Showing posts with label BAYANI AKAN SALLAH. Show all posts
Showing posts with label BAYANI AKAN SALLAH. Show all posts

Friday, 15 November 2024

Manyan Falalolin Sallah Ga Rayuwar Kowanne Musulmi

Manyan Falalolin Sallah Ga Rayuwar Kowanne Musulmi

Allah ya farlanta wa al'ummar Annabi (S.A.W) salloli guda biyar a cikin kowacce rana, haka kuma ya shar'anta mana nafilfili da rawatib (nafilan bayan sallolin farilla) da witri waɗanda suke biye da farillai, saboda abin da yake cikinsu na amfani da fa'idoji da suke na dole a rayuwa, a rayuwa ta Addini da ta Duniya.


Manyan Falalolin Sallah
Hoto: Enter Islam

Allah ya ce:


{أَقِمِ الصَّلَاةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَى غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا } [الإسراء: 78]


"Ka tsayar da Sallah a lokacin da rana ta yi zawali (ta karkata daga tsakiyar sama), har zuwa duhun dare, da kuma karatun alfijir (Sallar Asubah), lallai karatun alfijir ya kasance abin halartowa ne".


Dukkan sallolin farilla guda biyar sun shiga cikin wannar ayar, saboda Sallar Azahar da La'asar suna cikin lokacin da yake bayan zawali zuwa farkon dare, Sallar Magriba da Isha'i kuma suna cikin lokacin duhun dare ne, sai kuma Sallar Asubahi da Allah ya kirata da karatun alfijir.


Kuma hadisai mutawatirai game da sallolin farilla sun zo da bayanin lokutansu da sharuɗansu da wajibansu da abin da yake cikasu, da kuma bayani a kan falalolinsu da yawan lada da sakamakonsu.


Daga cikin falalolinsu:


1. Su ne ibada mafi girma da bawa yake samun ƙasƙantar da kai ga Allah, da cikar zuciya da imani da Allan da girmama shi, wannan kuwa shi ne sinadarin rabautar zuciya rabauta ta har abada, da samun ni'imarta.


2. Sallah ita ce abincin zuciya mafi girma, da ruwan da yake shayar da bishiyar imani da jijiyoyinta da suke kafe a cikin zuciyar.


Ita Sallah tana tabbatar da imani a cikin zuciya, tana girmar da shi, kuma tana girmar da abin da yake ƙara imani na aikata ayyukan alheri, kuma tana hani a kan munanan ayyuka da sharri, kamar yadda Allah ya ce:


{إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ } [العنكبوت: 45]


3. Yana daga cikin falalolin sallah, kasancewarta ita ce mai taimako mafi girma a kan abin da zai amfani bawa a lamuransa na addini da rayuwa.


Allah ya ce:


{وَاسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ } [البقرة: 45]


"Ku nemi taimako (a kan dukkan lamuranku) ta hanyar yin haƙuri da yin sallah".


Taimakon da sallah take yi wa bawa a lamuransa na Addini:


Amma ta yadda sallah take taimaka wa bawa a maslahohinsa na Addini, lallai idan bawa ya dawwama a kan yin sallah ya kiyayeta, kwaɗayinsa a kan aikata ayyukan alheri zai ƙarfafa, kuma za ta sauƙaƙe masa ayyukan ɗa'a, da kyautatawa mutane cikin nutsuwar zuciya da neman sakamako a wajen Allah, kuma za ta tafiyar ko ta raunana masa abin da yake kai wa ga ayyukan saɓo.


Wannan kuwa abu ne da yake bayyana a zahiri, ake jinsa a jiki, saboda ba za ka ga wanda ya kiyaye sallah, na farilla da na nafila ba, face sai ka ga tasirin hakan a kan sauran ayyukansa, saboda haka ne sallah ta zama tambarin samun rabauta.


Amma kuma ta yadda take taimakawa a kan maslahohin duniya, shi ne ta yadda take sauƙaƙa wa bawa wahalhalu, kuma take sanyaya masa rai a kan masifu da suke samunsa, kuma Allah zai yi sakamako wa ma'abocin sallah da sauƙaƙe masa lamuransa na rayuwa, Allah zai sanya masa albarka a cikin dukiyarsa da ayyukansa da dukkan abin da yake haɗe da shi.


4. Daga cikin falalolinta, duk wanda ya cikata, kuma ya kyautatata to ya rabauta.


Annabi (S.A.W) ya ce:


"إن أول ما يحاسب به العبد يوم القيامة من عمله صلاته، فإن صلحت فقد أفلح وأنجح"


"Lallai farkon abin da za a fara yin hisabi wa bawa a kansa a ranar ƙiyama daga cikin ayyukansa shi ne sallarsa, idan ta gyaru to haƙiƙa ya rabauta kuma ya ci nasara".


