Sunday 26 May 2019

TAKAITACCEN TARIHIN ATTAJIRIN DA YAFI KOWA KUDI A DUNIYA: ABUBUWAN DA BAKU SANI BA GAME DA BILL GATES

Tura Wannan Zuwa Ga
Cikakken sunan sa shine william Henry 'Bill Gates' III.  An haifeshi a ranar 28 ga watan oktoba na shekarar 1955 a wani fari mai suna 'seatle' wanda yake qarqashin birnin washington DC dake qasar Amurka.



Attajirin da Yafi Kowa Kudi a Duniya.



Marubuci: Sadiq Tukur Gwarzo



Mahaifin Bill Gates Lauya ne, mahaifiyar sa kuma malamar makaranta.

Don haka tun yana qarami ya iya rubutu da karatu.

A wannan lokacin kuma ya fara karatun jaridu, har sha'awar kafa kamfani ya shiga ransa.

Bill Gates yana dan shekaru 13 ya soma ido biyu da na'urar kwamfuta.

Makarantar da yake karatu ce ta siyo ta. Dalibai na biyan kudi suyi amfani da ita na wani qayyadajjen lokaci.

Bill Gates ma sai ya biya nasa kudin, aka bashi lokacin amfani da ita.

Sai dai lokacin na qarewa, yayiwa kwamfutar wayo (daga nan ya fara hacking), akan dole ta bashi damar cigaba da amfanuwa da ita a kyauta.

Amma da akai rashin sa'a makarantar ta gano haka, sai ta koreshi.

Abu nagaba shine, Bill Gates ya samu damar shiga jami'ar Harvard bayan ya ci maki sosai a jarrabawar share fage.



Attajirin da Yafi Kowa Kudi a Duniya.




Ance maki 1600 ne qurewa a jarabawar mai suna SAT, amma sai gashi Bill Gates ya ciyo maki 1590, watau goma kurum ya fadi.

Alokacin bai ma san me zai karanta ba..

Wata rana yana karatun jarida sai ya hango tallar wani sabon kamfanin qere-qere.

Nan take ya dauki lambar su ya kirasu.

Yace yana musu tallar wata masarrafa (programme) idan zasu iya.

Sai kuwa suka ce suna so.


Alhali kuma bashi da masarrafar.


Daga nan sai Bill ya nemo abokinsa Paul domin su rubuta masarrafar.

Haka suka rinqa amfani da kwamfutocin jami'ar Harvard ba dare ba rana, da kyar suka rubuta ta.


Attajirin da Yafi Kowa Kudi a Duniya.



Da suka kammala, sai Bill ya sanyawa masarrafar suna BASIC, ya dauke ta ya nufi Mexico don karbo kudinta.

Anan aka biyashi kudi Dala dubu uku, amma da sharadin yana da ikon qara siyar wa wasu.

Sai dai ina son kusani, Bill gates bai kammala jami'ar Harvard ba, ba kuma don ya kasance daqiqi bane, sai dai kawai saboda karatun baya qayatar dashi, kwamfuta ita ke burgeshi.


Shekaru biyar bayan haka sai ga kamfanin IBM ya gurfana a gaban Bill, suna son ya rubuta musu masarrafa.

Kasancewar 'basic' bai gamsar dasu ba, sai ya shiga cigiya, har ya samo 'DOS' a hannun wani.

Ya biyashi kudin sa, shi kuma ya siyar musu dashi.


Attajirin da Yafi Kowa Kudi a Duniya.





Daga nan sai Steve Jobs (wanda ya qirqiri kamfanin apple) yazo. Shima ya nemi Bill Gates ya qirqiro sabbin masarrafai irinsu 'MS word' wadanda suka fi nada. Daga baya dai gayyar tasu ta watse. Amma dai Bill ya saci dabarun Steve jobs, da sune kuma ya qirqiri masarrafar 'windows'.


Bill Gates ya shiga kogin tunani akan abubuwan daya kamata a sanyawa kwamfuta don amfanuwar mutum a gida da ofis. Duk ya tattara abubuwan ya cusa su a wata masarrafa. Sai ya sanya mata suna 'windows'.

Daga nan ya fara siyar da masarrafar a kasuwa.

Ance Bill gates tun yana matashin sa a jami'ar Harvar yake shaidawa Furofesoshi malamansa cewa zai tsaya a gaban su yana matsayin babban attajiri a dai-dai sa'ar da zai cika shekaru talatin, sai dai burinsa na zamowa attajiri ya samu ne a lokacin daya cika shekaru talatin da daya.


Attajirin da Yafi Kowa Kudi a Duniya.



Cinikayyar Masarrafar windows ne ya bashi damar zamowa attajiri. Da kadan da kadan ne ya zamo attajiri na daya a sahun attajiran duniya alkacin yana da misalin shekaru 39.


Daga nan kuma ya shiga kyautar da dukiyar sa baji ba gani. Ya kafa gidauniya mai suna 'Bill and Melinda foundation' wanda suke gudanarwa dashi da matarsa, da kuma amininsa attajiri Warren Buffet.

Gidauniyar da take daukar nauyin karatun dalibai sama da 5000 duk shekara.

Take gina manyan dakunan gwaji na kimiyya a makarantu.

Take kuma biyan kudin bincike tare da bada kudin magani na manyan cututtuka da suka addabi duniya domin a rarrabasu kyauta.


A shekarar 2010, Bill Gates ya raba dukiyar sa biyu ya bayar da rabi da niyyar tallafawa marasa shi. Don haka sai aka daina jin duriyar sa a sahun attajirai.



Amma abin mamakin shine, a wannan shekarar ta 2016, ninkin dukiyar daya bayar kyauta guda biyu ne ya koma gareshi. Kuma qididdiga ta nuna cewar yafi kowa arziki a duniya.


A yanzu haka Bill Gate ya sanya hannu a wata yarjejejiya cewa duk sa'ar daya mutu, a sadakar da kashi cassa'in da biyar na dukiyar sa.

A baiwa iyalansa ragowar kaso biyar din dayayi saura.

Har yake cewa yayi imanin wadannan kudin zasu ishi 'yan nasa guda uku rayuwa mai inganci, tunda ya basu ilimi mai kyau.



Attajirin da Yafi Kowa Kudi a Duniya.




Wani lissafi da akayi, ya nuna cewar a duk daqiqa, kudin dake shiga aljihun Attajiri Bill Gates sun tasamma dala 250, a mintuna daya kuma dala 15000 ke shiga.

Dai-dai kenan da naira dubu hamsin a duk Sakan din agogo, kuma naira miliyan uku a duk minti daya.

Manzon Allah (s.a.w) yayi gaskiya da yace kyauta ke kara arziki.

Hadisi ya tabbatar da cewa a kullum akwai mala'ikan da yake roqon Allah Ta'ala yaninka dukiya ga dukkan mai kyauta ya kuma yi hani da dukkan mara yinta.

Allah yasa mu dace Amin.




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user