Friday 27 March 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (19) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
DA KAYAN KAI AKE NA RATAYA

Akwai hikima mai girman gaske mutum ya fara tunanin yin wani abu a gefe nasa na kansa wanda zai taimake shi, in likita ne yana da kyamis, in babban malamin makaranta ne yana da wata 'yar makaranta a gefe koda kuwa ta lesson ce, in kanikanci kake yi a wurin wani maigidanka na tsawon lokaci ka sami wani ɗan wuri a ƙofar gidanka kana gyara wa maƙwabta mashinansu, in kafinta ne ka fara gyara wa mata 'yan kujerunsu a cikin gida lokacin da ba za ka je wurin aiki ba, wannan shi ne wayewa, a duk lokacin da ka gama ƙwarewa ko ba a sallame ka ba za ka yi naka na kanka.

Yi Tsari Mai Kyau...

MarubuciBaban Manar Alkasim

Akwai hikima mai girman gaske mutum ya fara tunanin cewa zai iya yin wani abu nasa na kansa, koda kuwa talaka ne kamar yadda muka lissafo bare wani babban ma'aikacin gwamnati mai aiki a wata babbar ma'aikatar tatse 'ya'yan bishiya, in mutum na samun kuɗi ya gane cewa in fa ya sauka daga muƙaminsa kuɗinnan da yake samu sun gama shigowa kenan sai dai kuma shigewa, yanzu sai ya fara tunanin riƙe su ta yadda ba za su ƙare ba, hakan kuma ba zai taɓa yuwuwa ba sai in ana ƙara yawansu, kenan ya fara tunanin yuwuwar yin wani abu da zai kawo kuɗin shiga.

Mafita ga wanda yake aiki a babban ma'aikatar katako ita ce: Me zai hana shi yin ɗan wani shago ya sami wanda zai riƙa taimaka masa wajen tsarewa? Yanzu rashin aiki ya yi yawa, mutane na zaune ne babu aikin yi, kana fara neman mai taimako nan da nan za ka samu, sai ka koya masa aikin kamar yadda kake so ya yi, ka kawo kayan aiki masu kyau da nagarta, nan da nan za ka ga kana buƙatar sama da mutum guda matuƙar dai ka sami kayan aiki na zamani, ka inganta aikinka kuma ka ƙimanta shi a idonka, kana aiki a wani wuri kana faɗaɗa naka a hankali da abinda kake samu acan, kafin ka kai ga yadda za a ce ba a buƙatarka a wurin aikinka kai kanka ka fara tunanin ya dace a ce ka yi ritaya don ɗaukaka wurinka da habɓaka shi.

A ɗaya hannun kuma matuƙar mutum zai yi wani ɗan wurin sana'a komai ƙanƙantarsa ba zai yuwu a ce shi ne komai ba, misali ka yi wani ɗan kamfani da kake nuƙa zoborodo kana zuba shi a 'yar jaka kamar shayi, ba zai yuwu a ce komai kai kake yinsa kai kaɗai ba, misali a ce kai ne shugaba, masinja, mai gadi, mai fita talla da sauransu, dole ka sami ma'aikata, su ma ka hana su yawon banza kenan, suna samu daga jikinka, wannan ne abinda ya dace, don aikin da ka yi a baya ya ba ka damar da za ka yi naka ne, ba wai kuma in ka gama ka dawo ka tanƙwashe ƙafa sai dai in an yi a ɗiba maka ba, in ka yi haka duk ilimin da ka samo ya zama na banza kenan

Masu bincike na ƙasashen Turai sun gano cewa tsabar kuɗi da za a saka jari duk da cewa shi ne ginshiƙi na habɓaka sana'a ko kasuwanci ba shi ne komai ba, kuɗi na da nasa gudummuwar da yake badawa na masamman amma yawaitar mutane a ɓangarori daban-daban na ma'aikata ko wuraren sana'a ita ce babban sanadi na habɓaka wuri, misali kana da kuɗi kuma ka zuba su a harkokin koyarwa akwai tambayar da za a yi maka wato a wani ɓangare? Kana da buƙatar lafiyayyen gini na zamani da aka cike shi da furanni, ka ƙayata ɗakunan karatu da ofisoshin ma'aikata, ga azuzuwa gyararru da kujeru rantsattsu, 'yan abubuwan sauƙaƙe rayuwa duk ka yi su.

A gefe guda kuma ka samo ingantattun malamai waɗanda suka san abinda suke yi, ka tanadi albashin da za a riƙa ba su su da sauran ma'aikatan dake wurin, ka ga ai ka gama komai, yi ƙoƙari ka gina ɗakin cin abinci da ɗalibai za su riƙa ganin ya fi musu sauƙi da a ce suna dafawa da kansu, a gyara abincin da ake yi ka ɗan sauƙaƙe ƙudinsa, anan ma ka dawo da kuɗaɗensu aljihunka kenan, kuma ka samar wa jama'a da aikin yi, daga gefe kuma ga wani ɗan shagonan ka gina na kasuwanci, anan ne za a riƙa kwafe wa ɗalibai takardunsu, ana sayar da katin waya kuma ga na'urar canjin kuɗi in akwai mai buƙata.

Sannan kuma in kana da dama hatta ɗan shagon da za a riƙa sayen ƙananan kayayyaki duk ka samar a cikin makarantar, ƙarshe dai kuɗin duka aljihunka zai dawo, in ka ga ba za ka iya ba, to gina ɗakunan waɗannan abubuwan ka bayar a matsayin haya ana biyanka kuɗinsu, shi ma ka samar wa wasu da damar kasuwanci kai ma ka sami wata hanyar da za ka ƙara kuɗin shiga, wannan kam dabara ce duk wanda yake da idon kallo, a kowani fanni ka shiga za ka ga muna da waɗannan damammakin amma natsuwa da kai hankali nesa shi yake damummu, ba ma iya tantance abubuwan da muke buƙata, da waɗanda rayukammu suke so, akwai hanyoyin cin nasara da dama ba ma kallonsu, bai yuwuwa ka ce komai kai ɗaya za ka yi.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (17) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (18) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (20) Cikin Sauki

Yi tsari mai kyau, hau kan hanya, duk wata 'yar dama da ka samu janyo wani ku tafi tare, shi zai sami nasa, kai ma za ka daɗa ɗaukaka ba tare da ka yi asarar komai ba, mu dubi filin wasan ƙafa kowa da irin aikin da yake yi, ƙarewa ma an rubuta sunansa a bayan rigarsa da lambarsa dake nuna irin aikin da zai yi da iya hurumin da zai tsaya, haka tsarin mutum a cikin lamarinsa yake, duk aikin da mutane za su yi a ma'aikatanka su ma a ƙarshe manufar dai kenan, a tabbatar ma'aikatar na sarrafa abubuwan da ake buƙata, kuma kayan na karɓuwa ta wurin saye su a duk lokacin da aka yi, wannan kuwa ba tunanin mutum guda ba ne ba aikinsa ne shi kaɗai ba.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user