Monday 23 March 2020

Karanta Muhimman Abubuwa 10 da Yakamata Ku Sani Dangane da Cutar Coronavirus

Tura Wannan Zuwa Ga
Babban Malamin addinin musuluncin nan, Dr. Muhammad Sani Umar Rijiyar lemo (Allah Ya kara masa lafiya da albarka) ya ja hankulan al'ummar musulmi dangane da cutar nan ta sarƙewar numfashi (Covid 19) da ta addabi duniya a halin yanzu.

Tataccen Bayani Akan Cutar Sarƙewar Numfashi (CORONAVIRUS) A Mahangar Musulunci

Babban Malamin ya gabatar da wannan Jawabi ne a Majalisin sa da ya saba gabatar da karatu a dukkan ranakun Laraba, a Masallacin Cibiyar Imamul Bukhari dake Unguwar Rijiyar Zaki a cikin birnin Kano.

Ga bayanin da Babban Malamin ya gabatar a taƙaice:

Zan yi amfani da wannan dama kafin mu fara karatu domin tunatar da 'yan uwa musulmai a kan yanayin da duniya take ciki a halin yanzu na afkowar cutar nan da ake kira da (Corona Virus).

Mu duba mu gani yadda wannan 'Yar ƙaramar ƙwayar halitta ta cuta, wacce ko da abin hangen nesa (Microscope) sai an ƙura ido sosai ake iya ganin ta, amma gashi ta mayar da kowa gida, ta tayar da hankalin duniya, har ƙasashe masu tinƙaho da ƙarfin kimiyya da karfin tattalin arziki, da cigaba, hankulansu ya tashi! Lissafinsu ya birkice, duk wani abu da suke tunƙaho dashi bai iya amfanar dasu komai ba. Wanda wannan lallai shi zai nuna maka ƙarfin Ikon Allah, zai nuna maka babu wani wanda ya isa gaba ga Allah.

Mu al'ummar musulmi ga matsayar da ya kamata mu ɗauka dangane da wannan cuta:

1. Kallon da musulmi ya kamata su yi wa wannan cuta daban yake da na kafirai, haka a cikin musulmai ɗin ma, mai karanta Alkur'ani da Sunnar Annabi (S.A.W) kallon da zai yi mata daban yake da na wanda ba ya karantasu. Mu musulmi mun yi imani da Ƙaddara, duk wani abu da ya faru to dama can Allah Ya san da shi, kuma bai faru ba sai da ganin damar Allah, saboda babu abinda ke gudana a cikin Mulkin Allah sai da izininsa sai da saninsa. (Malamin ya ambaci ayoyin Alkur'ani mai girma a kan haka).

2. Mu musulmi mun sani cewa ba wannan ne farau ba, ba yanzu aka fara samun irin wannan annoba ba, Allah Ya sha aiko da azabarsa ga al'ummomi da suka gabace mu, saboda sun kangarewa tafarkinSa, sai Allah Ya aika musu da annoba iri daban-daban, misali: mutanen Fir'auna Allah Ya aika musu da annoba iri-iri, kamar annobar ambaliyar ruwa, annobar jini, duk abinda suka buɗe sai suga ya zama jini, annobar fãra da kwarkwata. A ƙarshe kuma Allah Ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Nuhu kafinsu, Allah Ya aiko musu ambaliya ya halakar dasu, haka mutanen Annabi Lud Allah Ya kifar dasu suka halaka baki ɗaya.

3. Duk da cewa ita wannan al'umma ta Annabi (S.A.W) Allah Yayi alƙawarin ba zai tumɓuketa Ya halakar da ita baki ɗaya ba, idan da Allah Ya so haka ɗin tabbas zai iya, irin waɗannan musibu sun isa shaida a kan haka, to amma Allah sai ya aiko da irin wannan annoba domin jan kunne da kashedi ga bayi. Yayin da annobar tazo kuma bata banbance salihi nagari da na banza, kowa haɗawa take dashi, sai dai tana zama Rahama ga Salihai, azaba kuma ga fanɗararru.

4. Daga cikin darasin da ya kamata musulmi ya lura dashi a kan sha'anin wannan cuta, mu duba mu gani, a lokacin da Ɗan Adam yake tutiya, yake tunƙaho cewa ya mallaki ilimi, ya mallaki ƙarfin tattalin arziki, wasu har suna ganin Allah ma baya yi musu komai, su sun isa, su sune!!! Kwatsam sai ga wata 'yar ƙaramar halitta daga halittun Allah, wacce ido ma baya iya ganinta saboda tsabar ƙanƙantar ta, sai gashi ta baza duniya, ta bazama manyan ƙasashe, tattalin arziki yana ta rushewa, kowa ya firgita. Lalle wannan ya isa wa'azi! Wannan ya isa shaida akan girman Allah da ƙarfin mulkinSa.

