Tuesday 28 May 2019

Karanta Ka Ji: Babban Dalilin da Yasa Ban Shiga Harkar Siyasa Ba - Nafisa Abdullahi

Tura Wannan Zuwa
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi wadda aka fi sani da ‘Nafisa Sai Wata Rana’ a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, ta ce ta ki yi wa kowane dan takara kamfe ne saboda ba ta so ta tilasta wa masoyanta su zabi ra’ayinta.


Nafisa Abdullahi



Nafisa ta bayyana haka ne a wata hira da shafin sadarwa na Kannywoodscene a makon jiya.


A lokacin da aka tambayi jaruma Nafisa wadda ta fara fitowa a fim tana ’yar shekara 19  a cikin wani fim mai suna ‘Sai Wata Rana’ a shekarar 2010 kan dalilin da ya sa ba ta shiga tafiyar ’yan fim da suke yi wa ’yan siyasa kamfe ba, sai ta ce, “Ba na so in tilasta wa masoyana su zabi dan takarar da nake yi wa kamfe, na fi so su zabi ’yan takarar da su suke so.”


Da aka tambaye ta ko me ya sa ba ta nuna goyon baya ga Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ko wanda ya yi wa Jam’iyyar PDP takara, wato Abba Kabir Yusuf ba, sai ta ce, “Wannan ba hurumina ba ne, kowa yana da ’yancinsa.”


Jaruma Nafisa wadda ta zama Gwarzuwar Jaruma a lokacin Gasar Kannywood Awards a shekarar 2014 ta ce a yanzu tana shigar Turawa ne saboda tana da ra’ayin hakan, “Kamar yadda a da nake sa atamfa da doguwar riga, yanzu ma na yi ra’ayin sa kayan Turawa ne.”


Da aka tambayi jarumar wadda take shugabancin kamfanin shirya fim na Nafs Entertainment ko me take yi don ganin tauraruwarta ba ta dusashe ba, sai ta ce, “Kun sani ba tun yanzu ba, ba na fadi tashi don ganin tauraruwata ba ta dusashe ba, ina yin abubuwa ne yadda nake so a lokacin da nake so, ba tare da tunanin maganganun mutane ba.”


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






Source: AMINIYA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user