Saturday 15 June 2019

KARANTA JAWABIN SHUGABA BUHARI MASU RATSA ZUCIYA

Tura Wannan Zuwa Ga
Na yanko wasu bangare cikin jawaban da shugaba Buhari ya gabatar shekaran jiya Laraba 12-6-2019 don tunawa da ranar da aka assasa tsarin Mulkin Demokaradiyyah a wannan Kasa tamu Nigeria.Muhammadu BuhariMarubuciDatti Assalafy
Shugaba Buhari yace:8. Ni da dukkan 'yan Nigeria dole muyi jinjina da godiya ga rundinar  sojin Nigeria da rundinar 'Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro bisa aikinsu na sadaukarwa dare da rana don su karemu su kare mana ci gabanmu

9. Ta'addanci da rashin tsaro matsalace ta dukkan kasashen duniya, hatta manyan kasashen duniya da suke da ingantaccen tsaro suna fuskantar karuwar matsaloli na tsaro a cikin kasashensu

10. Babban burin wannan sabuwar gwamnatin shine ta daura akan nasarorin da ta samu cikin shekaru hudun da suka gabata, a yanzu kuma wannan sabuwar gwamnati zatayi la'akari da kusakuran da aka samu a baya don a gyara don ta magance dukkan matsalolin Kasar, sannan ta gabatar da shirinta na gina sabuwar Nigeria

11. 'Yan uwa 'yan Nigeria, na samu damar da nayi karatun Firamare kyauta, na je makarantar ma'aikata na sojoji, har zuwa makarantar horo akan yaki

12. Na fara karatuna a Katsina, da Kaduna, sannan nayi karatuna a babban mataki na ilmi a Kasar Ingila, India da Amurka

13. Nayi aiki a garin Kaduna, Lagos, Abeokuta, Makurdi, Port Harcourt, Maiduguri, Ibadan, Jos daga karshe yanzu ina aiki a Abuja, gaba daya rayuwata na gudanar da itane akan bautawa al'umma, bani da wani abinyi sama da bautawa al'umma, ban iya wani aiki ba sama da bautawa al'umma

14. Na taba tsintar kaina cikin mawuyacin hali lokacin da muke kokarin tabbatar da Nigeria a matsayin kasa daya dunkulalliya, har a yanzu babu abinda zanyi sama da na tabbatar da cewa na bada rayuwata don tabbatar da Nigeria ta cigaba da kasancewa a matsayin kasa guda daya, tare da daga darajar 'yan Nigeria

18. Yawancin rikici da tashin hankali na kabilanci da banbancin addini dake faruwa a wannan kasar tamu akwai wasu kebantattun mutane 'yan siyasa da wasu shugabannin addini da suke daukar nauyin tashe tashen hankulan don su haddasa rabuwa a tsakaninmu, da haddasa gaba, da cimma burin kansu, wanda hakan yana matukar gurgunta mana Kasarmu

19. Kasarmu Nigeria babban kasace a duniya, bisa hasashen Majalisar dinkin duniya, yawan al'ummar Kasarmu zai kai mutum miliyon dari hudu da sha daya (411) zuwa shekarar 2050, wato nan da shekaru 31 masu zuwa, hakan zaisa mu zama Kasa ta uku a duniya da suke da yawan al'ummah bayan Kasar China da India

23. Mu 'yan Nigeria muna alfahari da tarihinmu tun daga lokacin da muka samu 'yancin kai a shekarar 1960, mun baiwa majalisar dinkin duniya gagarumin gudunmawa wajen kwantar da tarzoma a ko'ina a duniya, mune muka kashe wutar yaki a Kasar Liberia, Sierra Leone, Ivory-Coast, sannan shekaru biyu da suka gabata mun kashe wutar yaki da tayi yunkurin tashi a Kasar Gambia

24. Imba don Nigeria ba da batun 'yanto Kasashen Angola, Mozambique, Namibia, Zimbabwe da South Africa daga fitinar yaki abune da zaiyi matukar wahala, wannan bayanin ba wani bane ya yabbatar dashi ba face marigayi Nelson Mandela

27. Lokacin da muka karbi ragamar shugabancin Nigeria a shekarar 2015 bayan ansha gwagwarmaya, mun gano manyan matsaloli guda uku wanda sune muka saka gaba tun lokacin yakin neman takara, sune matsalar tsaro, matsalar tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa

28. Babu wanda zai yi jayayya akan cewa cikin shekaru hudu da suka gabata ba muyi kokari wajen magance wadannan manyan matsaloli guda uku ba gwargwadon iko

29. Bayan nayi rantsuwar kama aiki a ranar 29 ga watan biyar na shekarar 2015 akwai babbar matsala na rashin tsaro, bayan kananun hukumomi guda 18 a yankin arewa maso gabas dake karkashin ikon 'yan ta'addan Boko Haram, mayakan Boko Haram suna iya kaddamar da harin ta'addanci a kowani birni dake fadin tarayyar Nigeria har da babban birnin tarayya Abuja, sannan Boko Haram zasu iya kaddamar da hari a kowace ma'aikata har da ginin Majalisar dinkin duniya, da babban helkwatar rundinar 'yan sandan Nigeria, a haka na karbi mulki

30. Mun yarda cewa har yanzu akwai matsalar tsaro na garkuwa da mutane da ayyukan 'yan bindiga a wasu kauyuka, amma a akwai banbanci mai girma daga tsakanin shekarar 2015 da muka karbi mulki zuwa yau, kuma muna ta kokarin ganin cewa mun shawo kan matsalolin tare da goyon bayan hukumomin tsaro ta hanyar amfani da kudi, wadatasu da kayan aiki, da musayar bayana sirrin tsaro, muna dab da magance wadannan matsaloli tare da gagarumar nasara... ~Muhammadu Buhari

Wannan shine fassaran jawabin da shugaba Buhari yayi cikin harshen turanci, sai na tattaro guraren da yayi bayani akan tsaro na fassara har da nambobinsu, akwai sauran bayanai masu yawa da yayi da harshen turanci, ana iya duba shafin mai taimaka masa da yada labarai Mr Femi Adesina.


Jama'ar Nigeria da muke tare a wannan dandali na Facebook, ko kuna da shawaran da zaku baiwa shugaba Buhari akan inganta tsaron Nigeria?

Sannan ku fada mana matsaloli na tsaro da suke faruwa a yankin ku, ina so kowa ya bayyana mana halin tsaro a yankinsa

Nima ina da wata shawara da nakeso na rubutawa shugaba Buhari akan hanyar da zaibi ya inganta tsaron Nigeria da taimakon Allah, makusantan shugaba Buhari ku taimaka wajen isar masa da sakon da zaran na wallafa.

Muna rokon Allah Ya taimaki shugaba Buhari Ya bamu zaman lafiya a Kasarmu Nigeria Amin.Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryar Hausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina sukeDomin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslimi cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Wakokin Gargajiya, Wakokin Siyasa, Wakokin Zamani, Wakokin Bege na Annabi Muhammad (SAW) , Sharhi akan al'umaran Yau da Kullum , Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya.Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user