Daga cikin littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.


Tushe/Asali: Zauren Ɗaliban Ilimi

Friday, 31 May 2024

Falalar Riga Liman Zuwa Masallacin Juma'a

Falalar Riga Liman Zuwa Masallacin Juma'a

Manzon Allah (SAW) ya ce: "Idan ranar Juma'a ta zo, a kowane ƙofar masallaci akwai Mala'iku , suna rubuta sunayen mutane ɗaya bayan ɗaya (gwargwadon lokutan da suka zo, daga wane sai wane a zuwa, to haka falalar da za su samu ya danganta da sammakonsu), idan Liman ya zauna sai su ɗage takardunsu, su zo su saurari huɗuba" Muttafaƙun alaih.


Falalar Riga Liman Zuwa Masallacin Juma'a
Hoto: NBC NEWS


{Wanda duk bai zo ba har sai bayan liman ya hau mimbari ya fara huɗuba, kenan bai samu shiga wannan rigista ba, to shi kam ya yi hasaran wannan falalar da waɗancan za su samu}.


A hanzarta a yi sammako domin a samu a shiga cikin rijistar Mala'iku.


Tushe/Asali: Zauran Ɗaliban Ilimi

Friday, 24 May 2024

Darajar Wanda Ya Je Sallar Juma'a Da Wuri

Darajar Wanda Ya Je Sallar Juma'a Da Wuri

Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Wanda ya zo a sa'ar Farko yana da ladar wanda ya yi Sadaka da RAƘUMI, a sa’a ta biyu kamar mai Sadaka da SANIYA, sa’a ta uku kamar sadakar RAGO, sa’a ta hudu kamar Sadaka da KAZA, sa’a ta biyar kamar mai Sadaka da ƘWAI ....” [Bukhari da Muslim].

DARAJAR WANDA YA JE SALLAR JUMA'A DA WURI
Ishraq fataftah


MarubuciyaFaridah Bintu Salis


KU YI SALATI GA MANZON TSIRA (ﷺ)

ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺻَﻞِّ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻛَﻤَﺎ ﺻَﻠَّﻴْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪٌ، ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﺑَﺎﺭِﻙْ ﻋَﻠَﻰ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﻣُﺤَﻤَّﺪٍ، ﻛَﻤَﺎ ﺑَﺎﺭَﻛْﺖَ ﻋَﻠَﻰ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﻭَﻋَﻠَﻰ ﺁﻝِ ﺇِﺑْﺮَﺍﻫِﻴﻢَ، ﺇِﻧَّﻚَ ﺣَﻤِﻴﺪٌ ﻣَﺠِﻴﺪٌ .


ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ
ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ ﷺ

Friday, 17 May 2024

Abubuwan Da Matafiyi Zai Iya Yi A Sallar Juma'a

Abubuwan Da Matafiyi Zai Iya Yi A Sallar Juma'a

1. Matafiyi yana iya bin sallar juma'a don ya samu falalar sauraron huɗuba, ya kuma rabauta da addu'ar Musulmi. Sai dai ba zai iya haɗa ta da sallar la'asar ba, domin sallar juma'a salla ce mai zaman kanta ba ita ce sallar azahar ba. Shi kuma haɗa salloli ana yin sa ne tsakanin Azahar da La'asar ko Magariba da Isha'i a lokacin ɗaya daga cikinsu.


Sallar Juma'a Ga Matafiyi ko Matafiya
Hoto: English Alarabiya





2. Idan matafiyi yana son haɗa sallar azahar da la'asar a ranar juma'a, to yana iya bin sallar juma'a da niyyar azahar, sannan sai ya haɗa ta da sallar la'asar, domin shi a wurinsa ya yi sallar azahar ce ba juma'a ba. Wasu daga cikin malamai sun hana sallatar juma'a da niyyar azahar, amma babu wata ƙwaƙƙwarar hujja a kan haka, domin saɓanin niyya tsakanin liman da mamu ba ya tasiri wajen hana bin sallar junansu, bisa zancen malamai mafi rinjaye.


3. Matafiyi zai iya limancin juma'a ga mazauna gari bisa zance mafi inganci. Domin kasancewar juma'a ba ta wajaba a kansa ba ba ya nufin rashin ingancin juma'arsa idan ya sallace ta, duk kuwa wanda sallarsa ta inganta to limancinsa ya inganta.


