Showing posts with label Koyarwar Addinin Musulunci. Show all posts
Showing posts with label Koyarwar Addinin Musulunci. Show all posts

Sunday, 1 December 2024

Hukuncin Wanda Ya Ƙi Fitar Da Zakka

Hukuncin Wanda Ya Ƙi Fitar Da Zakka

Mai ƙin fitar da zakka iri biyu ne: Kodai ya ƙi bayarwa ne saboda bai yarda wajibi ba ce, ko kuma ya ƙi bayarwa ne saboda tsananin rowa da son abin duniya.


Hukuncin Wanda Ya Ƙi Fitar Da Zakka
Hoto: Royal group charity

Idan ya ƙi bayarwa ne saboda bai yarda da wajibcinta ba, to ya kafirta. Idan kuwa don rowa ne, ko sakaci to fasiƙi ne. Kuma hukuma za ta iya karɓa ta ƙarfi daga gare shi.


Kamar yadda Khalifan Annabi (S.A.W), wato Abubakar (R.A) ya yaƙi waɗanda suka ƙi bayarwa a zamaninsa. (Duba Zakatul Ma’adni na Almukhtar bin Umar bin Al-Hussain As-Shankidi Sh:18-19).


Kuma ya kamata mu sani cewa, ƙin bayar da zakka yana sabbaba azaba mai muni ga mutum a lahira.


Ga dai hadisin da Muslim ya rawaito game da haka:


عن أبي هريرة قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: "ما من صاحب كنـز لا يؤدي زكاته إلا أحمى عليه في نار جنهم فيجعل صفائح فتكوى بها جنباه ووجهه حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقدار خمسين ألف سنة. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار. وما من صاحب إبل لا يؤدي زكاته إلا بطح لها بقاع قرقر. كأوفر ما كانت تستن عليه كلما مضى عليه أخراها ردت عليه أولاها، حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار. وما من صاحب غنم لا يؤدي زكاتها إلا بطح لها بقاع قرقر كأوفر كانت فتطؤه بأظلافها وتنطحه بقرونها ليس فيها عقصاء ولا جلجاء. كلما مضى عليه آخرها ردت عليه أولاها حتى يحكم الله بين عباده في يوم كان مقداره خمسين ألف سنة مما تعدون. ثم يرى سبيله إما إلى الجنة وإما إلى النار...".


Fassara


Daga Abu Huraira (R.A) ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Babu wani mai taskace kuɗi, wanda ba ya bayar da zakkarsa, face sai an ƙona shi (kuɗin) a wutar Jahannama ya yi faɗi sannan a dinga goga masa a gyaffansa da fuskarsa; har lokacin da Allah zai yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawon shekara dubu hamsin. Sannan a nuna masa hanyarsa, kodai zuwa aljanna ko kuma zuwa wuta.


Babu wani mai raƙuma wanda ba ya bayar da zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai faɗi, cikakkunsu. Sannan su dinga bi ta kansa. Idan suka kai ƙarshe, sai a dawo da na farkon, haka za a dinga yi masa, har Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayinSa. A yinin da ya ke kwatankwacinsa tsawon shekara dubu hamsin.  Sannan sai a nuna masa hanyarsa, kodai zuwa Aljanna ko zuwa wuta.  Babu wani mai tumaki ko awaki wanda ba ya bayar da zakkarsu, face sai an jefa shi a cikinsu, a wani kwari mai faɗi, cikakkunsu. Sannan su dinga taka shi da kofatansu, suna sukansa da ƙahunnansu.


Babu mai tanƙwararren ƙaho a cikinsu, balle marar ƙahon.  Idan suka kai ƙarshe, sai a dawo da na farkon, haka za a dinga yi musu, har Allah Ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, a yinin da yake kwatankwacin tsawonsa shekara dubu hamsin. Sannan sai a nuna masa hanyarsa, kodai zuwa Aljanna ko zuwa Wuta…”. (Duba Nailul Audar na Shaukani, juz’i 2, sh:172-173).

Saturday, 30 November 2024

Sharuɗɗan Wajabta Bayar Da Zakka

Sharuɗɗan Wajabta Bayar Da Zakka

Dangane da abin da ya gabata, za mu fahimci cewa, tsabar kuɗi da kayan sayarwa suna buƙatar sharuɗa biyar kafin a fitar musu da zakka, su ne: Musulunci, ‘yanci, mallaka, cikar nisabi, da cikar shekara. Idan kuwa zakkar dabbobi ce, to, sai a ƙara sharaɗi ɗaya shi ne, kasancewa suna fita kiwo. Ba a ɗaure su ana nemo musu abinci ba, (watau ba turkakku ba).


