Showing posts with label Labarin Wasanni. Show all posts
Showing posts with label Labarin Wasanni. Show all posts

Wednesday, 17 July 2019

NAFI KOWA FARIN CIKIN KORAR SUPER EAGLE  A WASAN  AFCON 2019 - DATTI ASSALAFY

NAFI KOWA FARIN CIKIN KORAR SUPER EAGLE A WASAN AFCON 2019 - DATTI ASSALAFY

Naji dadi da aka koro kungiyar kwallon kafa ta kabilar Igbo ko inyamurai (Super Eagle) daga gasar cin kofin nahiyar afirka.


Super Eagle


Har ga Allah ban so su kawo zuwa wannan lokaci na Quarter final ba, ana diban makudan kudin 'yan Nigeria ana kashewa  'ya'yan Inyamurai akan wata shirme kwallo, wanda hakan babu abinda zai amfanawa Nigeria da 'yan Nigeria sai asara.

Masoya kwallon kafa ina tayaku murna sosai da aka koro kungiyar kwallon kafa ta inyamurai, abin mamaki mutanen da kake gani Ahlussunnah ne na gaske suma an shagaltar dasu wasan kallon kafa har ssunabayyana bacin ransu.


Ra'ayin Datti Assalafy


AN ZARGENI RASHIN KISHIN NIGERIA

Maganar da nayi jiya akan kwallon kafa, wasu sun zarge ni da cewa wai bana kishin Nigeria, har da kiran waya daga wajen abokan zumunci.

Hakika inda akwai wani alfano da talakan Nigeria, musamman 'yan uwana Musulmai suke samu a dalilin kwallon kafa tabbas da zanyi kishinta, kuma da zanyi fatan Nigeria taci nasara a kowani mataki.

Amma sai naga babu abinda harkan kwallo yake karawa a Nigeria face talauci da asara, turawa sun mana wayo suna samun makudan kudi akan harkan kwallo, wanda yau inda zaka shiga wani kauye mai nisan gaske zaka iya samun gidan kallon kwallo suna zuba kudi, kudin na tafiya asusun ajiyar kudaden yahudu da nasara.

Sai kaga mutum a kauyen kayau ya haddace sunayen 'yan kwallo, idan ka titsiye shi kyakkywan karatun Fatiha bai iya ba, a majalisun matasa sun dena tattaunawa akan abinda zai amfane su, ya kuma amfani al'ummar su, sai dai jayayya akan kwallo kawai.

Kallon kwallo ya haddasa gaba da kiyayya a tsakanin matasa, ya shagaltar da matasa akan mayar da hankali ga abinda zai amfane su, yana hana 'yan uwa musulmai Sallah akan lokaci cikin jam'i, har kisa anayi a kan kwallo, yara kanana suna zuwa gidajen kallon kwallo su hadu da miyagun mutane suna koya musu munanan dabi'u da laifuka da ta'addanci da iskanci.

Yanzu turawa sun jefa wadannan 'yan uwa matasa da suka shagala da harkan kallon kwallon kafa cikin mummunan laifi na sana'ar caca (9ja bet), wanda karshen 'dan caca rikakken barawo yake komawa, caca na hana mai yinta tabuka komai a rayuwa, abinda turawa suka koyawa matasan mu kenan.

Akwai lokacin da majalisar dattijai a Nigeria tayi yunkurin hana cacar 9ja bet amma ba su kai ga nasara ba, alherin Allah Ya kai ga tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, domin shine gwamna na farko da na sani ya haramta cacar kwallo ta 9ja bet, ya musu koran kaji daga jihar Borno.

Don nayi adawa da harkan kwallo bai kamata  ace bani da kishin Nigeria ba, dangantani da rashin kishin Nigeria akan don nayi adawa da kwallo cin mutunci ne da kuma batanci da rainin hankali gareni wanda ba zan lamunta ba, rayuwata na Sadaukar akan kishin Nigeria da kuma zaman lafiyar Nigeria.

Yana daga cikin hanyoyin da yahudu da nasara sukace zasu yi amfani dashi wajen halakar da al'umma shine wasanni.

