Thursday 26 March 2020

Kowa Sai Yayi Nadama Kowa Sai Yayi Kuka

Tura Wannan Zuwa
A duk lokacin da aka rufe kowacce ƙofa tsanani yayi yawa, dole kowa ya nema ma kansa mafita. Idan aka ce aiki sai ɗangata shi kuma mara gata zai nemawa kansa mafita mai kyau ko mara kyau. Ka yi duk yadda zaka yi ka ci zaɓe amma yawo ya gagare ka.

KOWA SAI YAYI NADAMA KOWA SAI YAYI KUKA..

Marubuci: Dr. Ahmad  Ibrahim BUK

Bafulatani da bai damu da waye Shugaban ƙasa ko Gwamna ko Sanata ba yana rayuwa a daji daga shi sai shanunsa, bai damu da kwalta ko lantarki ba, ya samar da nama da madara da man shanu, an taɓo shi ya nemi mafita ta hanyar kama mutane a ba shi kuɗi.

Mutum har cikin gidansa za a je a sace shi a sace iyalansa, yawo a manyan motoci ya gagari Shugabanni. Aiki ya zama daga 'ya'yan masu mulki sai 'ya'yan masu Naira. Kowa yana ji yana gani an rasa zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Zalinci da rashin manufa ya sa waɗanda ya kamata su samar da aminci suna neman koyawa mara gata ya nemi gata ta hanyar tayar da hankali da barazana ga rayukan mutane. Yau AK47 na neman zama abinda mara gata zai nema don nemawa kansa gata a wajen masu gata. Yara ƙanana sun iya sarrafa AK47 sun kuma san inda zasu nema su samu.

Duk dabara da azancin mutum bai isa ya gyara wannan matsala ba har sai an gyara hanyoyin da suka haifar da matsalolin. Allah ba ya jefa mutane a bala'i haka kawai har sai sun aikata abinda zai janyo bala'in. Allah baya shafe alheri da jin daɗin mutane har sai idan su suka aikata abinda zai shafe alherin.

Kowa sai yayi nadama kowa sai yayi kuka matuƙar ba a yarda akwai matsala an kuma yarda a gyara ba.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user