Sunday 26 May 2019

KARANTA LOKUTAN YIN SALLAH DA ADADIN SU

Tura Wannan Zuwa
ASUBAH: Sallah ce da ake yin ta raka'a biyu, Lokacin yin ta kuma shine bayan bullowar alfijir na gaskiya.


Sujjada a cikin Sallah




Sannan ana yin karatunta a bayyane, Fatiha da sura a kowacce raka'a sannan a yi tahiya ayi sallama.



AZZAHAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacin yin ta yana farawa idan rana ta bar tsakiyar sama ta karkata zuwa mafadarta.

Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.



Amma a ranar Juma'a sallar Azzahar tana zamowa sallar Juma'a a inda take komawa raka'a biyu kuma ana yin karatunta a bayyane, bayan liman ya kare khuduba.



LA'ASAR: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta na farawa daga inda inuwar abu tayi daidai da tsayinsa.

Sannan ana yin karatunta a asirce, Fatiha da sura a raka'o'in biyun farko, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.



MAGRIBA: Sallah ce da ake yin ta raka'a uku, lokacin yin ta shine idan rana ta fadi a mafadarta (a nan Najeriya fuskar yamma).

Sannan ana yin karatun raka'o'i biyun farko a Fatiha da sura amma a bayyane, sai a zauna a yi tahiya sannan a mike a yi raka'a daya ta karshe a karanta Fatiha kawai a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.



ISHA'I: Sallah ce da ake yin ta raka'a hudu, Lokacinta yana farawa ne idan shafaki ya buya (wato dan jaja-jajan nan na bayan faduwar rana idan gari ya fara duhu).

Sannan ana yin karatunta raka'o'in biyun farko Fatiha da sura a bayyane, sai a zauna a yi tahiya, sannan Fatiha kadai a raka'o'in biyun karshe a asirce, sannan a sake yin tahiya a yi sallama.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user