Ina rokon Allah Ya kara nakasa tasirin kwallon kafa a Kasarmu Nigeria.

Yaa Allah Ka cirewa 'yan uwa musulmi sha'awar kallon wasan kwallon kafa a cikin zukatansu Amin.

Allah Ya taimake
mu akan gaskiya.


MU KALOLI MASU ALAKA:

KARANTA ZAFAFAN SHAWARWARI 10 ZUWA GA SHUGABAN KASAR NIGERIA MUHAMMADU BUHARI

KARANTA LAIFIN DA SHUGABAN KASAR MISRAH MUHAMMAD MURSI YA AIKATA A IDON DUNIYA

KALLI YADDA SA'IN SA YA JAWO WATA TA CAKA MA WANTA WUKA YA MUTU HAR LAHIRA


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






Source: Datti Assalafy

Thursday, 27 December 2018

Karanta Kaji: Ko Ka San ’Yan Wasan Da Babu Kamarsu A Gasar Firimiyar Ingila?

Karanta Kaji: Ko Ka San ’Yan Wasan Da Babu Kamarsu A Gasar Firimiyar Ingila?

Hukumar dake kula da buga gasar cin kofin ajin firimiya ta kasar Ingila ta fitar da sunayen zakakuran ‘yan wasa guda 10 a gasar ta firimiya da babu kamarsu a gasar da ake fafatawa a wannan kakar.



Ta fitar da jerin sunayen ‘yan wasanne duba da auna irin kokari da gudun mawa da kowanne ya yi wa kungiyar sa kawo yanzu da akayi rabi a gasar bayan kowacce kungiya ta buga wasanni 18. Saidai kungiyoyin kwallon kafa guda 2 sune sukafi mamaya wato kungiyar Liverpool da takwarrata ta Manchester City don ko wacce kungiya akwai ‘yan wasan ta guda 3 acikin guda 10 da aka fitar.

Ga jerin sunayen ‘yan wasan daga mai jan ragamar na 1 kenan har zuwa na 10:

Mohammed Salah (Liverpool). Eden Hazard (Chelsea). Raheem Starling (Manchester City). Harry Kane (Tottenham). Virgil Van Dink (Liverpool). Ederson (Manchester City). Sergio Aguero (Manchester City). James Milner (Liverpool). Pieree-Emerick Aubameyang (Arsenal). Wilfried Zaha (Crystal Palace).

Har ila yau, idan an kammala buga gasar, hukumar ta FA zata sake fitar da sunayen ‘yan wasanda babu kamarsu a gaba daya gasar da aka buga kuma yawanci kungiyar data lashe gasar ‘yan wasanta suna fin yawa.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: LEADERSHIP A YAU

Tuesday, 25 September 2018

Karanta Kaji Yadda akai ya zama Gwarzon duniya: Modric ya kawo karshen Ronaldo da Messi

Karanta Kaji Yadda akai ya zama Gwarzon duniya: Modric ya kawo karshen Ronaldo da Messi

Dan wasan Real Madrid Luca Modrci ya lashe kyautar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya da take bai wa gwarzon dan kwallon duniya na shekara a wani biki da ya gudana a birnin London, abin da ya kawo karshen kane-kanen da Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka yi wajen lashe kyautar a tsakaninsu cikin tsawon shekaru.


Modric ya doke Ronaldo na Juventus da Mohamed Salah na Liverpool wajen lashe wannan gagarumar kyautar a bana.

Dan wasan mai shekaru 33 ya lashe kofin zakarun nahiyar Turai karo na uku a jere a kungiyarsa ta Real Madrid, sannan ya jagoranci kasarsa ta Croatia har zuwa matakin wasan karshe a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Rasha.

Ronaldo bai samu damar halartar bikin karramawar ba, yayin da har ila yau Mohamed Salah ya doke shi wajen lashe kyautar Puskas da ake bai wa dan wasan da ya jefa kwallo mafi kyawun ciyuwa a raga.

Ko da dai wasu na ci gaba da jinjina wa Ronaldo kan kwallon da ya jefa ragar Juventus a bara a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, wadda ta kai ga magoya bayan Juventus a Turin mikewa tsaye don girmama shi.

