Monday 9 July 2018

HIKAYAR GIMBIYA HARIBAI: ƊIYAR SARKIN DAULAR PITUGAR DAKE HINDU

Tura Wannan Zuwa Ga
A wani lokaci mai tsayi daya gabata a Hindu, anyi wani sarki a
daular Pitugar mai jiji-da-kai. Sunansa Dheema.


Marubuci: SADIQ TUKUR GWARZO

Sarkin yana da ƴaƴaye ƴammata guda biyu, dukkansu
kyawawa ne.

Ɗaya ta faye yawan surutu, gata da halin ko-in-
kula, sunanta Kalimbai. Ɗayar kuwa sunan ta Haribai, kuma ita
mai shiru-shiru ce da natsuwa.
Da lokacin aurensu yayi, sai wani hamshaƙin attajiri ya fito
neman auren babbar cikinsu watau Kalimbai, ai kuwa sarki ya
bashi aurenta. Akayi gagarumin biki na ƙawa, duk gari kowa sai
labari yake saboda kece raini da akayi a wannan biki.

Bayan biki ya ƙare, sai Sarki Dheema ya lura da kaɗaicin da
ɗiyarsa Haribai take fama dashi tun bayan auren yayarta
Kalimbai, don haka sai yakan ware lokaci yana zuwa ɗakinta
suna firar duniya da ita.

Rannan sarki ya shiga ɗakin Haribai suna taɗi kamar yadda
suka saba, sai idanuwansa yakai ga wani fai-fai a ɗakin mai
ɗauke da rubutu kamar haka: "Duk gidan da mace mai hikima
take a cikinsa, a koda yaushe zai rinƙa bunƙasa"
"Wanene ya sanar dake wannan zance?" Sarki Dheema ya faɗa
yana mai nuni da rubutun dake jikin fai-fan.

"Babu wanda ya sanar dani, amma da kaina nayi imani da
hakan" Haribai ta bashi amsa.
Sarki Dheema yayi murmushin yaƙe saboda yadda zuciyarsa ta
sosu daga wannan magana.

Yace "kinga, ni Sarki ne, kuma kasancewata a gidan nan shine
yasa komai da komai yake bunƙasa acikinsa. Don me zakice
sai gida na ɗauke da mace mai hikima zai bunƙasa?"
Haribai tace "Baba, magana ta fa haka take. Bunƙasar gidan
nan ta dogara ne ga Hikimar mahaifiyar mu"
Sarki ya fusata, ya daka mata tsawa yana muzurai, yace sam
ba haka wannan zance yake ba. Amma Haribai ta dage kai-da-
fata cewar hikimar mahaifiyarsu a wannan gida ne sanadin
haɓaka da albarkar gidan baki ɗaya.

A ƙarshe Sarki ya tashi ya fice daga ɗakin, yana tunanin hanyar
da zai ladabtar da wannan ɗiya tasa, har ta gane cewa tayi laifi
babba.

Akan haka ya ƙudurce cewa shine zai lalubo mata
ƙasƙantaccen mutum ya haɗata aure dashi.
Cikin wannan mako Sarki Dheema ya lalubo wani mutum mai
sana'ar saran itatuwa da faskarawa mai suna Nandu, yace
masa "Kai Nandu! Zan aura maka ɗiyata Haribai"
Nandu yace "Ranka ya daɗe ni talaka ne, sam-sam ba zan iya
ɗaukar ɗawainiyar rayuwar jindaɗin da ɗiyarka zata iya buƙata
daga gareni ba. Don haka bani iyawa".

Sarki Dheema yace "aikuwa zaɓi biyu gareka, kodai ka auri
Haribai ko kuma nasa a datse min kanka"
Ba shiri Nandu yace ya yarda da wannan aure.

Duk da irin dagewar da waziran Sarki gami da iyalansa sukayi
akan hana wannan aure, amma ya kafe sai da akayi.

Haribai kuwa bata taɓa ɗaga kanta akan lamarin ba.

Akayi biki babu armashi, ta tafi tarewa a wani ruɓaɓɓen gida da
mijinta Nandu ke rayuwa aciki nesa da gari.

