Monday 16 March 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (18) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
RASHIN GIRMAN KAI

Na isa wata ƙasa a 2002 inda na kammala digirorina a 2015, idan muka lura da cewa na ɗan jima a can, kuma ko tun farko karatun ne dai ya kai ni, sannan a matakin digiri wanda ko kafin na tafi ina da diploma kuma na ɗan jima ina koyarwa waɗannan abubuwa za su iya ba ni damar da zan ɗan lura da wasu abubuwa waɗanda sun ɗan saɓa wa yadda na saba gani a ƙasata, ba ina cewa sun fi mu hikima ne da jajurcewa ba, amma akwai wasu abubuwan da in an koya za a iya magance zaman banza, bambaɗanci, ubangidanci, neman alfarma da ƙarfa-ƙarfa, a can ne na ga wanda yake aiki a gidan jarida da majalla ta ƙasa da rana, in dare ya yi ya koma wata jami'a a matsayin mai-kula da yara yana kwana da su, yana ɗan samun na cefane.

Zai yi wahala mutumin da ya yi kansila a same shi ya koma ajinsa na furamare 

MarubuciBaban Manar Alkasim

Na ga soja a matsayin major kuma malami ne a wata jami'a, na shiga ajinda yake koyar da addinin kiristanci, tsakanina da Allah bayan na gabatar da wata ƙasida sai da ya nuna min cewa ban san komai a ƙasata ba, ni kaina na yarda da hakan, musamman irin hujjojin da ya bayar, na ji labarin wani babban sojan sama da yake koyar da konfuta a wata jami'ar, ni da kaina na taɓa ganinsa a cikin kaki ina ta mamaki, na ga wasu masu dafa abinci a wata jami'a ashe 'yan sanda ne, suna aikin ne idan sun cire kaki don su ƙara ƙarfin abinda suke samu a wata.

A lokacin da muke ɗalibai na ga wani ministan ilimi wanda shi ne shugaban tsangaya ta ilimi a wata jami'ar, akwai wani ɗan sanda da muka san shi, sai ga shi yana kamisho, ban sani ba in wannan yana da alaƙa da tsaro ko baida shi, ina kuma da masaniyar cewa ƙasata ba ta ba da hurumin da ma'aikacin gwamnati zai yi aiki biyu ba, amma kuma ba a hanaka ka nemi na rufin asiri a wani wurin ba, babban abinda yake ba ni sha'awa da su shi ne babban aikin da kake yi ba zai hana su su yi wani da ake ganin ƙasƙantacce ne ba, tabbas akwai masu yin haka anan amma ba su ne suka fi yawa ba.

Zai yi wahala mutumin da ya yi kansila a same shi ya koma ajinsa na furamare kamar yadda yake da, to bare kuma wanda ya hau matsayin shugaban ƙaramar hukuma, da ya koma aikinsa na baya ya gwammace ya riƙa bin 'yan uwansa 'yan siyasa su ba shi ko su hana, matsalar da muke fama da ita kenan, na ga kansiloli a baya da suka riƙa sayen filaye da gina gidaje suna wadaƙa da kuɗi yadda suke so, abin takaici ba sa iya aiki da damar da suka samu ta wurin gina ƙaramin kamfani ko wata ma'aikata ko shagon kayayyaki yadda in suka sauka za su koma can don rufin asiri, da sun sauka da ɗan ƙaramin lokaci sai ka ga sun lashe abinda suka tara.

Waɗanda suka sayi filaye, motoci da sauransu in ba sa'a aka yi ba nan da nan za su kaɗar da su su bi kan kuɗin su lashe, da a ce kansilanmu malamin makaranta ne, lokacin da ya sami kuɗinnan kamar ana zubo su da bakin ƙwarya sai ya sayi wani fili ya gina makaranta tunda ya san kan abinnan, yana sauka ya ƙara faɗaɗa ta ya sami hanyar da zai riƙe rayuwarsa ya ɗauki wasu ma aiki, yau a ce mutum tela ne aka ciro shi aka naɗa shugaban ƙaramar hukuma, da sai ya yi kamfacecen shagon teloli, ya zuba kekunan da ba ko'ina ake samunsu ba, ya ɗibi ma'aikata, sannan ya yi ofis ɗinsa na masamman saboda ko-ta-kwana, yana sauka ya san inda zai je.

Hana ƙarya na ga wani kansila wanda tun asali shi manomi ne, ɗan abinda yake samu a gwamnatance ya riƙa ƙara shi cikin abinda yake birnewa a ƙasa, ya ƙara zama babban manomi, koda ya sauka ba wani abu nasa da ya canja, don ko tun yana kai yakan ɗibi 'yan ƙwadago su shiga daji, nan ma ya taimaki wasu, duk da cewa rayuwa ta ɗan sauya da ya sauka ɗin, amma bai wani shiga halin ni-'ya-su ba, wani tela da na sani ya sami aiki babba, kuma yana samun kuɗi ba shakka, a maimakon ya ƙawata sana'arsa ta farko ya haɓaka ta bai yi ba, a ƙarshe damar da yake da ita ta kuɓuce masa, har muka rabu shagonso ba a daina murza zare a cinya ba, bayan na ga wasu suna amfani da wani ɗan inji ƙarami.

Matuƙar babban matsayin da ka samu a yau na ɗan wani taƙaitaccen lokaci ne da yatsun hannunka za su iya ƙirgawa, me zai hana ka yi wani shiri da za ka daɗe kana jansa bayan saukarka ko bayan gushewar wannan damar? In ka yi hakan aikin da ka samu zai daɗa taimakonka ne zuwa ga nasarar da kake sa rai da ci a rayuwarka, tabbas wasu suna da tsari, sukan waiwayi halin da suke ciki kafin su sami kansu a irin wannan halin na yau, sukan yi tunanin cewa in fa suka sauka za su iya komawa gidan jiya, sai su yi wa kansu tsari.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (15) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (16) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (17) Cikin Sauki

In a baya mutum ya karanci likitanci ne amma bai fara aiki ba saboda halin da ake ciki na ƙarancin gurabun aikin, sai Allah ya tarfa wa garinsa nono ya sami wani muƙaddashin ƙaramar hukuma na riƙo,  me zai hana ya ririta ɗan kuɗin da yake samu wurin gina ƙaramin asibiti, ya riƙa kawo kayan da ake buƙata a hankali yadda kafin ya sauka ya gama tanadar duk abubuwan da ake buƙata? Da farko dai in ya sauka zai ci gaba da aikin da ya karanto a wurin da shi ne shugaba, sannan kuma zai samar wa bayin Allah da aikin yi, ga riba ga lada.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: