Saturday 22 June 2019

KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 2: LABARIN YA DAUKI HANKULAN DUNIYA SOSAI

Tura Wannan Zuwa Ga
Kafin a ce haka sai gun biki ya cika da sarakin gari da mahukunta. Da zuwansu ba wanda ya dube su ma, kowa yana ta kansa, ganin haka fa sai Liman ya ce; “Ai ba tsayawa za mu yi ba, gara mu shiga mu ga abin da za mu samu.” Kafin a ce haka sai ga Sarki da Liman da sauran manyan gari suna kokawa da yara, an ture masu rawani can rigunan an yi kaca-kaca da su.Tauraruwar Hamada MarubuciBukar Mada

+2348021218337Na Sa'idu Ahmed Daura


Nakowa ya ji labarin zuwan manyan gari, sai ya fito a guje, ya duba bai gan su ba, duk sun saje da yara da sauran talakawa. Zuwa can ya ga Liman duk sajensa ya yi kura, bai ma sami wani abin kirki ba, ya fadi ya ce, “Allah ya gafarta Malam, lafiya haka ?” Liman ya ce, “Ai mun zo har da Sarki ne don neman albarka”. Nakowa ya ce, “To wannan ai wani abokina ne, ya zo taya ni biki, shi ne mai zubo kudi daga sama". Sai ku tafi gida in ba ku naku”. Nakowa ya aika masu nasu bayan sun je gida. Manyan gari duk kunya ta rufe su kan wannan abu. 


Da Zulkaratu ta fara wayo sai Nakowa ya sa ta makaranta ta zama ko yarinya ce mai kokari, kafin a ce haka har ta sauke. Aka sa ta kuma karatun littattafai wanda za ta gane sha‘anin addini, cikin lokaci kadan duk ta iya su. Zulkaratu ba ta cika shekara goma ba sai da ya zama ta san abubuwa wadanda duk sa'arta ba ta sani ba game da ilmi, kai har ma manyan. 


Da yarinya ta soma girma sai masoya suka yo ca, abin babu kama hannun yaro. Ya zamana daga Sarki sai dan sarki, don attajirai abin ya fi karfinsu, ko da ya ke masu karanbani sun shiga, ka san wannan wuri su talaka rabonsu hange, don ba a anbata su ba. 


To cikin manemanta akwai dan Sarkin garinsu, watau Langeri, ana ce da shi Yarima, yana son ta gaya, ko da ya ke ita ma ta fi sonsa da duk sauran manemanta. Yarima ya tabbatar shi zai aure ta. 


Sabo da haka sai ya tambayi ubansa Sarkin Langeri, wata gona tashi, yamma da gari, ya amshi kudi masu yawa, ya shiga gina gidan da za su zauna. Kafin a ce haka, ya gina gidan da ba a taba ganin irinsa ba duk arewa. Aka kawo kilisai da kujeru na zinari da azurfa aka zuba, abin sai wanda ya gani. Koyaushe a nan su ke hira da Zulkaratu. 


Akwai wani gawurtaccen Sarki gabas da Langeri a wani gari da ake kira Damas, wanda ya sami labarin Zulkaratu daga wani falke. Ya sa aka kira falken nan gidansa, Sarkin nan ya tambaye shi labarin Zulkaratu. Falke ya sanad da shi cewa ya tabbata duk duniyan nan babu matar da ta yi ya Zulkaratu a kyau, ga ta da fasaha da ilmi. Da Sarki ya ji haka sai ya fara shawarar yadda zai yi ya sami Zulkaratu.


Kashegari sai Sarkin Damas ya yi shirin kayan duniya masu yawa, ya kira Falken nan ya gama shi da wani babban bafadensa ya tura su Langeri, gun Nakowa su nema masa auren Zulkaratu. Falke da Bafade suka yi shiri, suka nemi sa’ar hanya suka tafi. A kwana a tashi har Allah ya kai su Langeri, suka je suka sauka, aka sauke kaya daga kan rakuma da aka labtawa. 


Bayan sun huta, suka tafi don su gana da Nakowa, kuma su ba shi labarin abin da ke tafe da su. Aka yi masu sallama, Nakowa ya fito, bayan sun gama gaisuwa, suka ba shi labarin abin da ke tafe da su, da kuma irin baiwar da Sarki ya aiko su da ita. Nakowa bai nemi ko ya ga abin da suka kawo ba, sai ya ce, " Na ji, na kuma gode, amma batun aure, ba ni iya ba da wannan yarinya nisan duniya har Damas don ba ni da kowa sai ita." Ya kawo kyauta mai yawan gaske ya ba su, ya ce, "Ku gaida mani Sarki, bakin irin jawabina ke nan, amma ina masa godiya tun da ya ke kaunar diyata, ni kuma ina kaunarsa kuma tsakanina da shi sai amana da alheri. Nisan garin shi ne kurum ya sa ba zan ba shi ba." Suka yi godiya suka fita. Da safiya ta yi suka yi shiri, suna masu bakin cikin bukatar Sarki ba ta biya ba, suka kama hanya zuwa Damas.


Ran nan da magariba duka isa Damas, ba su doshi ko ina ba sai gidan Sarki. Da Sarki ya ji su ne suka dawo, sai ya fito. Suka kwashe labarin yadda duk suka yi da Nakowa suka fada masa da jawabin da kyautar da Nakowa ya yi masu. Suka kuma ba shi labarin sun ji a cikin gari, wannan yarinya fa ba ta son kowa sai dan Sarkin garinsu, watau Yarima. 


