Saturday 15 June 2019

KARANTA ZAFAFAN SHAWARWARI 10 ZUWA GA SHUGABAN KASAR NIGERIA MUHAMMADU BUHARI

Tura Wannan Zuwa Ga
Da farko ina kara taya ka murnar lashe zaben da kayi a karo na biyu, da kuma murnar sake daukar rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a karo na biyu.


Shugaba Muhammadu Buhari




Marubuci: Hassan Auwal Muhammad


Baba! a matsayina na daya daga cikin wanda ake ta gwagwarmaya dani tin daga shekara ta 2003 lokacin da ka fara siyasa, har zuwa lokacin da Allah ya baka nasarar zama shugaban Nigeria a shekarar 2015, kuma ka sake samun nasara a zaben da akai cikin wannan shekara ta 2019, lallai an fuskanci kalubalai da dama a zangonggg mulkin ka na farko wanda yasa da yawa daga cikin yan Najeriya suke ga kamar baza’a taba samun canji a wannan kasar ba.

Saboda haka, ina da shawarwari guda 10 da nake son na baka a matsayin gudummuwa ta ta tayaka aikin don kawo cigaba da kuma wanzuwar arziki da samun zaman lafiya a wannan kasa tamu ta Najeriya.

Shawara ta 1:

Mai Girma Shugaban kasa, ina maibada shawara akan yadda za’a kara duba bangaren Sharia ta kasar nan, domin har yanzu akwai sauran alkalai da lauyoyin da ba kasar nance a gaban su ba, babban burinsu su tara dukiya ta hanyar karabar kudade masu tarin yawa a gun yan siyasa dake gaban shari’a bisa tuhume tuhumen da ake musu kan cin amanar kasa. Lallai yakamata a duba wannan abu domin samar da aldalci mai dorewa akan duk wani dan Najeriya.

Shawara ta 2:

Kamar yadda kai kokarin karawa jamian yan sanda albashij su a kwanakin baya, yana da kyau ai kokari tabbatar da ana biyan su kudaden su akan kari, kuma ya kamata a saka ido sosai domin wasu daga cikin manyan su sai sun juya kudaden a bankuna don samun kudin ruwa sannan suke fara sakar musu da albashin su wanda hakan yana kawo tsaiko wajen samun kudaden su da wuri. Hakanne kadai zai rage karbar na goro da suke a gun alummar wannan kasa, kuma rashin biyan nasu akan lokacin yana kashe musu gwiwa wajen zage damtse domin gudanar da aikin su cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Shawara ta 3:

Na tabbata nasan kana sane da tashin hankalin da alummar Jihohin Zamfara,Kaduna da kuma Katsina ke ciki game da rashin tsaro, sace mutane da kuma kashe wayanda basuji ba basu gani ba. Mai girma Shugaban kasa, lokacin da za’a ringa amfani da jamian tsaro su kadai wajen gano masu tada zaune tsaye yakama ta ace tuni an wuce wannan tsarin, duniya yanzu tana tafiya ne tare da kayan aikin samar da tsaro na zamani, kamar irin su kyamarori na makalawa a hanyayo yi da kuma wayanda ake harbasu sararin samaniya domin kula da abinda ke faruwa a duk fadin kasa koda ko a cikn daji ne. Ya kamata a duba wannan labari Baba!

Shawara ta 4:

Nasani cewa kai dan kishin kasa ne gaba dayan ta baka daukar bangare a magiya yawancin alamuranka, amman duk da haka Baba, ya kamata ka dubi yankin Arewa wanda tindaga 2003 har zuwa zaben da akai maka na 2019 shine yankin da yafi kowanne baka kuri’u masu tarin yawa. A dogon nazari ba sai anjira manyan yankin sun kawo kokon barar su na ayyuka ba kamar yadda yan uwan mu mazauna yammacin kasar nan keyi, mutumin Manyan Arewa kansu kawai suka sani, dan haka kar jira su, a daure a duba yankin domin shima yasan cewa ana mulkin demokarafiya.

Shawara ta 5:

Alummar wannan kasa wanda ya hada harda mai dakin ka Hajiya Aisha, sun dade suna kuka da cewa akwai wasu tsirarin mutane da basu da mukamin komai a wannan gwamnati taka, amman sun hana komai gudu inda ake zargin sai abinda suka ce ayi akeyi koda a kan harkar daukar mukamai ne sai mutanen da suke so koda ko basu da cencenta su zasu sa a dauka.

Idan har wannan zargi ya tabbata gaske ne, ya kamata Baba a duba na tsanaki wajen janye irin wayen nan mutane daga jikin ka ko sa barka kaiwa Alummar da suka zabe ka aiki!