A kullum da garin Allah ya waye, Nandu zai ɗauki gatarinsa ya
tafi daji sana'arsa ta saran itace. Acan ne zai wuni aiki, sai da
marece zai siyo kayan abinci da ɗan abinda ya samo, sannan
ya kaɗo kansa gida abinsa, ita kuwa matarsa ta sarrafa abinda
ya kawo ɗin zuwa abinci.

Sai Haribai ta lura da cewa tana wuni bata aikin komai a gida
har sai mijinta ya kawo kayan abinci da yamma take aiki.

Don
haka rannan sai ta shaida masa cewar "ina ganin, daga yau, ka
rinƙa raba ƙuɗin da kake samowa zuwa gida uku, kashi biyu ka
siyo mana abinci wanda zamuci sau biyu a rana, kashi ɗayan
kuwa mu rinƙa tara shi, idan yayi yawa sai mu ƙaro sabon
gatari.. Inaso na rinƙa binka daji aiki."

Abinda ya faru kenan, babu jimawa kuɗin siyan gatari ya taru.
Suka siya suna zuwa daji saro itace tare. Ya zamana ƙuɗin da
suke samu a wannan aiki da wanda suke ajiyewa tari duk sun
ƙaru.

Jimawa kaɗan kuma sai Harimbai ta sake samun wata
dabarar. Ta sanar da mijinta cewar ta lura da cewar
maƙwabciyarsu nada dutsen tishi da ake niƙa alkama izuwa
fulawa, don haka tana ganin ya kamata su siyo shi domin ƙara
haɓaka hanyar samar da kuɗinsu.

Nandu yayi murna matuka da haka, yace "duk yadda kikace
haka za'ayi". Ya ɗauki kuɗin da suka tara ya nufi kasuwa. Bai
dawo ba sai da ƙaramin dutsen tishi na dai-dai kuɗinsu.

Sannu a hankali ya zamana suna iya samar da kuɗin da zasu
iya warware matsalolin gabansu.

Ita Haribai a iya niƙan data keyi tana samar da abinda zasuci a
kullum. Don haka duk kuɗin da Nandu zai kawo gida ajiyewa
kurum akeyi.

Daga baya sai Nandu ya ware fili a gidan, ya zamana a kullum
itacen yake kawowa ya ajiye ba tare daya siyar ba.

Rannan akayi sa'a, lokacin ana fama da muku-mukun sanyi,
sai wani Sarki yazo shigewa ta wannan ƙasa da jama'ar sa.

Ya sauka a wani daji nesa da gari, sannan ya umarci barorinsa
su bazama nemo itacen da za'a hura wuta don jin ɗumi.
Koda isowar barorin cikin gari, sai sukayi kiciɓus da gidan
Nandu mai ɗauke da tarin itace. Sai kuwa suka nuna
buƙatuwarsu ga wannan itace. Nandu ya siyar dashi baki ɗaya
garesu. Ai kuwa ya samu riba mai yawa daga wannan ciniki.

A wannan lokaci, Kar kaso kaga murna wurin Harimbai da
Nandu.

Rannan kuma, Nandu yana saran itace, sai yazo kan wata
bishiya mai kyau. Ganyayenta yala-yala, itacen jikinta kuwa
sala-sala ne.

Daya komo gida sai yake nunawa matarsa kalar itacen daya
samo a wannan ranar. Sai ta cika da murna, tace "Maigida,
wannan ai itacen Sandal ne mai daraja. Aikuwa ya kamata ka
ƙoƙarta samo irinsu da yawa ka girke a gidan nan".

Kasancewar Haribai daga gidan sarauta take, ta san darajar
wannan itace. Domin sarakuna sunfi son ayi amfani dashi
wajen ƙone gawarsu idan sun mutu ko kuma wajen shagalin
bukuwan Havan da Pujan.

Kashe gari Nandu ya tafi daji, ya lalubi wannan itaciya ta
sandal tare da soma saran ressan ta a hankali ta yadda zata
ƙara tohowa. Haka ya rinkayi a kullum, daga wannan zuwa
waccan, har sai daya tara wannan itace da yawan gaske.

Akwai wata alƙarya a kusa da birnin Pitugar wadda aka wayi
gari Sarkinta ya rasu. Kafin rasuwarsa kuwa attajirin gaske ne.
Har kuma yayi wasicci da a ƙone gawarsa da itacen Sandal
bayan rasuwarsa.