Sharuddan Wajabta Bayar Da Zakka
Hoto: Sumit2k1b3/Freepik

Haka kuma idan amfanin gona ne, to shi ma sai a ƙara sharaɗi ɗaya, wato ya kasance abinci ne ga Ɗan Adam amma a fitar da sharaɗin cikar shekara. (Duba Al-FiKhul Muyassar na Ahmad Isa, juz’i, 1, sh;220-222).

Friday, 15 November 2024

Manyan Falalolin Sallah Ga Rayuwar Kowanne Musulmi

Manyan Falalolin Sallah Ga Rayuwar Kowanne Musulmi

Allah ya farlanta wa al'ummar Annabi (S.A.W) salloli guda biyar a cikin kowacce rana, haka kuma ya shar'anta mana nafilfili da rawatib (nafilan bayan sallolin farilla) da witri waɗanda suke biye da farillai, saboda abin da yake cikinsu na amfani da fa'idoji da suke na dole a rayuwa, a rayuwa ta Addini da ta Duniya.


Manyan Falalolin Sallah
Hoto: Enter Islam

Allah ya ce:


{أَقِمِ الصَّلَاةَ لِدُلُوكِ الشَّمْسِ إِلَى غَسَقِ اللَّيْلِ وَقُرْآنَ الْفَجْرِ إِنَّ قُرْآنَ الْفَجْرِ كَانَ مَشْهُودًا } [الإسراء: 78]


"Ka tsayar da Sallah a lokacin da rana ta yi zawali (ta karkata daga tsakiyar sama), har zuwa duhun dare, da kuma karatun alfijir (Sallar Asubah), lallai karatun alfijir ya kasance abin halartowa ne".


Dukkan sallolin farilla guda biyar sun shiga cikin wannar ayar, saboda Sallar Azahar da La'asar suna cikin lokacin da yake bayan zawali zuwa farkon dare, Sallar Magriba da Isha'i kuma suna cikin lokacin duhun dare ne, sai kuma Sallar Asubahi da Allah ya kirata da karatun alfijir.


Kuma hadisai mutawatirai game da sallolin farilla sun zo da bayanin lokutansu da sharuɗansu da wajibansu da abin da yake cikasu, da kuma bayani a kan falalolinsu da yawan lada da sakamakonsu.


Daga cikin falalolinsu:


1. Su ne ibada mafi girma da bawa yake samun ƙasƙantar da kai ga Allah, da cikar zuciya da imani da Allan da girmama shi, wannan kuwa shi ne sinadarin rabautar zuciya rabauta ta har abada, da samun ni'imarta.


2. Sallah ita ce abincin zuciya mafi girma, da ruwan da yake shayar da bishiyar imani da jijiyoyinta da suke kafe a cikin zuciyar.


Ita Sallah tana tabbatar da imani a cikin zuciya, tana girmar da shi, kuma tana girmar da abin da yake ƙara imani na aikata ayyukan alheri, kuma tana hani a kan munanan ayyuka da sharri, kamar yadda Allah ya ce:


{إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ } [العنكبوت: 45]


3. Yana daga cikin falalolin sallah, kasancewarta ita ce mai taimako mafi girma a kan abin da zai amfani bawa a lamuransa na addini da rayuwa.


Allah ya ce:


{وَاسْتَعِينُوا بِالصَّبْرِ وَالصَّلَاةِ } [البقرة: 45]


"Ku nemi taimako (a kan dukkan lamuranku) ta hanyar yin haƙuri da yin sallah".


Taimakon da sallah take yi wa bawa a lamuransa na Addini:


Amma ta yadda sallah take taimaka wa bawa a maslahohinsa na Addini, lallai idan bawa ya dawwama a kan yin sallah ya kiyayeta, kwaɗayinsa a kan aikata ayyukan alheri zai ƙarfafa, kuma za ta sauƙaƙe masa ayyukan ɗa'a, da kyautatawa mutane cikin nutsuwar zuciya da neman sakamako a wajen Allah, kuma za ta tafiyar ko ta raunana masa abin da yake kai wa ga ayyukan saɓo.


Wannan kuwa abu ne da yake bayyana a zahiri, ake jinsa a jiki, saboda ba za ka ga wanda ya kiyaye sallah, na farilla da na nafila ba, face sai ka ga tasirin hakan a kan sauran ayyukansa, saboda haka ne sallah ta zama tambarin samun rabauta.