Shawara ta 6:

Bangaren aikin Hajj waje ne da yake da muhimmancia tsarin tafiyar da gwamnatin wannan kasa harma da bunkasar tattalin arzikin ta, amman duk da haka Alumma na kokawa da yadda duk shekara ake samun karin kudin aikin Hajj wanda haka bakaramin kashewa mutane maniya ta da dama gwiwa ya ke ba. Har shekaru biyu da suka gabata an ta samun zarge zargen badakalar kudade a Hukumar Aikin Hajin ta kasa(NAHCON). Baba ina mai bada shawara a samar da wasu mutane masu amana, amintattu dan su kara bibiyar yadda ake tsara fitar da kudin aikin Hajj a wannan kasa!

Shawara ta 7:

Duk kusan bayanan da ke kunshe a cikin shawarwari na,  babu wanda za iya cimma nasara akan sa in ya zamanto babu ingantaccen ilimi a wannan kasa, Baba!
Ya kamata ayi dokar tabaci a wangaren ilimi, lalacewar ilimi fa a wannan kasa ta wuce duk yadda wani mutum yake tunani, maganr gaskiya sai an saka ido sosai wajen dawo da martabar ilimi a wannan kasa. Dayawa daga cikin maynayn karatarori da kanan su, sune suka mallaki makarantu masu zaman kansu, dan haka bazasu taba bari harkar ilimin gwamnati da bunkasa ba sabo da zata kashe musu tasu.

Lallai asa binciki mai tsauri kuma duk wanda aka kama da irin haka a kulle makaranta, sannan a bunkasa bangaren makarantun gwamnati a duk fadin kasar nan, mallamai a samar musu da ingantattun kayan aiki, tare da biyansu kudaden albashi cikin lokaci. In kai haka Baba, lallai zakasha mamakin yadda ilimi zai bunkasa cikin lokaci kadan a wannan kasa.

Shawara ta 8:

Mai girma Shugaban kasa, ina mai baka shawara akan duba yadda tsarin tsaron dukiya da kuma alummar wannan kasa yake a fiyalen jiragen kasar nan da kuma bodojin kasar baki daya. Lallai abinda ya faru da Zainab yar Jihar Kano babban kalubalai ne, an dade ana aikata irin wannan barna, domin kamar yadda bincike ya nuna an kashe mutane da dama a kasashen wajen bisa tuhumar safarar gwayar basusan ma yadda ta shiga cikin jakukunan su na tafiya ba.

Yadda ake tantance mutane kafin su hau jirgi a kasan nan gaskiyar magana bazai taba hana shiga ko fito da kwayoyi ba, kuma bazai hana masu mugun nufi ci gaba da bunnewa fasinja kwarar a jakara ba.

Shawara ta 9:

Kamar yadda muka shiga matsanancin faduwar tattalin arziki a wannan kasa, duk da cewa amfita, ya kamta ka kafa kwamati na masana tattalin arziki wayanda ba masu son zuciya ba, domin su zama aikin su tsara yadda tattalin arzikin kasar nan zaici gana da bunkasa mai makon komawa baya. Lallai masana sunta magana cewa gwamnatin ka ta baya bata da kwararru akan tattalin arziki, ina bada shawara a wannan mataki na gaban, ayi kokari a jarraba yin hakan.

Shawara ta 10:

Matsalar aikin yi a Najeriya bazata taba magabtuwa ba indai harkokin masana’antun mu basu dawo ba, kamar yadda mukaga ka dukuga wajen kokarin gina tashar wutar lantar ki a garin Manbilq na Jihar Taraba, kamatayi a kara bunkasa wasu yadda wutar zata fi bukatun yan Najeriya ma. Idan akai hakan, sai ka danar da duk wanda yake da Kamfani a fadin kasar nan ambashi wasu lokutu ko ya tashi ko kumq a kwace gwamnati ta tashe su da kanta daga baya asaya abashi kudin sa, ko kuma ta basu rance idan basu da karfin jari a yanzu domin tashin su.


Hakanne kadai zai sa matasan mu dake da karatun degree da dama babu aikin yi, su samu ayyuka, kuma wannan kadai zai rage karfin cin hanci da rashawa sosai a wannan kasa, saboda yawan kamfanonin mu dabasa aiki in suka tashi babu wanda zai jira sai gwamnati ta bashi aiki duk cen zaa tafi.

Shawarace daga daya daga cikin masu kaunar ka kuma masoyan ka dake tare dakai tin 2003 da kafara siyasa.



Hassan Auwalu Muhammad, Dalibi mai koyon aikin Jarida a Tsangayar Koyon aikin Jarida dake Jami’ar Bayero Kano.



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke



Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.



Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.



Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode








TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user