Monday 1 July 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 4

Tura Wannan Zuwa Ga
M. Danye bai san abin da baya ke ciki ba, yana cikin tafiya sai kurum ya ga mutane sun kewaye shi, shi ga zato ce ya ke Maigidansa ne da mutanensa, sai kuma ya fara tuba. Haba, ya gamu da mutanen Sarki, ga shi kuma har ya nuna masu rashin gaskiya, ai kafin haka sun bugo shi daga kan rakumi ya fado, suka daure shi kamar goro, aka kai shi gun Sarki. Da zuwa Sarki bai wata wata ba, sai ya kwace sauran rakumi, ya ce a kai shi kurkuku.


Tauraruwar HamadaMarubuciBukar Mada

+2348021218337Na Sa'idu Ahmed Daura


Ga shi an kwace rakumi da du kud‘insa da ’yan kayansa, ga kurkuku, sai kuma ya zamana, ba a nuna masa komi sai bakar azaba. Kullum da safe bulala dari, da yamma dari. Har dai ta kai yana cewa a zuciyarsa, da na sani da ban d'auko wa kaina wannan wahala ba, ga shi ina murna na kubuta daga hannun Maigidana, amma kubutar ta zaman mani wahala don ko rashin gaskiya kurum amma tun da na dauko alkawali neman yarinyar nan, gara a kashe ni ina cikin kokarina domin girman alkawali.

M. ‘Danye duk ya rame, ba ya komi sai d'oyi, ga rashin abinci isassshe, ga azaba. Bugu da kari sai kuma Sarki ya yi umurni ya rika kwashe kashin kasuwa wai don ya fiddo da kudi.

Da M. 'Danye ya ga abin so a ke a kashe shi ta hanyar wahala, sai ya ce a kai shi gun Sarki yana da magana. Aka kai shi, ya yi gaisuwa ya ce, “Allah ya ba ka nasara, ina so ka taimake ni ka kashe ni, don in huta da azaba". Da Sarki ya ji haka, sai ya ce, “Idan na kashe ka na taimake ka, kuma ka huta da azaba ?" M. 'Danya ya ce, “Ko dai ban huta ba gara Allah ya yi mani azaba, don watakila tashi ta fi taka rangwame, kuma wannan lalle taimako ne, don ko baka kashe ni ba yanzu, azabarka za ta kashe ni gaba, shi ya sa na ga in an kashe ni yanzu an taimake ni". Da Sarki ya ji haka sai ya bushe da dariya ya ce a sake shi. Da aka saki M. 'Danye bai kwana a garin ba, sai ya rarrafa ya bar garin. Kwanansa uku yana tafiya, sai ya isa wani babban birni. Ya sami gidan wata tsohuwa ya sauka ya yi ta jiyya.

Tsohuwar da M. 'Danye ya sauka gidanta irin matsolon tsoffin nan ne, sana'arta sayar da daddawa, amma duk abin da ta samu ba ta ci ba ta sha, sai ta zuba a tukunya, da dare ta shiga bara. Duk halin da ta ke ciki M.'Danye na lura da ita. Da dai ya gane ma'ajiyar tsohuwa sosai, ai kurum da ta fita, sai ya je ya bude tukunya ya kwaso kudi. Da safe in tsohuwa zata tafi kasuwa sai ya kawo kudi ya ba ta ta kwaso nama da kayan girki. Tun da azahar tsohuwa na rawar jiki, sai ta komo ta shiga hidimar girki, ba ta san ashe kud'inta ne ta ke ci ba. Kafin a ce haka tsohuwa ta yi bulbul har ta bar bara. Mutane sai mamaki su ke yi suna ccwa tsohuwar nan ta yi sa'a, ta sami wani bakon falke, sai gara ya ke kashe masu, dubi duk ta canza nan da nan.

Suna cikin haka da M.'Danye duk ya murmure, har ya soma ajiye teba da kudin tsohuwa, sai rannan tsohuwa ta ga safiya ta yi M. 'Danye bai ba da kudin girki ba, ta ce masa, "Maigida yau lafiya, na ga ko kudin girki ba ka ba da ba ?" Sai gogan ya ce, "Ai kudin namu sun kare”. Sai tsohuwa ta sha jinin jikinta. Ta tafi daki ta duba tukunya sai ta ga ko kwabo babu. Sai tsohuwa ta fasa kuka da kururuwa, nan da nan gida ya cika makiI. Aka tambaye ta dalili, ta ce “Kudina bako ya dauke". Mutane da suka ji haka sai suka rika yi mata dariya suna cewa, “Ai gara haka, kin tara kudi, kin ki ci, kin ki sha, kin damu mutane da bara, to ga shi Allah ya kawo maciyinsu".