Amma kuma ta yadda take taimakawa a kan maslahohin duniya, shi ne ta yadda take sauƙaƙa wa bawa wahalhalu, kuma take sanyaya masa rai a kan masifu da suke samunsa, kuma Allah zai yi sakamako wa ma'abocin sallah da sauƙaƙe masa lamuransa na rayuwa, Allah zai sanya masa albarka a cikin dukiyarsa da ayyukansa da dukkan abin da yake haɗe da shi.


4. Daga cikin falalolinta, duk wanda ya cikata, kuma ya kyautatata to ya rabauta.


Annabi (S.A.W) ya ce:


"إن أول ما يحاسب به العبد يوم القيامة من عمله صلاته، فإن صلحت فقد أفلح وأنجح"


"Lallai farkon abin da za a fara yin hisabi wa bawa a kansa a ranar ƙiyama daga cikin ayyukansa shi ne sallarsa, idan ta gyaru to haƙiƙa ya rabauta kuma ya ci nasara".


Daga cikin littafin Sheikh Ibnu Sa'adiy (r): Al- Riyadhun Nadhirah.


Tushe/Asali: Zauren Ɗaliban Ilimi

Monday, 28 October 2024

Karanta Yadda Ake Zakkar Amfanin Gona Ko Hatsi

Karanta Yadda Ake Zakkar Amfanin Gona Ko Hatsi

Malamai sun yi saɓani game da sharuɗɗan Zakkar amfanin gona.  Imamu Abu Hanifa cewa ya yi, duk abin da ake shukawa a ƙasa don amfan da shi to akwai Zakka a kansa. In ban da itatuwa da ciyayi da karmami.


Yadda Ake Zakkar Amfanin Gona Ko Hatsi
Hoto: Britannica

Shi kuwa Imam Ahmad sai ya ce, Zakka tana wajaba ne a kan duk abin da akan auna shi kuma ya kan bushe ya daɗe. Su kuwa Imamu Malik da Imamu Shafi’i, sai suka ce, zakka ba ta wajaba a kan amfanin gona sai wanda ake amfani da shi a matsayin abinci, kuma za a ajiye shi ya daɗe bai lalace ba.


Dangane da nisabi kuwa shi amfanin gona nisabinsa shi ne ya kai ‘wusuki biyar. Shi ‘wusuki’ ma’auni ne wanda kowanne ɗaya ya ke cin kwano sittin. Amma fa kwanon mai daidai da mudannabi huɗu. Watau a taƙaice dai idan aka ƙiyasta abin da aka noma aka ga zai kai kwano ɗari uku to ya wajaba a fitar masa da Zakka.


Game da abin da za a fitar kuwa, wannan ya danganta da irin ruwan da ya tsirar da amfanin. Idan da ruwan sama ya tsira, to sai a fitar da kashi ɗaya cikin goma. Idan kuwa ban ruwa aka yi, to sai a fitar da kashi ɗaya a cikin ashirin. Saboda faɗin Manzon Allah (S.A.W):


"فيما سقت السماء والعيون أو كان عثريا، العشر. وفيما سقي بالنضح نصف العشر".


“Abin da sama ta shayar, ko idanun ruwa, ko ya kasance mai jan ruwa ta jijiyarsa, to za a fitar da ɗaya cikin goma. Idan kuwa ban ruwa aka yi, sai a fitar da ɗaya cikin ashirin”. (Bukhari da Muslim suka rawaito.).

Saturday, 14 September 2024

Karanta Zafafan Kalaman Hikimomin Magabata Na Musamman Masu Dadin Gaske

Karanta Zafafan Kalaman Hikimomin Magabata Na Musamman Masu Dadin Gaske

Ba kowanne wayayye ne mai ilimi ba. Ba kuma kowanne mai ilimi ne yake da wayewa ba. Idan Allah ya ba ka ilimi nemi sanin duniya da zamanin da kake cikin sa sai ya zama kana da haske a kan haske. Idan kuma kana da wayewa da sanin duniya matsa kusa da malamai ka ƙara sani, sannan ne wayewarka za ta amfane ka.

Zafafan Kalaman Hikimomin Magabata Na Musamman Masu Dadin Gaske
Hoto: LinkedIn

Marubuci: Dr. Mansur Sokoto


Sarakunan da su ka yi mulkin duniya duk sun tafi ba su san wutar lantarki ba. Ba su sha ruwan firijin ba, balle su kunna fanka ko AC. Ba su hau keke ba, ballantana motoci da jirage. Ba su san abin da ake kira tarho ba ballantana wayar tafi-da-gidanka.