Sai dai kuma akaf garin, an rasa wanda keda wadataccen
itacen sandal da zai isa shagalin wannan biki. Akan haka ɗan
sarki mai mutuwa ya bada cigiya zuwa maƙwabtan birane, har
kuma akazo masa da labarin cewa akwai wani mai suna
Nandu yana dashi.
Sai yace aje wajensa a siyo masa itacen akan ko nawa ya
yanka.

Barorin ɗan sarkin sukayi murna da suka tarar da cewa Nandu
nada kalar itacen da uban gidansu keso kamar yadda labari
yaje gareshi. Suka siyi itacensa da darajar gaske.

Daga nan fa Nandu da mai ɗakinsa suka fita daga kangin
talauci. Tunda sun samu tarin dukiya.
Nandu yasa aka gina musu ƙatan gida na sarauta mai cike da
manyan zauruka, kai kace gidan sarkin garin ne.

Bayan tsawon lokaci da auren Nandu da Haribai, sai
mahaifinta Sarki Dheema ya cika da tausayin ƴartasa, har ya
soma da-na-sanin hukuncin daya ɗauka akanta.

Rannan sai ya yanke shawarar ya kai ziyara a garesu duka
domin ganin halin da suke ciki.
Bayan ya gama shirya kyaututtukan dazai kai musu, sai ya tashi
tare da da barorinsa, kai tsaye ya nufi gidan babbar ɗiyarsa
Kalimbai. Yana ɗokin ganinta, a zuciyarsa yana rayawa cewar
tabbas tana cikin farin ciki.

"Ɗiya ta Kamli, yaya kike?" Sarki Dheema ya faɗa yayin
haɗuwar su da Kalimbai.

Kalimbai ta rugo da murna, ta gaishe da mahaifinta. Sannan ta
gabatar masa da ƴaƴayenta waɗanda tace ƙiriniya tayi musu
yawa, ko makaranta ma basa zuwa.

Sarki Dheema ya kaɗu da yadda yaga wannan gida duk a
hargitse. Ga yara duk babu natsuwa. Sannan Barori biyu ne
kaɗai suka rage a gidan, yayin da a farkon aurensu gidan cike
yake da masu hidimta musu. Tabbas da alamu karayar arziƙi
ta gitta a wannan gida.

Ai kuwa da Sarki ya zanta da ɗiyar tasa sai ya gane cewar
itace silar durƙushewar maigidan nata, domin kullum cikin
buƙatar kashe kuɗaɗe take, ta gaza sauya rayuwa daga wadda
ta saba a gidan sarauta zuwa gidan aure data samu kanta.

Ran Sarki Dheema a ɓace ya fito gidan, yace gida zai koma
domin shawarta abinyi.
Yana isa kuma sai akazo masa da katin gayyata, akace masa
wani attajiri ne yayi sabon gida yake gayyatarsa bikin tarewa
domin neman albarkarsa.

Da sarki ya isa gidan, sai yake ta mamakin girma da kasaitar
sa. Mai gidan ya fito ya tarbeshi. Sarki yayi mamakin yadda
wannan baƙon attajiri yazo garinsa ya bunƙasa ba tare da
saninsa ba.
Ana haka sai ga ƴarsa Hambai ta fito cikin kayan ƙawa, tana
ɗauke da murmushi a fuskarta, tana mai marhaba lale ga
mahaifinta.

"Sannu da zuwa mai martaba mahaifina".
Sarki Dheema ya cika da mamaki, "ɗiya ta, gidan kine
wannan!!!?"

Ta amsa masa da cewa "kwarrai kuwa"
"Tayaya haka ta faru?" inji Sarki Dheema.

Hambai tace "Ranka ya daɗe, ka tuna da abinda ka taɓa
karantawa a ɗaki na?.." Daga nan cikin ladabi ta zayyana masa
duk hanyoyin da suka bi har rayuwarsu ta zamo haka.

Sarki Dheema ya gyaɗa kansa sama cikin mamaki. Ya raya a
zuciyarsa cewa hakika ƴarsa tayi gaskiya.. Duk gidan dake
ɗauke da Mace mai hikima, wannan gida sai ya bunƙasa.."

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.Com.ng
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user