Thursday 14 May 2020

Kalli Jirgin Ruwan Da Yafi Kowanne Dadewa A Duniya Fiye Da Shekaru Dubu 8

Tura Wannan Zuwa
Wannan shine Kwalekwalen da ake ce ma shi "Dufuna Canoe" shine Kwalekwale na biyu ma fi tsufa da ya ragu a tarihin duniya. Masana sun yi amfani da kayan duban tarihi suka gano cewa wannan Kwalekwale ya kai shekara 6500 kafin haihuwar Annabi Isa (A.S) sama da shekara 7000 kafin haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W) kuma kusan shekaru 8000 kenan yanzu a duniya.

Dufuna Canoe

Marubuci:- Sheriff Almuhajir

An samo wannan Kwalekwale ne a ƙauyen Dufuna da yake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Fune da ke Jihar Yobe. Tunda akwai mutane a wannan yanki na mu na Yobe har suna da ilimin da za su yi ƙere-ƙere na kimiyya, ya nuna cewa al-ummah ce kenan.

Yanzu abunda na ke tambaya shine; bisa ga wahayi Allah yace babu wata al-ummah da ba'a aiko mata Manzo ba, shin hakan yana nufin cewa akwai Manzo da aka yi cikin al-ummar jihar Yobe kenan shekara kusan dubu bakwai kafin haihuwar Annabi Muhammad (S.A.W).

Allah dai ya barwa kan shi Sani, domin amsa wannan tambaya zai yi wuya. Amma wannan yana sake nuna yalwa da kamalar Allah mahalicci.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user