Friday 21 June 2019

KARANTA LAIFIN DA SHUGABAN KASAR MISRAH MUHAMMAD MURSI YA AIKATA A IDON DUNIYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Har na kwanta nace bari dai in dan duba me duniya ke ciki. Garin laluban labari na lalubu bakin labari. Baccin ma yaki zuwa.


Muhammad Mursi




Marubuci: Mustapha Bello Muhammad



Bayan ya lashe zaben shugaban kasar Masar da gagarumin rinjayi a shekarar 2012, sai kasashen yamma, Amurka da kawayenta tare da hadin gwiwar Saudi Arabia suka  marawa sojojin kasar masar din baya domin su hambarar da gwamnatin shi. Aka ka mashi aka daure, karshe akace a yanke mishi hukuncin kisa akan lefin da bai aikata ba.


Laifinsa guda daya ne, yana da kishin addinin shi, kuma ya nuna kyama karara ga makubciyar kasar shi, watau kasar isra'ila.


shine shugaban kasa na farko da aka taba yi a duniya a wannan karnin wanda yake mahaddacin Qur'ani. A yau LItinin Allah yayi mishi cikawa yayin zaman kotu.


Yanzu haka kafafen yada labarai na turawa dama 'yan koran su na nan gida Najeriya sun dukufa wajen bata mishi suna. Domin kada ya burge 'yan baya a sami irin shi nan gaba.



Abin lura.



1. Kasashen da suka kashe miliyoin mutane a Iraqi, da Libya, da sauran wasu kasashe domin su tabbatar musu da domukuradiyya, sune dai suka kashe miliyoyin mutane a kasar Masar domin su hambarar da mulkin demukuradiyya su kawo mulkin soji. Har yanzu sojan da suke goyawa baya shine ke mulki, basa yi mishi maganar demokuradiyya tunda yanayi musu biyayya sau-da-kafa.



2. Duk da cewa, Marigayi Muhammad Mursi, cikakken dan sunni ne, wanda yayi mubaya'a ga kasar Saudi-Amerca, hakan bata hana Saudi-Amercan shigewa gaba wajen hambarar dashi ba domin tafarantawa uwargijiyar ta Amurka. Ke nan takun sakar dake tsakanin Sunni da ke da cibiya a Saudi-America, da shi'a dake da cibiya a Iran siyasar duniya ce kawai ake fakewa da sunna ko shi'a don cimmata.


3. Abin mamaki, lokacin da yaci zabe, yaje kasar Saudia kusan sau 3 yana neman taimakon kudi, shi a tinanin shi ai duk daya ne, amma suka hana shi. Soja na hawa saudiya ta bashi dalla biliyan daya a ranar 20 ga wata July 2013, kamar yadda 'yan gwagwarmayar Saudiya suka bayyana.


4. Ina tabbatar muku, mahukunta Saudi-America zasu iya amincewa a salwantar da rayukan duka mabiyansu na Najeriya don yiwa Amurka biyayya idan ta kama.


5. Da fatan Allah yaji kanshi ya gafarta mishi, da duka matattunmu baki daya. Muma idan tamu ta zo yasa mu cika da Imani.


Muna fatan Allah yaji kanshi da rahama, ya gafarta mishi Amin.



MUKALOLI MASU ALAKA:

DAN KISHIN ADDININ ISLAMA YA KWANTA DAMA MUHAMMAD MURSI


KARANTA ABUBUWAN MAMAKI 15 GAME DA MUTUWAR MUHAMMAD MURSI


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user