Sunday 5 May 2024

Hanyoyin Bambance Sana'a Domin Cimma Nasara

Tura Wannan Zuwa Ga

Idan aka yi la’akari da ma’ana, ba kowace sana’a ce za’a iya bambance ta ba. Bugu da ƙari banbance sana’a na da tsada, da ɗaukar lokaci kuma da matuƙar ƙalubale wajen cimmawa, sannan babu wuya ‘yan “kwafi kwafi” su kwafa.


BABBAN KALUBALEN BAMBANCE SANA’A
Hoto: Everyday Power


MarubuciBello Galadanchi


Idan aka tuna, kamfanin Apple ne ya fara suna wajen fito da waya da ake taɓawa a fuskarta, amma a halin yanzu kusan kowace waya ana taɓawa. Wani lokacin banbance sana’a ba ya kasancewa abin da ke bai wa sana’a tagomashi da fice na lokaci mai tsawo. 


Saboda tsabar wahalar nemo dabarar cimma banbance sana’a ta yadda dabarar za ta yi tasiri kuma ba za a iya kwaikwayar ta ba, wani masani a harkar talla mai suna Philip Kotler ya bada shawara ga masu sana’a yana mai cewa a mayar da hankali akan batutuwan da ke taɓa zuciyar mutane. Bari na yi bayani, wato masu sana’o’i su yi talla domin ƙulla soyayya tsakanin zuciyoyin kwastomomi da sana’ar, ta yadda su kwastomomin da kansu ne za su ringa bambance sana’ar daga saura komai kamanninsu.


Misali, irin tsari da zane da fasalin takalmin Nike da Adidas sun fita daban, amma banbancin su kaɗan ne ta yadda da ƙyar mutum zai iya banbance su ta fannin amfani da inganci. Amma a zuciyar kwastomomin waɗannan kamfanoni guda biyu, banbancin takalman na da yawa, kuma suna kishin kamfanonin da suke goyon baya. 


Shi ma kamfanin Apple ya banbance kanshi ne a ɓangaren sautin kaɗe-kaɗe a lokacin da ya ƙirƙiro manhaja mai sauƙin amfani da ita kanta na’u’rar sauraron sauti (iPod) mai kyau da inganci da ya ƙara bai wa kwastomomi jin daɗin amfani. Shi kanshi iPod ɗin ba shi ne na'urar sauraron sauti na farko ba saboda akwai MP3 da yawa a wannan lokaci, amma saboda irin manhajar da yake da shi, ya bai wa kwastomomi yanayin amfani mai daɗi wanda ragowar MP3 ba su bayar ba. Ta yaya za ka banbance sana’ar ka ta yadda za ka yi fice? 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user