Saturday 29 June 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 3

Tura Wannan Zuwa Ga
Da lokacin tafiya ya kusato, M. 'Danye ya tafi gun wani mashahurin Malami, ana ce masa M. Namuduka, ana yi masa lakabi da “Gobe-da-nisa” ya ba shi labarin ya zo ne don a ba shi taimako za shi Langeri, amma don ya sato Zulkaratu. M. Namuduka ya ce, “I, lalle muna jin labarin wannan yarinya, amma ga yadda mu ke jin yadda ta ke ga ubanta da fasahar ta, wannan al'amari naka mai girma ne, amma zan taimake ka, gobe ka zo mu ga Sarkin Aljannu."


Tauraruwar Hamada




MarubuciBukar Mada

+2348021218337



Na Sa'idu Ahmed Daura


Kashegari M. 'Danye ya dawo. M. Namuduka ya ce, “To ka iya ganin Sarki Aljannu, ba ka ji tsoro ba ?". M . 'Danye ya ce, “Allah ya gafarta Malam, na iya." M. Namuduka ya tashi ya shiga gaba M. 'Danye na biye da shi har bayan gari gindin wani dutse. Da suka isa, sai M. Namuduka ya dauko turare da wadansu hakukuwa ya turara, ya yi wani karatu, sai kurum M. 'Danye ya ga dutse ya bude. Suka shiga cikin dutse, sun kusa fadar Sarkin, sai M. 'Danye ya ga wanin tsohon aljani, fuskar kamar tsumma da gara ta ci, idon ko sai ka ce garwashin wuta, hakoran a kan kasa zube, bakin kaman an yanka kabewa, kan ko kut. Da aljani ya gan su, sai ya kura wa M. ’Danye idanu da kallo, M. 'Danye ko da ya ga shi ya ke duba sai ya yi baya. Mallam Namuduka yana tafiya abinsa bai san abin da ya auku ba, sai da ya juyo haka zai yi wa M. 'Danye gargadi, bai ga M. 'Danye ba, ya koma da sauri ya tarad da M. 'Danye har ya kai bakin kofa, ya ce, “A‘a ha, yaya ka dawo ?” Ya ce, “Wani aljani da za mu wuce, ya harare ni ya ce in komo." M. Namuduka ya dai lallashe shi suka shiga da kyar.


Da suka koma suka isa fada, sai M. 'Danye ya ga wani tsohon Aljani bisa karaga duk jikin gashi ne, yana sanye da rigar fatar zaki, hularshi ta karfe mai siffar kan jaki, ga aljannu sun kewaye shi, tsoro duk ya kama shi. Sa‘an nan Malam Namuduka ya sanad da Sarkin Aljannu abin da ke tafe da su. Da Sarkin Aljannu ya ji, sai ya fiddo wata ’yar laya ya ba shi, ya ce, “Wannan kada ya rabu da ita, ya je lafiya ya dawo lafiya, in ya kiyaye wadannan sharuda, ko ya gamu da mutum kada ya yi masa magana, kada kuma ya shiga ko wane gari, in ba garin da ya yi niyya ba". M. Namuduka ya ba M. 'Danye laya, M. 'Danye ya sa hannu biyu ya amsa ya yi godiya, suka fito. Bayan sun fito M. Namuduka ya sallame shi ya yi masa addu‘a, suka rabu, M. 'Danye yana cewa, ko kuma ba a sonsa da yin sa'ar ne.


Bayan sun fito, sai Sarkin Aljannu ya ce, “Ya kamata mu aika a dauko yarinyar nan, mu gan ta, mu ga kuma irin abin da ya sa, har a ke son sato ta." Da dare ya raba, Sarkin Aljannu ya sa aka je Langeri, kafin kiftawa da bissimillah aka kawo Zulkaratu ya dube ta da kyau, ya ce, “l, lalle gaskiya ne, ba mutum ba ko aljani ya yi kyawun wannan yarinya, Ialle ya isa mai kyau, to ba don. M. Namuduka yana cikin wannan magana ba da ba mu maida ta ba, amma sabo da shi mu, mun yi hakuri, tun da sun riga sun zo har gare mu". Ya sa aka mayar da ita nan da nan. Amma ita ba ta san abin da aka yi ba ma, balle halin da a ke ciki kuma.


Da lokacin da M. 'Danye ya dauka gun Sarki ya cika, sai ya yi shiri, ya kama hanya tun da asuba ta cikon wata daya da ya dauka gun Sarki, ya kama hanya mai zuwa Langeri ya yi ta yi. To abinka da hanyoyin sahara, wani wurin hanya sai ta bace, rairayi ya rufe ta, ya yini yana tafiya har magari ta yi. Da magariba ya tsaya a wani fili wanda aka share shi babu rairayi sosai, ya ci abinci ya yi sallah, sai ya kishingida don ya hutu, ai sai barci ya share shi don gajiyar tafiya, ko da ya ke sabon shi ce. M. 'Danye bai farka ba har rana ta fito. Can wajen hantsin gwauro sai wadansu, ‘yan hari bisa rakuma, suka zo suka tarad da shi yana barci. Babbansu ya durkusad da rakuminsa ya sauka, ya ɗauke duk kayan M. 'Danye har da 'yar laya da Sarkin Aljannu ya ba shi, sannan ya ta da shi. M. ‘Danye ya tashi firgigi a tsorace, ya wawuri kaya babu, ba wani makami, sai ya yi tuma, suka tisa shi gaba har kauyensu