Hankalin Sarki fa duk ya tashi, ya sa aka tara hakiman kasarsa duka da manyan fadawansa. Da aka taru Sarki ya ba su labarin Zulkaratu da kuma aiken da ya yi da jawabin da aka yiwo masa, ya tambaye su yaya za a yi, don shi lalle ya sami wannan yarinya ko ta wane hali. Sai wani daga cikin hakimai ya ce “Allah ya ba Sarki nasara, ai kurum sai mu tafi, mu ciwo garin a kama yarinya". Sai Wazirin garin ya ce, “A'a, tun da ga irin jawabin da ubanta ya yi, ga kuma kyauta da ya yi wa sarkimmu, to bai kyautu mu fada garin ba da yaki, sai dai mu yaudare su, mu sa a sato yarinyar allabashi in sun ce za a karbe ta, kuma nan sai a yi duk yadda za a yi.” Sarki ya ce da Waziri, “Ta kaka za a sato ta ?" Waziri ya ce, “Ai wannan ba wuya, zan zo mu shirya da almuru". Sarki ya yarda da shawarar Waziri, aka watse. 


Da magariba ta yi waziri ya tafi gidan sarki. Ya sami Jakadiya, ya sa ta yi masa sallama da Sarki. Sarki ya fito, Waziri ya fadi ya yi gaisuwa, sa'an nan ya ce, “Allah ya ba ka nasara, bisa maganar yarinya da ka sami labarinta, akwai wani shahararren barawo ana ce masa M. 'Danye, ba ni shakka idan har mun shirya da shi zai sato ta ya kawo ta nan". Sarki ya ce, “To ya ya za mu yi mu shirya haka, har mu sami wannan barawo ?" Waziri ya ce, “In har dai ka yarda in shirya yadda za zo da shi, ba za a cika wata ba duk inda ya ke mu same shi." Sarki ya yarda. 


Da Waziri ya koma gida ya kira wani amintaccen yaronsa, ya sa shi ya nemo masa M. 'Danye, amma kada su shigo gari sai magariba ko sun zo da wuri. 


Bayan mako biyu, yaro ya zo tare da M. ’Danye, ya shiga ya ba Waziri labari sun zo da shi. Da Waziri ya fito bai ko tsaya ba, sai ya kira M. 'Danye suka dunguma sai gidan Sarki. 


Aka yiwo sallama da Sarki, ya fito. Waziri ya yi gaisuwa, sa‘annan ya sanad da shi sun zo tare da M. 'Danye. Sarki ya ce, “Ya shigo" 


M. 'Danye ya shigo ya yi gaisuwa, Sarki ya amsa da murna da ban girma, sai ka ce wani hakimi. Sa'annan Sarki ya kwashe labarin Zulkaratu ya ba M. 'Danye, kuma ya fada masa abin da ya ke bukata ya yi masa kanta. M. 'Danye ya ce, “Ai don wannan ba komi ba ne, sai dai ina son dan lokaci don shiri." Sarki ya kawo kudi da tufafi masu yawa ya ba shi, ya kuma masa alkawari in har bukatarsa ta biya zai ba shi abin da zai ci har ya mutu. M. 'Danye ya roki Sarki ya ba shi wata daya don ya yi shiri, Sarki ya yarda. 


Waziri ya fito M. 'Danye na biye da shi har gidan Waziri, da suka isa sai Waziri ya ce da M. 'Danye, To ta inda aka hau ta nan a ke sauka, kada ka dawo da yarinya ka nufi gidan Sarki, nan gidana za ka kawo ta, don ni zan tafi da ita, sa'an nan in kai ka ka yi gaisuwa, Sarki ya sallame ka, kuma ni ma in sallame ka". Ashe Waziri abin da ya sa ya ke son a kawo ta, ya riga Sarki samun labarinta, shi ma yana sonta gaya, wannan ma shi ne dalilin da ya sa ya ki a karbo ta da yaki. Ya kawo ’yar kyauta ya yi wa M. 'Danye don karin guzuri, ya gargade shi kada ya fada wa kowa. kuma in ya zo kada ya shigo gari sai dare ya raba. Nufin Waziri, idan M. 'Danye ya zo da ita da dare ya kashe shi, ya amshi yarinyar. M. ’Danye ya yi sallama ya fita. 


Da lokacin tafiya ya kusato, M. 'Danye ya tafi gun wani mashahurin Malami, ana ce masa M. Namuduka, ana yi masa lakabi da “Gobe-da-nisa” ya ba shi labarin ya zo ne don a ba shi taimako za shi Langeri, amma don ya sato Zulkaratu. M. Namuduka ya ce, “I, lalle muna jin labarin wannan yarinya, amma ga yadda mu ke jin yadda ta ke ga ubanta da fasahar ta, wannan al'amari naka mai girma ne, amma zan taimake ka, gobe ka zo mu ga Sarkin Aljannu." 


Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, da karfe tara na dare, insha Allah.


Ga waɗanda Basu samu damar Karanta kashi na Farko (Na Daya)  ba to gashi nan mun kawo Muku..KARANTA LABARIN TAURARUWAR HAMADA KASHI NA 1
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user