Ko da gogan ya ga tsohuwa na neman ta maida shi kurkuku, sai ya garzaya gun Sarki. Aka yi masa iso, ya shiga ya yi gaisuwa, ya ce da Sarki, “Kara na ke yi". Aka ce, “Fadi karanka“. Ya ce, “Wata tsohuwa ce mai saida daddawa, na zo ba ni lafiya, na sauka a gidanta, na kawo kudi na bata ta ajiye, na ce ta rika yi mana abinci, to yanzu na sami lafiya na yi shiri zan wuce, to sabo da ban zo na gaida ka ba, mu ko bisa al‘adarmu, mutum kamar ni bai kamata ya zo garin Sarki kamar ka ba bai je ya gaida shi ba. Saboda haka na ce ta kawo fam hamsin don in zo in gaida ka, sai ta fasa kururuwa da kuka, ta ce bata san wannan magana ba".

Ko da fadawa suka ji haka, kafin Sarki ya yi magana, sai suka ce, “Ta aika”. To da shine dalili yanzu ko bara ba ta yi. Da Sarki ya ji maganar fadawa da maganar fam hamsin, sai ya ce a je a kamo ta. Kafin haka an taso keyarta, tana kuka. Da zuwanta, Sarki ya ce, “Ke manufika, kukan me ki ke, ina kudi ?" Tsohuwa ba ta san cikin magana ba, ta ce, “Wallahi duk shi ya debe mini kudin". Sarki ya ce, munafika, ki fiddo su duk inda ki ka sa su". Aka kai tsohuwa kurkuku aka jefa. Sarki ya ce da M. 'Danye, “Je ka na neme ka in ta nuna inda su ke."

Da M.'Danye ya ga ya fita laflya, sai fa ya yi tunanin ya gudu ya bar garin. Sabo da haka zakara ya ba shi sa‘a, ya bar tsohuwa cikin wahala ya san dai ba abin da za’a samu.

Yana cikin tafiya sai ya yi aune da wani katon barawo. Da barawo ya ga M.'Danye, sai ya ce, “Kai mai tafiya, tsaya nan !" M.'Danye ya ce, “Af, abin da mu ke wa wad’ansu, yau mu a ke wa. lalle in kana da rai ba irin canjin da ba za ka gani ba".

Ko da barawo ya ji muryar M. 'Danye, sai ya ce, “Ko Malam ’Danye ne ?" M. 'Danye ya ce, “I, ai ni ne." Ashe wannan barawo yaronsa ne da a ke kira Dabo. Dabo ya ce, “Ai, ni ne Dabo.“ M.'Danye ya ce, “To tun da na same ka ba zan barka ba, sai mu tafi don ka ji abin da ya fito da ni". Ya kwashe labari duk ya gaya masa da irin wahalar da ya sha.

M. 'Danye ya shiga tsubbu.

Da M. ‘Danye da Dabo suka runkuta har suka isa wani kauye mai kuraye. Da suka isa, sai M.’Danye ya ce da Dabo," To wannan sana‘a ta mu, sai mu ajiye ta, don lalle in mun ce, za mu yi ta sai ta hana mu samun biyan bukata, don kada a kama mu a daure, ko da ya ke dai dubarun yin sata suna da yawa, amma dai kai sa mini ido." Dabo ya ce, “To."

A wannan kauye sai M.’Danye ya ce da Dabo, “To zan zama Malami, zan rika yin duba." Abinka da wanda ya iya bakinsa ga shi wajen lalata ko Ja’iru na “Magana Jari ce" ya sanda shi. Kafin a ce haka duk gari ya gama wani babban Malami ya sauka kusa da bayan gari wanda ba abin da bai sani ba. Kafin a ce haka gidan da ya sauka dare da rana cike ya ke da mutane masu son a yi masu duba, da masu neman taimako.

Ran nan da dare, sai wata mace ta zo, ta ce, “Gafarta Malam, mijina ne ya mutu tun shekara bakwai, amma na rasa manemi, ina so ka bani laya ta samin bazawari, in ya samu ko wane iri ne zan baka fam ashirin". M.’Danye ya dauki alkalami da takarda da tawada yana rubutun karya, sai ga wani kure kisim-kisim ya biyo ta kusa da gidansu, yai tsaye ya yi kuka, wuu-wuu. Sai kurum M.'Danye ya ajiye alkalami ya ce, “Ai sai biya, don kin ce ko wane irin bazawari, to wannan kukan da ya yi cewa ya yi, ina bazawarar ga shi.”


Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe 9 na dare, insha Allah.


Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Uku  ba to gashi nan mun kawo Muku..


KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 3


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user