Duk hasken gidajensu a wancan lokaci bai wuce na kyandur da fitila mai amfani da kalanzir ba.

A yau kai sarki ne amma ba ka gamsu da abin da ka samu ba. Idan kana da mota ta maƙwabcinka kake kallo. Idan kana da gida na wani babban mutum kake kallo. Oh! Allah sarki. Ɗan Adam da buri yake mutuwa.

Sufanci na gaskiya ababe biyar ne: 1. Riƙo da Alkur'ani da Sunna 2. Kauce ma cin haram 3. Yin tuba ga Allah 4. Rashin cuta ma mutane 5. Bai wa kowa haƙƙinsa. - Sahl bin Abdillah At Tustaree.

Idan ka kasa gane wurin da ka yi shuka kada ka samu damuwa wata rana ruwan sama ne zai nuna maka. Shuka alheri ka wuce a can gaba za ka tsince shi.

Hattara da hawaye guda uku: Hawayen iyaye, da hawayen maraya, da hawayen wanda ka zalunta. Kowanen su hawayensa na iya nutsar da kai a cikin tekun bala'i.

Ɗan Adam na girma ne a matakai biyar: Zai fitar da haƙora idan ya kai shekaru bakwai, idan ya ƙara bakwai zai balaga, bayan wasu bakwai tsawonsa zai kammala, idan ya ƙara bakwai ya samu cikar hankali. Bayan haka sai kunne ya girmi kaka (Ma'ana rayuwa za ta karantar da shi abubuwa da dama daga nan har mutuwa ta zo masa). - Al Imam As Thauree.

Hattara da mabuɗai guda uku:
Fushi, mabuɗin azaba.
Tsoro, mabuɗin fitina.
Kwaɗayi, mabuɗin wahala.

Mala'iku su na da hankali ba su da sha'awa. Dabbobi suna da sha'awa ba su da hankali. Ɗan Adam ne Allah ya haɗa masa guda biyun. Idan hankalinka ya rinjayi sha'awarka ka bi sawun mala'iku. Idan sha'awarka ta zarce hankalinka ka shiga sahun dabbobi.

Matakan tsira biyar ne: Sanin Allah, Ƙaunar Allah, Tsoron Allah, Yarda da Allah, sai kuma gudun duniya. - Yahya bin Mu'adh.

Idan an yi maka ƙazafi ka tuna iyalin shugabanmu ma'aiki Sallallahu Alaihi wa Sallam. Kwana hamsin tana cikin sunu da takaici sai da Allah maɗaukaki ya wanke ta.

Allah ya yi mana kunnuwa biyu da idanu biyu amma ya yi mana baki ɗaya. Ko ka san dalili? Mahaliccinmu ya fi son mu yi kallo, mu saurara fiye da yadda mu ke magana.

Idan na ƙwarai da mugu su ka haɗu kowa ma yana iya gane bambanci. Amma a tsakanin na ƙwarai da wanda ya fi shi, da mugu da wanda ya fi, wannan sai ma su hankali ne su ke iya rarrabewa.

Ababe biyar su suka dace da biyar: A samu yaro yana a makaranta, Saurayi wajen neman abinci, Dattijo a masallaci, Mace a gidan aure, Mugu a kurkuku. - Al Hakeem At Tirmidhi.

Ba a sanin matsayin saurayi sai ya yi aure. Ba a sanin halin talaka sai ya wadata. Ba a sanin gaskiyar ɗan siyasa sai ya kai ga muƙami.

Idan kana jin kaɗaici ka tuna Annabi Adam Alaihis Salam. Ya zauna a duniya shi kaɗai ba kowa.

Idan ka sha wuya a wajen wa'azi da karantarwa ka tuna Annabi Nuhu Alaihis Salam. Shekarunsa dubu ba hamsin yana wa'azi.

Idan 'yan uwanka sun cuce ka ka tuna Annabi Yusuf Alaihis Salam. A cikin rijiya su ka jefa shi.

Idan matsalolin rayuwa sun dabaibaye ka, ka tuna Annabi Yunus Alaihis Salam. Kifi ne ya haɗiye shi amma ya samu kuɓuta a dalilin ambaton Allah.

Matsaloli da wahalhalun rayuwa ba su ne ƙarshen Ɗan Adam ba. Manya ma sun gamu da matsaloli kala-kala.

Abin damuwa shi ne matsalarka ta zama sanadin rabuwar ka da Allah mahaliccinka.

