Saturday 25 April 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (21) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
ƘOƘARIN KAWO GYARA

In kana son kawo gyara a ma'aikatarka ko wurin sana'arka na yau da kullum dole ne ka riƙa sanya ido, duk kuma wanda ya yi kuskure a gyara masa, sai dai gyarar kan yuwu ne wajen nuna masa kuskurensa, galibin abinda muke yi shi ne in mutun ya yi kuskure a dinga zaginsa da harshe can sama kowa na ji, ko matarka da ka auro in dai za ka juri ɗaga mata murya za a kai lokacin da za ta shiga ramawa, samun mutum a keɓe cikin natsuwa gyara ne, yi masa kwarwa cikin mutane kuwa kunyatawa ne.

Ka Halarci Duk Wani Wurin Farin Ciki Ko Baƙin Ciki..

MarubuciBaban Manar Alkasim

ƘARFAFA GWIWA DA KALMOMI MASU DAƊI

In har kana da masu aiki a ƙarƙashinka ka zama mai yawan raha a tsakaninsu amma ta wurin yin amfani da kalmomi masu daɗi yadda mataimakanka ba za su damu ba, aƙalla za su ruƙa dariya ne a duk lokacin da ka cakali wani, irin su "Katafila sarkin aiki" ko "Agogo da aiki aka san ku" da dai sauran kalmomi masu daɗi waɗanda suke ƙarfafa gwiwa, to bare kuma in wani sha'ani na gama-gari ya taso kamar Azumi ko Sallah babba ko ƙarama, ka daure a yanka dabba, in babban wuri ne ana samun kuɗi a raba wa ma'aikata ɗanyen nama, in ƙaramin wuri ne a yanka rago a soye shi yadda kowa zai ci ya san ya ci nama, wannan ƙarfafa gwiwa ne, ka yi ƙoƙari ka halarci duk wani taro irin wannan.

TA'AZIYYA BIKI KO SUNA

A matsayinka na babba ka daure ka halarci duk wani wurin farin ciki ko baƙin ciki na ma'aikatanka, kai babba ne, wannan tabbas ba ja, amma duk wani ƙaramin da ya gan ka a wurin wani abu nasa zai ji daɗi sosai ba kaɗan ba, masamman abinda ya shafi baƙin ciki kamar mutuwa, asarar dukiya da sauransu, to bare kuma a ce ka ɗan guntsila wani abu ka miƙa masa, kar ka raina ƙanƙancin abinda za ka yi, ka duba girman tasirinsa ne a zuciyar wanda ka ba wa, nakan ji ana cewa "Alhaji fa ya zo" wani za ka ji ana cewa "Ai ɗabi'arsa ce, lamarin ma'aikatansa nasa ne." In da zai yi tunani duk wahalar da suke sha duk da cewa suna samun abin rufin asiri ƙarshe dai komai wurinsa zai dawo, ba domin gudummuwar da suke badawa ba komai cak zai tsaya.

SANYA GASA A TSAKANIN MA'AIKATA

Ka yi ƙoƙarin sanya wata gasa a tsakanin ma'aikatanka, lura da waɗannan 'yan bokon, duk da cewa muna kallon su marowata ne, amma abinda suke yi yana yin tasiri sosai a zuciyar ma'aikatansu, sukan yi wasu 'yan alluna a ƙarshen shekara su rubuta sunan mutum su ba shi a matsayin wata lambar yabo da take jinjina masa a kasancewarsa wanda ya fi kowa zuwa da wuri, ko rashin fashi, ko tsafta, ko ladabi da biyayya, ko aiki tuƙuru da sauransu, irin waɗannan kyaututtuka suna da tasiri ba ƙarami ba a zukatan ma'aikata, kowa zai yi ta hanƙoron a ce ya samu, ba kuma zai samu ɗin ba sai ya aikatu, da haka sai aiki ya bunƙasa, to bare a ce ana saya wa mutane motoci da mashina ko talabijin da wayoyin hannu da sauransu.

