Friday 10 May 2024

Karanta Hukunce-Hukunce 6 Na Sallar Juma'a

Tura Wannan Zuwa Ga
1.  GABATARWA

Kowane musulmi yana buƙatuwa ga sanin hukunce-hukuncen juma'a tunda ta bambanta da sauran salloli ta wasu mas'aloli, musamman ma limamai tunda su ne jagorori.

HUKUNCE-HUKUNCE 6 NA SALLAR JUMA'A
Hoto: Britannica


2. MAI GYANGYAƊI YAYIN KHUƊUBA

ANNABI (SAW) ya ce "idan gyangyaɗi ya kama ɗayanku a juma'a ya sauya wurin zama".

[AHMD,ABU-DAWUD,TRMZ,HKM DA ASSAHIHA]

3. SALATIN ANNABI A RANAR JUMA'A

ANNABI ya ce "daga mafificin yinnanku wunin juma'a, acikinsa aka halicci ADAM (AS) a cikinsa aka busa masa rai, a cikinsa za a yi ƙiyama- ku yawaita yi mini salati acikinsa domin za'a bijiro mini da ita"
[AHMD,ABU-DAWUD,NASA'I & IBN MAJAH"

4. YADDA IMAM ZAI YI ADDU'A AKAN MIMBARI

UMAAR BN RU'AIBAH ya ga BASHAR BN MAR'WAN ya ɗaga hannayensa biyu yana addu'a akan mimbari, sai ya ce: "ALLAH wadaran waɗannan hannayen, haƙiƙa na ga ANNABI yatsarsa na tahiyya yake ɗagawa yayin addu'a akan mimbari.".

[AHMD].

SHAUKANY ya ce: "Makruhine ɗaga hannaye yayin adu'a akan mimbari".

IBN TAIMIYYA ya ce: "Daga hannaye yayin addu'a akan mimbari makruhine domin ANNABI yatsansa yake ɗagawa sai dai idan zai roƙi ruwa yana daga hannayensa koda akan mimbari ne".

[AL-IKHTIYARATUL FIQHIYYAH-80].

5. TSABTA DA ZUWA DAWURI

ANNABI ya ce "Wanda ya yi wanka ranar juma'a ya shafa turare idan akwai, ya zo masallaci cikin nutsuwa ya yi nafila kuma bai cutar da kowa ba ya yi shiru ya saurari khudubar imam, an kankare masa laifukansa tsakaninsa da wata juma'a."

[AHMD,IBN-KHUZAIMA].

ANNABI ya ce e "Wanda ya zo a lokaci na farko kamar ya yi sadaka da raƙumi 
ko saniya ko tinkiya ko kaza ko ƙwai. Idan imam ya fara huduba MALA'IKU za su nannade takardun.".

[BHR & MSLM]

6. IDAN IMAM YA YI KHUDUBA BA ALWALA

IBN QUDAMA ya ce: "Sunna ce yin huɗuba da alwala, idan imam yana huɗuba sai ya tuna ba shi da alwala sai ya kammala khudubar sai ya yi alwala ya ja sallah, haka ma IBN TAIMIYYA ya ce a MAJMU'UL FATAWA.

7. RUFEWA


Kada duniya ta ruɗe mu domin daɗinta kaɗan ne.

Mu yi guzuri da taƙawa domin muna da dogon bulaguro.

Kada mu kifu a duniya domin wanzuwa acikinta korarre ne.

Mutuwa dai ba ta suɓucewa kuma ba ta karɓan fansa kuma ba ta musanyawa ga wanda aka turo ta ta ɗauke shi.

TABBATACCIYAR MAGANA NE: Cewa za mu koma zuwa ga UBANGIJINMU ya yi mana tambaya akan ni'imomin da ya ba mu.

ME MU KA YI DA ITA ?

SHIN NI DA KAI DA KE MUN TANADI AMSAR DA ZA MU BAWA UBANGIJINMU ?

Tushe/Asali: Musulunci Hanyar Rayuwa 
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user