Wani abu da ke ci gaba da dagula tunanin magoya bayan Salah shi ne yadda aka cire sunansa daga cikin jerin ‘yan wasan FIFA 11 da suka fi iya taka leda duk da cewa yana cikin ‘ya wasa 3 ta suka yi takarar lashe kyautar gwarzon dan wasan bana.

JERIN 'YAN WASAN FIFA 11 NA BANA

David de Gea ( Manchester United )

Dani Alves (Paris Saint-Germain)

Raphael Varane ( Real Madrid )

Sergio Ramos (Real Madrid)

Marcelo (Real Madrid)

Luka Modric (Real Madrid)

N'Golo Kante ( Chelsea )

Eden Hazard (Chelsea)

Lionel Messi ( Barcelona )

Kylian Mbappe (Paris Saint-Germain)

Cristiano Ronaldo ( Juventus )

A bangaren guda an zabi Kocin tawagar Faransa, Didier Deschamp a matsayin gwarzon mai horarwa na shekara, yayin da 'yar wasan Brazil da ke taka leda a Orlando Pride, watO Marta ta lashe kyautar ta FIFA a bangaren mata.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: RFI HAUSA

Wednesday, 1 August 2018

Karanta Dalilin da yasa aka yankewa Cristiano Ronaldo Hukuncin Ɗaurin Shekara 2

Karanta Dalilin da yasa aka yankewa Cristiano Ronaldo Hukuncin Ɗaurin Shekara 2

Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7, bayan daurin shekaru biyu da kotu ta yi masa. 


Sai dai kuma ba zai zauna gidan kurkuku ba

Wannan ya zo karshen kiki-kakar da ake da shi a kotu na tsawon lokaci inda mahukuntan kasar Spain suka zarge shi da kin biyan haraji a lokacin da ya ke wasa a Real Madrid.

Ronaldo dai ya musanta zargin da ake masa. An yanke masa wannan hukunci ne ranar Juma’a.

An zargi Ronaldo da kin biyan haraji har na Yuro milyan 5.7

Ronaldo mai shekara 3 a duniya, ba zai je gidan kurkuku ba, saboda dokar kasar Spain ta ce ko da an yanke wa mai laifi irin wannan hukuncin dauri, matsawar a karon farko ne, to ba zai je gidan yari ba, sai dai ya biya tarar kawai.

Amma kuma maimakon dauri, zai rika biyan wani sabon haraji na Yuro 250 a kowace rana har tsawon shekaru biyun da aka yanke masa, a madadin zaman gidan kurkuku.

Bayan wanna, Ronaldo zai biya tarar dala miliyan 3.7 da kuwa zunzurutun Yuro milyan 5.7 wadanda tun da farko ya ki biya a matsayin tarar da ta sa aka maka shi kotu.

Akwai kuwa tarar wata Yuro milyan daya da zai biya, a matsayin kudin ruwan da suka taru a hannun sa, a tsawon lokacin da ya ki biyan harajin.

Gaba daya dai Ronaldo zai biya tarar Yuro miliyan 19, wadanda idan aka auna su a sikelin naira, bilyoyin nairori ne masu yawa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source: Premium Times Hausa

Tuesday, 24 July 2018

Karanta Cikakken Tarihin Mesut Ozil: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Dan Wasan Kwallon Kafa Mesut Ozil - Hotuna da Cikakken Tarihi

Karanta Cikakken Tarihin Mesut Ozil: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Dan Wasan Kwallon Kafa Mesut Ozil - Hotuna da Cikakken Tarihi

Ko Dan Ni Musulmi Ne Ake Kalubalanta Ta A Kungiyar Kwallon Kafa Ta Jamus?, Cewar Ozil


Mesut Ozil ya bayyana hakan ne bayan ya ajiye bugawa kasar Jamus wasa bisa kalubalantar sa da hukumar kwallon kafa ta kungiya da wasu magoya bayan kungiyar kasar suke yi don ya gana da shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan.