Wanda bai samu kyauta ba bai dage ba kenan, in babban kamfani ne ko saudiya sai a kai wani, duk da cewa mutum ɗaya ya samu, amma zai zaburar da sauran ma'aikatan idan suka ji cewa dagewarsa ce da jajurcewa silar samun kujerarsa, in ƙaramar ma'aikata ce za a iya saya wa talaka ƙaramin buhu na shinkafa, ko galan ɗin manja ko na man-gyaɗa, ko dai wani abinda zai jawo hankalinsa, wannan ya fi masa wata lambar yabo, da yawammu ba mu san ƙimarta ba, ba mu cika wani lura da cewa nan da nan za mu murtsuke ci ya ƙare kenan ba.

ƊORA WA MUTANE NAUYI

Ita kuma wata ɗabi'a ce mummuna da ta zama dole mutum ya guje ta a matsayin shugaba ko abokin aiki, za ka taras wani kullum cikin hanzari ne "Don Allah wane ɗan riƙe min wuri kaza ina son na yi kaza" ko ka ji yana cewa "Don Allah yau ba zan sami damar zuwa ba amma wane ɗan kama min kaza" in hakan ya fara yawa ko ka nema ba mai kula ka, za ka taras duk wanda ka kama yana zillewa saboda an maimaita ba ɗaya ba ba biyu ba, ko shugaba ne ya yawaita ɗora wa ma'aikatansu wasu ayyuka a wajen abubuwan da suka san sun zama musu dole tabbas za ka taras sun noƙe, ko in suka ji motsinsa kowa ya kama gabansa, ba laifi ya faru sau ɗaya ko biyu amma ba a haɗe ba kuma kar ya yi tsawo, in ka ɗora wa mutane aiki to yagar musu wahalar aikinsu ka matsa su karɓa koda sun ƙi, shi ne zai ba ka garantin ka nema wata rana.

Idan kuma ka shugabanci wani ɓangare na jama'a a cikin ma'akata, taka ce ko aiki aka ba ka, ka yi ƙoƙari wurin tabbatar da an yi aikin cikin nishaɗi, a maimakon ka zaɓo wanda ka raina ka labta masa kaya ka jira ya yi shi kaɗai, yi ƙoƙari ka kira taro, koda ka san yadda za a yi ka ɗan dakata, ka fito da aikin sarari, ka nemi shawarar abokan aikin naka kan yadda za a tafiyar da shi, a maimakon mutum guda ya yi shi kaɗai, wanda hakan kuma zai ɗauke shi wani ɗan lokaci, ka yi ƙoƙari ka kasa musu yadda kowa zai yi da kyau, kuma cikin nishaɗi sannan a ɗan ƙanƙanin lokaci, buƙata ta biya kenan, sannan shugaba ya riƙa samun lokaci yana zaunawa da ma'aikatansa yana tattaunawa da su.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (19) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (20) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (22) Cikin Sauki

Abinda ya fi komai mahimmanci ma ya riƙa shiga cikin aikin, in zai yuwu kar ya bari a sami wani ɓangare na kamfanin wanda ba ya shiga a yi da shi ko a ce bai san kansa ba, wannan sifar shugaba na ƙwarai kenan wanda tabbas nasarar yake nema kuma aiki yake yi tuƙuru don isa gare ta, ba wai mutum ya yi ofishi a gefe sai dai a riƙa kawo masa takardu yana cikewa ko tattaunawa da abokan ciniki ba, na yi karantarwa a wata makaranta wacce hedimastan lokaci-lokaci yakan hutar da wani malami shi zai koyar don ya ga fahimtar 'yan ajin da duk inda suka tsaya a karatunsu, ɗan lokaci kaɗan za ka gan shi a ƙofar tagarka yana kallon abinda kake yi wa ɗaliban, in ya ga kuskure za ka ji kira a ofis, ya gyara maka cikin tsanaki.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user