4. Ya tabbata cewa Sayyidina Mu'awiya (RA) ya yi tafiya zuwa wani gari da ake kira An-Nukhaila, kuma ya yi wa mutanen garin sallar juma'a. [Duba Ibn Abi Shaiba#5501]. Hakanan shi ma Sarki Umar Ɗan Abdul-Aziz ya je wani gari da ake kira As-Suwaida'u, tafiyar kwana biyu daga Madina, kuma ya ja su sallar juma'a duk kuwa da yana matafiyi. [Dubi Ibn Abi Shaiba#5500].

Friday, 10 May 2024

Karanta Hukunce-Hukunce 6 Na Sallar Juma'a

Karanta Hukunce-Hukunce 6 Na Sallar Juma'a

1.  GABATARWA

Kowane musulmi yana buƙatuwa ga sanin hukunce-hukuncen juma'a tunda ta bambanta da sauran salloli ta wasu mas'aloli, musamman ma limamai tunda su ne jagorori.

HUKUNCE-HUKUNCE 6 NA SALLAR JUMA'A
Hoto: Britannica


2. MAI GYANGYAƊI YAYIN KHUƊUBA

ANNABI (SAW) ya ce "idan gyangyaɗi ya kama ɗayanku a juma'a ya sauya wurin zama".

[AHMD,ABU-DAWUD,TRMZ,HKM DA ASSAHIHA]

3. SALATIN ANNABI A RANAR JUMA'A

ANNABI ya ce "daga mafificin yinnanku wunin juma'a, acikinsa aka halicci ADAM (AS) a cikinsa aka busa masa rai, a cikinsa za a yi ƙiyama- ku yawaita yi mini salati acikinsa domin za'a bijiro mini da ita"
[AHMD,ABU-DAWUD,NASA'I & IBN MAJAH"

4. YADDA IMAM ZAI YI ADDU'A AKAN MIMBARI

UMAAR BN RU'AIBAH ya ga BASHAR BN MAR'WAN ya ɗaga hannayensa biyu yana addu'a akan mimbari, sai ya ce: "ALLAH wadaran waɗannan hannayen, haƙiƙa na ga ANNABI yatsarsa na tahiyya yake ɗagawa yayin addu'a akan mimbari.".

[AHMD].

SHAUKANY ya ce: "Makruhine ɗaga hannaye yayin adu'a akan mimbari".

IBN TAIMIYYA ya ce: "Daga hannaye yayin addu'a akan mimbari makruhine domin ANNABI yatsansa yake ɗagawa sai dai idan zai roƙi ruwa yana daga hannayensa koda akan mimbari ne".

[AL-IKHTIYARATUL FIQHIYYAH-80].

5. TSABTA DA ZUWA DAWURI

ANNABI ya ce "Wanda ya yi wanka ranar juma'a ya shafa turare idan akwai, ya zo masallaci cikin nutsuwa ya yi nafila kuma bai cutar da kowa ba ya yi shiru ya saurari khudubar imam, an kankare masa laifukansa tsakaninsa da wata juma'a."

[AHMD,IBN-KHUZAIMA].

ANNABI ya ce e "Wanda ya zo a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da raƙumi 
ko saniya ko tinkiya ko kaza ko ƙwai. Idan imam ya fara huduba MALA'IKU za su nannade takardun.".

[BHR & MSLM]

6. IDAN IMAM YA YI KHUDUBA BA ALWALA

IBN QUDAMA ya ce: "Sunna ce yin huɗuba da alwala, idan imam yana huɗuba sai ya tuna ba shi da alwala sai ya kammala khudubar sai ya yi alwala ya ja sallah, haka ma IBN TAIMIYYA ya ce a MAJMU'UL FATAWA.

7. RUFEWA


Kada duniya ta ruɗe mu domin daɗinta kaɗan ne.

Mu yi guzuri da taƙawa domin muna da dogon bulaguro.

Kada mu kifu a duniya domin wanzuwa acikinta korarre ne.

Mutuwa dai ba ta suɓucewa kuma ba ta karɓan fansa kuma ba ta musanyawa ga wanda aka turo ta ta ɗauke shi.

TABBATACCIYAR MAGANA NE: Cewa za mu koma zuwa ga UBANGIJINMU ya yi mana tambaya akan ni'imomin da ya ba mu.

ME MU KA YI DA ITA ?

SHIN NI DA KAI DA KE MUN TANADI AMSAR DA ZA MU BAWA UBANGIJINMU ?

Tushe/Asali: Musulunci Hanyar Rayuwa