Monday 9 July 2018

KARANTA KAJI: ABUBUWA GUDA 5 BA'A SANIN SU SAI DA ABUBUWA GUDA 5

Tura Wannan Zuwa
ABUBUWA GUDA BIYAR BA'A SANINSU SAI DA
ABUBUWA
GUDA BIYAR :

1. Ba'a sanin darajar Bishiya sai ta dalilin
'Ya'yanta.

2. Ba'a gane mace ta kirki acikin mata sai yayin
da Mijinsu ya
talauce.

3. Ba'a gane aboki na kirki sai yayin da kake cikin
Tsanani.

4. Ba'a gane Mumini na kirki sai a lokacin da
Jarrabawa ta
sameshi.

5. Ba'a gane Mutum mai karamci sai yayin da
bukata ta tashi.


ABUBUWA GUDA BIYAR SUNA ZUWA DA
ABUBUWA GUDA
BIYAR :

1. Yawan Istighfari yana kawo yawaitar Arziki da
'Ya'ya.

2. Runtse idanuwa daga kallon Haram yakan
kawo Hasken
basira.

3. Kunya tana kawo alkhairi.

4. Taushin Kalamai yakan kawo samun abinda
ake nema.

5. Fushi yakan kawo Nadama.

ABUBUWA GUDA BIYAR SUNA JUYAR DA
ABUBUWA GUDA
BIYAR :

1. Taushin Kalamai yana juyar da Fushi.

2. Neman tsari daga Allah yana juyar da sharrin
Shaitan.

3. Bin abu cikin nutsuwa yana juyar da nadama.

4. Kamewa harshe yana juyar da yin Kuskure.

5. Addu'a tana juyar da mummunar Qaddara.

MUTANE GUDA BIYAR, SAMUN KUSANCI DASU
BABBAN
ARZIKI NE :

1. 'Da (Yaro) mai biyayyar Iyaye.
2. Salihar Mace ta kirki.
3. Aboki mai rikon alkawari.
4. Makobci Mumini na kirki.
5. Malami Faqeehi (Masanin Fiqhu) Mai tsoron
Allah.

ABUBUWA GUDA BIYAR SUNA QARA MA
ABUBUWA GUDA
BIYAR DA'DI :

1. Lafiyar Jiki tana Qara ma mutum Jin dadin
wadatar da yake
da ita.

2. Abokan tafiya na kirki suna Qara ma tafiyar
da'di.

3. Kyawawan Halaye suna Qawata Kyawun
Halitta.

4. Hutun Zuciya yana Qara ma Barci dadi.

5. Zikirin Allah cikin dare, yana Qara ma daren
da'di.

ABUBUWA GUDA BIYAR SUNA 'DAGA MARTABAR
MUTANE
BIYAR :

1. Aiki da Ilimi yana Qara martabar Malamai.

2. Tsayawa kan gaskiya yana Qara martabar 'Yan
kasuwa.

3. Rikon amana yana Qara martabar Ma'aikata.

4. Girmama Malamai yana Qara martabar dalibai.

5. Kyauta tana Qara ma Mawadaci Martaba.

Allah ya bamu ikon yinsu.

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user