Friday 15 May 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (22) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
ME YA DACE?

Kowa da ka gani yana da abinda yake damunsa, kuma abu ne sananne ba zai taɓa yuwuwa a ce mutum ya ɓoye duk abinda yake damunsa ba, ko bakinsa bai faɗa ba wani lokaci fuskarsa za ta bayyana, mukan ɓoye amincewarmu ta bayyana kamar yadda take hankatso damuwarmu, amma wani sa'in dole sai mutum ya yi ƙoƙarin shawo kan zuciyarsa da abinda yake damunsa, don kar harshensa ya riƙa kuɓucewa ya ɗebo masa aikin da bai shirya masa ba, na ga wani mutum da abokan kasuwancinsa suke gudunsa a dalilin abubuwan da suke damunsa, ba wai faɗa yake yi da mutane ba ko zage-zage kamar mahaukaci, a'a.

Duk wanda ka kalla yana da fuskar da yake kallon matsalolinsa..

MarubuciBaban Manar Alkasim

Da ka ɗan zauna da shi na wasu 'yan daƙiƙoƙi zai fara faɗo maka matsalolinsa, wallahi ban da lafiya, duk kuɗina na kashe su a magani, wurin aikina kaza-kaza, 'yan uwana duk masu kuɗi ne ba sa taimaka min, na yi asarar kaza da kaza, kuɗi duk in na samu sai su watse a banza, wane ne ya yi min baki, mahaifana kaza da kaza, mutane sun riga sun saba da shi, ba wani abu yake nema a wurinsu ba kuma ba wani abu za su ba shi ba, amma ba sa son jin irin waɗannan koke-koken marasa kan gado, da wahala ka ji mutum yana yi wa kansa fata na gari, a kowani lokaci sai yi wa kansa mummunan fata yake.

Wani kuwa iya abinda zai iya gaya maka shi ne "Alhamdu-lillahi" wani ya ce maka "Harkar ce sai godiyar Allah!" Ko zai ƙara maka wani abu sai dai ka ji ya ce "Abubuwa duk sun tsaitsaya amma in sha Allah komai zai gyaru, akwai alamun alkhairi nan kusa ba da jimawa ba" haka zai fara kallo wasu hanyoyi da za abi a fita, ya fara tunanin kawo sauyi a harkar, ko dai ya canja wurin zama, ko ya sauya kayan ko dai ya ƙawata ta ta wurin shigo da sabbin tsare-tsare, irin waɗannan ba su cika dauwama a halin ni-'ya-su ba, don ba su yarda da cewa akwai abinda bai da mafita ba, ba su yarda da cewa lamarinsu yana hannun wani dan-adam ne ba bare ya takura su, rayuwa kullum a birgimar hankaka take, wata rana ka ga fari wata rana ka ga baƙi.

Duk lokacin da mutum ya yi karo da wani abu mai kyau ya san cewa ba abinda yake dauwamamme, wata rana zai ga abinda ba shi yake so ba, sai ya yi masa shirin ko-ta-kwana, in zai zo ɗin ma yakan zo masa da sauƙi, wanda yake ganin cewa wani zai iya yi masa wani abu to duk lokacin da mummunan abu ya same shi zai ce wannan mutumin ne, a maimakon ya fara tunanin cewa jarabawa ce wace hanya zai bi ya cinye ta sai ya fara tunanin wane ne ya yi masa kaza dole ya rama, kuma  ya ce "Shikenan ya gama da ni sai dai Allah ya isa kawai" ko ya ce za a yi musu hisabi a ranar ƙiyama, batun neman mafita kuma ya ƙare.

YA ZA KA KALLI MATSALOLINKA?

Duk wanda ka kalla yana da fuskar da yake kallon matsalolinsa, yana da hanyar da yake tunani ta daban, wani za ka taras addini ya yi masa tasiri, duk abinda ya same shi ko yake son yi zai kawo Allah a matakin farko, irin waɗannan ba su cika rigima da mutane a kan abu ƙarami ba, cikin sauƙi za su warware babbar matsala su ce maka "Ba komai, haka Allah ya so" su ma ɗin akwai ɓangaren da sukan yi kuskure, abinda ya kamata su ɗauki mataki don kare faruwar abin a gaba ga shi sun bar shi ya wuce sakaka, wasu kuma ba sa son ka kawo musu Allah a duk lamarin da ya shafi sana'arsu, a tunaninsu maganar Allah a addini kawai ake samunta ba ta haɗa hanya da kasuwanci ba, in mutum ya yi dai-dai ya ga dai-dai in ya yi kuskure ya taɓa ya ji, da yawa waɗannan ba sa cin nasara a rayuwa.

Haka za ka sami kowa da fannin da yake tunaninsa, to kai abinda ya kamace ka shi ne ka kalli mutum da sifar da ta dace, ka kalli hanyar da yake tunani, ka kalli wayewarsa da iliminsa, ka kalli komai nasa, mace ce ko namiji, yaro ne ko babba, ya matattararsu take? Bai yuwuwa kai da aka haife ka a Kano ka tashi a cikin Hausawa, ƙila ma mahaifinka ne limamin masallacinku, ka sami wannan tarbiyyar, ka ce abokin sana'arka ko mai maka aiki da ya taso a Kudancin Kaduna ba ma musulmi ba ne kana son ya yi maka irin ma'amallar da kai ka taso a ciki, kuma kana da tabbacin ba wahayi za a yi masa ba, za ku yi ta samun saɓani ne, in maigidanka ne ƙila ka rabu da shi, in ɗan gidanka ne ƙila ka kore shi.

Ba yadda za a yi mutum ya riƙa kallon kansa wurin yanke hukunci a kan wasu, ba dole ba ne a sami fahimta iri guda, amma kallon mutum a ɗabi'arsa zai taimaka, wata abokiyar aikina, daga kudancin Kaduna, ba a yi wata ba take gaya min irin wahalar da ta sha da mahaifiyarta, ina son na ba ta haƙuri ta ɗibo ashar ta haɗo da mahaliccin gaba ɗaya sai da na girgiza a lokacin, ba arziƙi na yi ƙoƙarin kulle hirar gaba ɗaya, ita da kanta ta fahimci ban ji daɗin maganar ba sai ta fara ƙoƙarin gyarawa, na tabbata in ba suɓutar baki ba ba za ta ƙara irin wannan a gabana ba, hanzarin da na yi mata ita ba musulma ce ba, ba ta da ƙawaici irin namu na Hausawa, ba ta da tarbiyyar girmama uwaye, shi kansa Allan ma ba su bi hanyar da za su kaɗaita shi ba bare su ba shi sauran sifofinsa da ya keɓantu da su.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (19) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (20) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (21) Cikin Sauki

To bayan wannan ma a matattarar da muke ma, ko ciki guda ne akwai abinda ake kira Keɓantattun Halaye ga Kowa, wato "Individual Deferences" a Turance, ko "Fruuq Fardiyya" a Larabce, irin waɗannan halaye ko ciki ɗaya yara suka fito, wato 'yan biyu za ka taras kowa da ɗabi'unsa, in haka ne kuwa dole sai mun riƙa yi wa juna hanzari, in mutum ya kwabsa maka a matsayinka na shugaba ka kalli sauran ayyukan da yake yi kawai ka yi masa rangwame, in kuma kai ne yaron gida to ka yi masa hanzari, ka gane irin halin wadatar da yake ciki da matsayinsa, wanda in kai ne ba za ka yi haka ba, shikenan ya wuce sai a kalli gaba kuma.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user