TARIHIN RAYUWAR MESUT OZIL A TAKAICE

An haifi dan kwallon ne wanda ya fito daga tsatson Turkawan da suka yi kaura zuwa Jamus a garin Gelsenkirchen, kuma yana cikin tawagar kasar da ta lashe gasar kofin duniya a 2014.

Ya buga wa kasar wasa sau 92 sannan sau biyar magoya baya na zabarsa gwarzon dan kwallon kasar tun daga shekarar 2011.
Sai dai tawagar kasar ta kasa kai wa zagaye na biyu a gasar kofin duniya ta Rasha, duk da cewa suna daya daga cikin wadanda aka yi hasashen za su lashe kofin.

Asalin sabanin

Ozil da Ilkay Gundogan na Manchester City dukkaninsu jamusawa kuma 'yan asalin Turkiyya sun sha suka daga hukumar kwallon kafa ta Jamus bayan ganawarsu da Recep Tayyip Erdogan a watan Mayu.

A cikin wata sanarwa, Ozil ya ce, "ziyarar ba ta shafi siyasa ba ko wani zabe."

"Ina da zuciya biyu, daya a Jamus daya kuma a Turkiyya", kamar yadda Ozil ya wallafa a Twitter.

"Wannan ni ya shafa na wakiltar ofishi mafi girma a kasar iyaye na."


Ozil, wanda mahaifiyarsa 'yar kasar Turkiya ce, ya kara da cewa "a lokacin da muka ci kofin duniya a 2014, sun dauke ni tamkar dan Jamus amma saboda wannan karon ba mu yi nasara ba, sai suka soma nuna min wariya. Ga abokan wasana irin su Close da Podiski su ma ruwa biyu ne amma ba a kalubalantarsu".


"Ni dan kasar Jamus ne a wurinsu a lokacin da muka yi nasara, amma ni dan ci-rani ne idan muka sha kashi," a cewar Ozil.

Ozil ya ce lokacin da yana karami, mahaifiyarsa ta horar da shi a kullum ya kasance mai girmamawa kuma kada ya taba manta asalinsa.

Daga baya kuma Ozil ya sake wallafa wani sako yana mai kalubalantar kafofin watsa labaran Jamus da suka dauki laifin rashin nasarar da kasar ta yi a gasar cin kofin duniya suka dora a kan hotunansa da shugaban Turkiya.


Ya ce "ba su soki rawar da na taka ba da kuma tawagarmu ba amma sun soki asali na da kuma yadda nake girmama shi.
"Wannan ya keta iyakar da bai kamata a keta ba, inda jaridu suka nemi dora alhakin kasar Jamus a kai na."


Bayan dan wasan ya gana da Erdogan a wani taro a Landan, inda Ozil ya ce sun tattauna game da kwallon kafa, sai jam'iyyar AK mai mulki a Turkiyya ta wallafa hotuna ana dab da zaben da Erodogan ya lashe.

'Yan siyasar Jamus da dama sun soki Ozil da Gundugan, suna masu bayyana shakku kan amincinsu ga mutunta tsarin dimokuradiyar Jamus.


Jamus ta soki shugaba Erdogan kan yadda yake murkushe abokan hamayyar siyasa bayan murkushe wani yunkuri na yi ma sa juyin mulki.

Ozil ya ce ba ruwansa da wanda ke shugaban kasa, ko dan Turkiyya ne ko Jamus, tunaninsa ba zai sauya ba.

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil ya yi ritaya daga buga wa Jamus kwallon kafa yana mai cewa an nuna masa banbancin launin fata tare da cin zarafinsa saboda ya dauki hoto da shugaban kasar Turkiyya.



Nan bada dadewa ba cikakken Tarihin sa yana zuwa gare ku , kawai bayan 24 hours Ku sake bude wannan Post domin Karanta Cikakken Tarihin Saboda a halin yanzu Muna kokarin tattara Tarihin waje daya

Dubban Magoya bayan shi a shafin Twitter sun kalubanci lamarin.

Tarihin Ahmed Musa: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Dan Wasan Kwallon Kafa Ahmed Musa - Hotuna da Cikakken Tarihi

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng