar tafiya wani gari neman kudi. Akayi sa'a kuwa, garin da sukaje suka sami 'yan kudinsu, har ma kowannen su yayi aure.

Rannan sai suka ce ai kuwa ya kamata muje garinmu da matayen mu domin suga iyayen mu. Ai kuwa sai suka yi shiri suka kama hanya. Tinkis tinkis suna tafiya, sai dare yayi musu cikin wani daji. Sai daya abokin yace ai kuwa ya kamata su tsaya ana shikuma ya nemo musu karyo musu itacen da zasu kunna wuta, in yaso idan ya samu 'ya'yan itatuwa ma zai hado musu dashi.

Tafiyar sa keda wuya sai ga Zaki ya qaraso wurin, yana gurnani, matan nan duk suka rude, shikuwa namijin yayi ta maza ya zare wuka ya durfafi zaki. Kaca-kaca har ya samu nasarar halaka zaki.

Yana cikin hutawa sai yajiwo tafiyar abokin nasa yana dawowa, sai kuwa yace da matan su kwanta kamar sun mutu shi kuma ya tsayar da zakin kamar mai rai, domin ganin yadda abokin zaiyi.

Isar abokin keda wuya yayi kuwa, yace aikuwa rayuwa ta bata da amfani, tilas na rufarwa zakin nan in yaso ya kashe ni kamar yadda ya kashe min 'yanuwa. Da fadar haka sai ya rarumi zaki, sai dai ga mamakin sa sai ya tarar da zaki a mace, anan ne abokin da matan suka tashi suna masa dariya gami da jinjina masa. Kaji kadan daga amincin hausawa".


Za mu ci gaba Insha Allah.


KARANTA WANNAN: TUNDA NAKE BANKO TABAJIN LABARI MAI BAN TAUSAYI IRIN WANNAN BA






Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user