Da fa M. ’Danye ya ga ya zo hannu ya ga ya zama bawa, sai ya fara tunanin yadda zai ya fita daga wannan hali. Can dabara ta zo masa, ya ga lalle abin da ya fi karfinka, sai lallashi, ya ga kuma don ya lallashi ubangidansa kan ya bar shi ya tafi, wannan ba ta yi wo, sabo da haka sai ya shiga fadanci yadda za a yarda da shi har ya samu ya gudu. Sabo da haka kullum in suna fira da ubangidansa, sai ya rika cewa, “Ni dai Allah ya ba ni sa’ar fitowa da ka kamo ni, da ma ba ka kamo ni ba, da na biyo ka, ga shi ni ba ni wata wahala, in ci abinci irin wanda na ke so, wallahi har ba ni son in ko fita yawo, haka duk al’adarku ta ke, ku jiya wa bayinku dadi? Ubangida ya ji an yaba shi, sai ya ce, “Ai duk garin nan ba mai yi wa bawa, yadda na ke wa nawa, nan gaba ma in idonka ya fara budewa da mutane zan fara tura ka kasuwoyi kana sayar mani da alkama da shinkafa, don lalle in nuna ma na yarda da kai. Da M. 'Danye ya ji an masa susa inda ke masa kaikayi ya ga kuma har zai sami guzuri, sai ya ce, “Haba Maigida ai wannan wahala ce, ni dai ba ni so gara kullum ina tare da kai, ko da ya ke dai in ka sani zan yi don faranta ma rai, kuma ka kara ganin gaskiya ta, ya kaikaici idonsa ya yi masa gwalo.


Jin haka sai ya sa Ubangidansa ya himmantu da ya tura shi kasuwoyi, sabo da haka ya labta wa rakuma biyu kayan alkama da na shinkafa ya kira M. ‘Danye ya gama shi da fatake.


M. 'Danye suka mika tare da fatake. Suna tafiya sai tambayarsu hanyoyi ya ke, har ya dace ya ga hanya mai zuwa Langeri.


Da magariba ta yi suka sauka inda za su kwana, suka ci abinci, suka yi yar fira, sabo da gajiyar tafiyar nan da nan suka yi barci, amma M. 'Danye idonsa biyu, ya yi kamar ya yi barci. Can da dare sai ya tashi ya yi Iabtu, ya hau rakumi guda ya bi haya, ya dire hanyar Langeri ya yi ta yi.


Da asuba suka tashi, suka dubu, ba M. 'Danye, suka yi tsammani ko har ya yi gaba. Sabo da haka suka ci gaba wai ko sun tarad da shi, ina, har suka isa kasuwa babu M. 'Danye.


M. 'Danye da isa wani dan kauye sai ya sayar da alkama da shinkafa da rakumi guda, ya sami isashen guzuri ya ci gaba da tafiyarsa.


M. 'Danye yana cikin tafiya sai ya ji wani ya ce, “Ta nan ya bi”. Sai ya zaci ko Ubangidansa ne ya biyo shi, sai ya ce, "Wallahi hanya ta bace mani har suka barni“. Da mutanen nan suka ji haka sai suka ce, “Ai ba mu yarda ba, sai mun tafi da kai gun Sarki, don sun tabbata ba shi da gaskiya". Da ya ya ga da gaske su ke, sai ya ba su duk kudin alkama da kudin rakumin, don yana tsoron kada su tafi da shi, har ubangidansa ya tarad da shi, sa‘annan suka bar shi. Yana tafe yana cewa su dai kayan zalunci ba su da albarka. Ashe su mutanen nan jakinsu ne ya bace, su ke cewa, ta nan ya bi, shi kuma M. 'Danye yana zaton da shi su ke, ganin ko alamar rashin gaskiyarsa shi ya sa suka turza, su da suka sami wannan kudi sun yi ta jaki, ai sai gida.


Mutanen nan da suka shiga garinsu, sai suka nufi fada don neman fadanci, suka kwashe labarin M. 'Danye suka ba Sarkin garinsu kan lalle wani gawurtaccen barawo ne, akwai kudi masu yawa gun shi, don mu ma har ya ba mu. Sarki da ya ji haka, mai nema a duhu ya samu a sarari, sai ya tura dogarai kan dawaki, suka bi M. 'Danye. M. Danye bai san abin da baya ke ciki ba, yana cikin tafiya sai kurum ya ga mutane sun kewaye shi, shi ga zato ce ya ke Maigidansa ne da mutanensa, sai kuma ya fara tuba. Haba, ya gamu da mutanen Sarki, ga shi kuma har ya nuna masu rashin gaskiya, ai kafin haka sun bugo shi daga kan rakumi ya fado, suka daure shi kamar goro, aka kai shi gun Sarki. Da zuwa Sarki bai wata wata ba, sai ya kwace sauran rakumi, ya ce a kai shi kurkuku.



Za mu ci gaba ranar Litinin mai zuwa, da karfe tara na dare, insha Allah.


Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Biyu  ba to gashi nan mun kawo Muku..


KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 2




Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user