Idan ka kyautata ma mutum za ka mallake shi. 

Idan ka wadatu daga mutum za ka zama tsaran sa.

Idan kuwa ka buƙatu zuwa ga mutum, to dole sai ka zamo bawansa.

Kyawun hankali ya riƙa tunani.

Kyawun harshe ya riƙa faɗin gaskiya. 

Kyawun Budurwa kunya. 

Kyawun Yaro biyayya.

Idan kana cikin damuwa ka jira samun sauƙi daga wurin Allah, wannan jiran da kake yi ibada ne. Domin kyautata zato ne ga Allah. Wanda ya kyautata ma Allah zato kuwa lallai ne Allah zai ishe shi.

Wanda fuskar mata take ba shi sha'awa mata ɗaya ba ta isar sa. 

Amma wanda kyakkyawan hali yake so ɗaya ma sai ta ishe shi.

Alheri yana tattare ne a ababe biyar: Wadatar zuci da neman halal da tsoron Allah da kamun kai da barin cuta ma mutane. - Al Imam As Shafi'ie.

Idan ciwo ya addabe ka ka tuna Annabi Ayyub Alaihis Salam. Har sai da ya ji ƙamshin mutuwa a kan cuta.

Masana sun ce, lafiyar Ɗan Adam tana cikin samun ababe guda bakwai:

1. Samun isasshen hasken rana yana bugun jikinka.

2. Yawan shan ruwa (da rana).

3. Wadataccen bacci (da dare).

4. Shaƙar tatacciyar iska.

5. Shan Farar Zuma.

6. Tafiyar minti 30 a kullum da ƙafa.

7. Cin lafiyayyen abinci.

Idan za ka yi alheri ka gaggauta shi, ka sirranta shi, sannan kada ka yi gori. Wannan shi ne halin mutanen kirki!.

Akwai miliyoyin halittun Ubangiji waɗanda ba su da aljihu, ba asusun ajiya a gida ko a banki amma ba su daina cin arziki ba. Kwantar da hankalinka, arzikinka yana nan ba zai wuce ka ba. Nemi Halaliya, don ba ka wuce arzikinka, kuma saurin nema ba ya kawo samu.

Idan mahaifinka na tsanar ka a kan riƙon addini ka tuna Annabi Ibrahim Alaihis Salam. A kan haka ne ya sha wuya a hannun mahaifinsa.

A Hotel ake rubuta "Idan mun burge ka ka faɗa ma duniya. Idan mun ɓata ranka ka faɗa mana". Wannan shi ne yadda ya kamata ka yi hulɗa da kowane Musulmi ɗan uwanka.

Abu ɗaya ne kyakkyawa wanda ko makaho yana iya ganin sa, shi ne kyawun hali. Ka zama mai kyawun hali ba sai ka faɗi ba mutane da kansu za su yabe ka.

Da dare kowa ya na rufe ƙofarsa ne don tsoron mutane. A lokacin ne kuma Allah ya ke buɗe ƙofofinsa don karɓar mutane. Ko kana ƙwanƙwasa ƙofarsa ta hanyar salloli da zikiri da addu'o'i da tilawa a wannan lokaci?

Idan ba ka iya yin sadaka daga abin aljihunka ba to ka yi sadaka daga cikin haƙoranka. Murmushi ga fuskar ɗan uwanka shi ma sadaka ne.

Kada jin daɗin wani ya tsone ma ido, ba ka san abin da ya rasa ba kafin Allah ya ba shi wannan ni'ima da yake cikinta. Kada damuwarka ta tada hankalinka, ba ka san alherin da za ta jawo ma ka ba. Haƙuri maganin zaman duniya.

Idan ka makara a wajen aiki kana jin kunyar shugabanka. Idan ka makara zuwa masallaci ko kana jin kunyar Allah?

Idan yaro ya yi wayo kyawunsa a sa shi makaranta. Idan ya girma kyawunsa a gan shi a masallaci. Mace ita kuma kimarta idan ta girma tana a gidan mijinta.

Kamilin mutum shi ne wanda ya tara ababe guda uku: Ga kyauta ga daɗin zama ga kuma yawan ibada.

Karatu akwai wuya, ilimi akwai daɗi. Nema akwai wuya, arziki akwai daɗi. Zama da Jahilci ba wuya, rashin ilimi akwai takaici. Haka duniya take, yaro ɓata hankalin dare ka yi suna!

Na samu wannan a cikin wani ɗan nazari da nake yi na ga ya dace kada na yi maku rowar sa.