Tuesday 7 May 2024

Hanyar Da Za Ku Bi Domin Share Hawayen Masoyan Ku

Tura Wannan Zuwa Ga

A lokacin da masoyiyarka ko masoyinki ya faɗa a cikin wata damuwa, tabbas akwai buƙatar ganin kun share hawayensa, tare da ƙoƙarin ganin kun zamo sanadiyar dawo masa da farin-cikinsa da ya rasa. To amma ta yaya hakan zai samu? 


HANYAR SHARE HAWAYEN MASOYI/MASOYIYA
Hoto: Medical News Today 


MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Da akwai hanyoyi masu yawa da mutum zai iya bi, wajen ganin ya samu nasarar kawar da damuwar da masoyinsa ke ciki, kaɗan daga ciki kuwa akwai:


Lallashin masoyi da nuna tausayawa a kan halin da yake ciki da furta masa kalamai na soyayya masu taushi da sanyaya zuciya. 


A kan haka ma wani masanin al'amuran soyayya (S.I. Fatimiyya) ya ce:


"Babbar hanyar da ake bi wurin share hawayen masoyi ita ce, yin amfani da salo iri-iri na nuna ainahin damuwa da shi wannan masoyin. Ta hanyar yin amfani da kalaman kwantar da hankali. Ko ta hanyar yin amfani da kalaman soyayya. Sannan kuma da ta hanyar nuna tausayawa ga masoyin nan naka."


Ire-iren waɗannan kalamai kuwa, suna nan a cikin zuciyar kowane Ɗan-Adam, sai dai buƙatar tausasa harshe kawai. Misali:


Masoyiya Ta.


{Na san na yi miki laifi wanda har hakan ya sa kika yi fishi. To amma mene ne ya sanya kika bari fishinki ya kawo har zuwa tsawan wannan lokacin? Ko kin san adadin mutanen da fushinki ya sanya a damuwa kuwa? Tabbas, suna da yawa, daga cikinsu kuwa har da ni. Ki daure ki yafe min ki manta da komai, domin kuwa fishi ba zai yi maganin komai ba, kuma bai dace da ke ba.}


Masoyi Na.


{Na kwana cikin damuwa da tunanin irin halin da ka kwana a ciki masoyi na. Kai ne farin-ciki na, a dukkan lokacin da kake cikin damuwa na kan kasance cikin ƙunci da ƙunar zuciya. Zan so ka daure ka share dukkan damuwar zuciyarka. Na tuba ba zan ƙara ba, wancan ma a bisa kuskure ne.}


Waɗannan da kuma ire-irensu.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user