Thursday 14 May 2020

Duniyar Yaudara A Soyayya Da Yadda Take

Tura Wannan Zuwa
Wata mata da mijinta sun ziyarci gidan zoo, sai matan taga biri yanata wasa da matarsa. Abun yayi matuƙar burgeta sai tace ma mijinta, kai kalli soyayya irin wannan rayuwa cike take da jin daɗi da dacewa.


Duniyar Yaudara

Marubuciya:- Aisha Isah

Lokacin da sukayi gaba zuwa ɓangaren zakoki kuwa, sai taga namijin zaki ya kwanta nesa da matarshi yayi shuru sai tace "Kai wannan labarin soyayya ce me baƙanta zuciya, wannan kalan soyayyan takan kawo gajiya cike take da damuwoyi."

Sai mijinta ya kalleta yace, karɓi wannan kwalban a hannuna ki jefi matar zaki da'ita lokacin data jefa sai zakin ya zabura ya miƙe yayi ihu yana neman wacce ta taɓa masa matarsa don ɗaukan fansa.

Sai yabata wani dutse yace muje ki jefawa matar biri, saiko suka tafi tana jefawa matar, birin yaruga aguje yana neman maɓoya kada shima abin yazo kansa.

Sai mijinta yace mata kingani, kada ki ruɗu da abinda mutane suke nunawa agabanki, karma ki yaudari zuciyarki akan haka.

Akwai mutane da suke yaudarar mutane da yanayi na ƙarya.

Kuma akwai mutane da suke ɓoye tsananin so dasuke maka acikin zuciya, alhalin zuciyar cike take da so da ƙaunarka.

Muna duniyar yaudara ne, Allah (S.W.) yakare Mu Amin.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user