Tuesday 7 April 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (20) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
HANNU ƊAYA BAYA ƊAUKAR JINKA

Haka Bahaushe yake cewa, alokacin da ka so fara wata sana'a ko aiki naka na kanka ko kasuwanci dole za ka buƙaci mutanen da za su taimaka maka wurin cika burinsu, misali wani tsohon ma'aikacin banki da ya yi wani ƙwarƙwaryan shago, ya ɗora wani makusancinsa don ya tafiyar masa da shi, ya kawo duk abinda ake buƙata masamman na'urannan ta bankin tafi da gidanka, wannan abu ne mai kyau matuƙa tunda makusancinsa yana samu da shi, sai dai duk abinda mutum zai tsara matuƙar zai nemi taimakon wasu to ya tabbatar waɗanda suka dace ne za a saka a wurin.

Neman Taimakon Wasu don yin Nasara..

MarubuciBaban Manar Alkasim

Taimakon na kusa da kai wajibi ne, akwai halin ma da za ka kawo shi kusa don ya riƙa ba ka bayanin duk abubuwan dake faruwa, amma dagewa cewa naka ne kawai za ka sanya a wuri matsala ce babba wace za ta iya ruguza maka shiri, sai in ya cancanta da matsayin, wasu kan yi sha'awar sanya 'yan uwansu makusanta a wuraren sana'a da kasuwanci alhali 'yan uwan ba su cancanci wurin ba, a ƙarshe sai ka ga an ƙare da nadama, kodai ɗan uwan ya aikata ma-sha-a, ko ya yi sama-da-faɗi da dukiyar wasu ko handama da babakere, duka dai munanan abubuwa ne, ko ɗan uwanka yana da takarda ka tabbatar ya zauna a wasu wuraren dake da alaƙa da aikin, ya naƙalci komai, kuma yana da alƙawari.

BIYAYYA

Alƙawari a aiki da tattali da tanadi koyonsa ake yi kamar yadda ake koyon aikin kansa, galibin masu kukan cewa sun ɗauko 'yan uwansu sun cuce su za ka taras ba wata horarwa ta masamman da suka samu kafin su shiga sana'ar, ba su koyi yadda za su yi ta'amuli da dukiyar wani ba ko kaɗan, abinda suka sani kawai yanzu za su shiga kuɗin ɗan uwansu, shi ya sa nan da nan sai ka ga abin Allah-wadai ya faru, a ƙarshe kuma su haramta musu ci gaba da ma'amalla da su har abada, su ce bare ya fi ɗan uwa, alhali su suka yi kuskure tun farko.

DAI-DAI RUWA DAI-DAI ƘURJI

A duk lokacin da ka ce kai da abin hannunka kawai za ka yi harka kana da matsala, amma kimanin shekara uku zuwa huɗu da suka gabata na taɓa ganin wani malami yana bayanin cewa kar mutum ya taɓa karɓar bashi a kan wata sana'a da zai fara, ya ririta abinda ke hannunsa kawai, na ga kuma waɗanda suka yi masa raddi da cewa kashi saba'in da biyar cikin ɗari na waɗanda suka ci nasara ba da dukiyar hannunsu suka yi aiki ba, musamman masu manyan ma'aikatu da masana'antu, to dai duk abinda mutum zai yi kar ya taɓa yarda ya sha ta fi ciki, dole a ci bashi amma wanda za a iya biya ba wahala, kamar wanda za a gyara wuri a ƙara jari da makamantansu.

KULA DA MATAIMAKA

Duk lokacin da mutum yake ganin cewa shi fa zai rayu ko shi kaɗai ne kuma ba ya buƙatar taimakon kowa to akwai matsala babba, amma abu mafi girma a ciki shi ne son kai, wato ya kasance mutum komai shi kaɗai yake so ya kwashe ba ruwansa da kowa, in kana da wurin sana'a kar ka yarda a ce kanka da iyalanka kaɗai ka sani, yi ƙoƙari a ce hatta mai yi maka gadi yana da matsayi a wurinka, kuma kana ba kowa haƙƙinsa yadda ya dace, ko kwana ɗaya mutum ya yi ba ka gan shi ba tambayi inda yake, za a gaya masa cewa ka tambayi halin da yake ciki, in bai da lafiya ne kuma ba za ka iya zuwa duba shi ba saboda wani zarafi yi ƙoƙari ka kira shi a waya, in kana da ɗan wani abin hasafi ka yi masa, in ka matso kusa da ma'aikatanka ba za ka taɓa ganin abinda zai dame ka ba, mutum yana son alkhairi koda kuwa ba yawa.

IN GORA TA CIKA BA TA KARA

Haka Hausawa suke cewa, in ka ga mutum yana ji da kansa kuma yana nuna isa da fankama a wurin sana'arsa to bai shirya aikin sosai ba, matso kusa da ma'aikatanka ka janyo su jiki, komai ku riƙa yi tare, za ka ga duk abinda ya taso sun iya samun ƙarfin gwiwar da za su tuntuɓe ka ko ku tattauna tare, kar ka zama kamar dodo kowa na tsoron ya yi magana da kai, a irin wannan matsayin abubuwa da yawa za su yi ta faruwa ba ka sani ba, yanzu an fara fahimtar amfanin haka, akwai wani mai neman gwamna da mai neman ɗan majalisa da na gani, alla-alla suke yi su ji an yi rasuwa ko taron biki ko suna a duk yankinsu ka gan su a wurin, mafi yawancin tarurrukan da suke halarta ba gayyatarsu ake yi ba, amma suna so ne a gan su a yaba da ƙoƙarinsu a ƙarshe a zaɓe su, ɗan majalisan ya ci, mai neman gwamnan ya fadi, dukansu biyun dai sun dena abubuwan da suka fara, na ce da sun sani su ci gaba, don gabar ta fi baya yawa.

MAGANIN MATSALA

Wasu fa ba su san yadda za su magance matsalolinsu ba samsam, idan mutum ya yi kuskure a wurin aiki sai maigidansa ya yi masa kaca-kaca a gaban jama'a, wani lokacin ma ya kore shi, na ji wanda yake iya bakin ƙoƙarinsa wajen tsare hanyar cin abincinsa, amma da ya yi kuskure ɗaya, haka maigidan ya zazzage shi kuma ya kore shi, ko aure mutum yake yin kuskure wajen gyara shi ko tantama ba na yi zai sami matsala wajen zama da mace, a shekarun baya na yi hira da wani tsoho wanda yake ce min ya yi aure so goma sha biyar, amma mata biyu na san shi da su, na ji matar da aka ce masu zaman haya a gidanta ba sa yin shekara sun gudu, saboda rashin iya ma'amalla, na ga wani mai sana'a duk wanda ya zo koyon aiki wurinsa sai ya gudu, bai iya ma'amalla da su ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (18) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (19) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (21) Cikin Sauki

Na ga malamin jami'an da ya yi hatsari ɗalibansa suke addu'ar Allah ya ƙarisa shi a asibiti, suka ce ina ma ya mutu tun daga wurin hatsarin, na ga wanda wani mutum ya jawo shi don su yi sana'a tare, amma ya munana ma'amallarsa, ya mayar da wurin nasa shi kaɗai, a ƙarshe ya sallami wanda ya kawo shi, ba a jima ba lamarin nasa balbalce, dole mu riƙa kyautata alaƙarmu da masu yi mana aiki ko masu aiki a ƙarƙashimmu ko ɗalibammu matuƙar muna son ganin ci gaba a rayuwarmu.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user