5. Mu musulmi mu sani cewa babu abinda zai yaye mana wannan annoba illa kaɗai mu koma ga Allah, mu guji dukkan abubuwanda ke janyo Allah Yayi haka ga al'umma, kamar manyan laifuka, Zinace-Zinace, Zalunci, Ɓarna a bayan ƙasa.

6. Mu sani cewa komawa ga Allah shine matakin farko domin magance wannan annoba, duk wani abu da ba wannan ba ciko ne, amma komawa ga Allah shi ne Jigo. Mu koma ga Allah da yin addu'o'i da yin istigfari.

7. Mu sani cewa lalle babu wata musiba da wuce a jarrabeka a cikin addininka, yau gashi ana ta rufe masallatai, ana hana fitowa sallar Jam'i, har sallar juma'a da yawa daga ƙasashe sun bayarda sanarwa a dakata sakamakon wannan cuta. Lalle wannan abun tsoro ne! Kamar Allah Yayi fushi da mutane ne yace: Ku fita ku bar min ɗakuna na (Masallatai) tunda ɓarnar ku a bayan ƙasa tayi yawa. Babbar musiba ce a rabaka da ɗakin Allah, a ce babu Umarah, babu Ɗawafi, babu sallar Jam'i, lalle babu musibar da tafi musiba a cikin addini. Tabbas Allah Yana fushi da mutane, Ya zama wajibi mu koma mu tuba ga Allah.

8. Musulunci ya yarda da tsarin killace marasu lafiya, da kuma tsarin kare kai daga cututtuka, musulunci shi ya fara zuwa da irin wannan tsari. (Malamin ya ambaci Hadisi a kan haka) amma kuma a musulunci munyi imani da cewa zama da mai cuta ba shi ke janyo kamuwa da cuta ba har sai idan Allah Ya hukunta haka, cuta a karan-kanta bata da ikon shiga tayi tasiri a cikin mutum sai da ganin damar Allah. ita cutar sababi ce, sababi kuwa baya aiki a karan-kansa sai idan Allah Ya ƙaddara, mu duba mu gani, wuta a al'adarta tana ƙona mutum, amma Annabi Ibrahim da aka jefa shi a wuta sai Allah Ya sa wutar taƙi ƙona shi, mu duba ruwa yana dulmiyar da mutum, amma sai Allah Ya sa Annabi Musa da mutanensa suka taka saman ruwa suka wuce ba tare da sun dulmiya ba, saboda haka ko da abu sababi ne, Allah Yana iya zare sababiyyar yaƙi yin aiki. A musulunci mun sani cewa duk abinda ya sameka ba zai kuɓuce maka ba, duk kuma abinda ya kuɓuce maka ba mai samunka bane. Kamar yadda Annabi (S.A.W) Ya faɗawa Abdullahi Ɗan Abbas.

9. Irin wannan annobar an sha yinta a baya, a lokacin Sahabbai an samu annoba da tayi sanadiyyar rasuwar wasu daga cikin Sahabbai, kamar: Mu'az bin Jabal, da Abu Ubaida bin Aljarrah da sauran su, wannan ya faru a shekara ta (18) bayan Hijra.

Haka nan akwai annobar da aka taɓayi inda tayi sanadiyyar mutuwar 'ya'yan Anas bin Malik kusan mutum saba'in (70), da Ƴaƴan sahabi Abu Bakrata kusan Mutum arba'in (40).

10. Na daga cikin abinda zai magance irin wannan annoba, gujewa aikata Zalunci, danne haƙƙin mai haƙƙi, wajibi ne shugabanni su riƙi yin adalci su guji yin zalunci, domin zalunci sababi ne afkawa irin wannan masifa.

A ƙarshe Malamin yayi addu'a mai ratsa zukata, inda Ya roƙi Allah da Ya yaye mana wannan masifa ba don halinmu ba, Allah Ya dube mu da Rahamarsa da Ludufinsa ya kawo mana agaji.

Waɗannan bayanai an tattaro su ne a taƙaice daga jawabin babban Malamin, mai buƙatar cikakken jawabin sai ya nemi karatun littafin (Alwabilussayyib) darasi na 149.

Marubuci:
Musa Muhammad Dankwano.
Secretary, Dr. Muhd Sani Umar R/lemo Academic Forum.

المنتدى العلمي للدكتور محمد الثاني عمر

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user