Thursday 20 February 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (15) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa Ga
KYAUTATA ZATO KO MUNANAWA

Ni fa ina ganin kamar kyautata zato ko munana shi ba halittaccen abu ne a cikin jikimmu ba, gaskiya sabo ne ko yanayin da mutum kan ɗauka daga tarbiyyar da ya samu, kodai ta gida ko ta matattara ko makaranta, wannan ko shakka babu in aka matsa wa mutum yakan canja a hankali, sai ka ga in yana son faɗin abu sai ya fara kawo togaciya tukun ya ce "Koda yake ni ana cewa na faye kaza da kaza" a hankali sai irin wannan munana zaton ya fita daga cikin ɗabi'unsa, wani kuma yakan kyautata sakamakon abubuwa amma zama da wasu mutane da lura da yadda abubuwan suke cancanjawa dole ya sauya tunani.

Hanyoyin samun nasara a rayuwa

MarubuciBaban Manar Alkasim

Kyautata zato shi ne duk abinda aka ce za a yi sai mutum nan da nan ya yi zaton cewa in sha Allahu sakamakon abin zai zama alkhairi, ba wai yakan ƙi kallon matsalolin dake ciki ba ne, a'a, yana masa kallon cewa ne ba a riga an fara shi ba, bare a yi masa tunanin cewa wani abu mummuna zai shafe shi, anan kamata ya yi a kalli ɓangaren kyawun abin sai in an hango wata matsala daganan sai a tsaya a sake lissafi, misali mutum ne ya ce yana sha'awar shiga soja, a zahiri masu buƙatarsa a aikin suna yawa, shi kansa yana da hidundumu a gabansa, 'yan uwansa, garinsa, addininsa, ƙasarsa da sauransu, wannan ya kamata a fara dubawa sai in an hango wata matsala.

Wani ne ya kammala jami'a ya ce yana sha'awar noman citta, zaton alkhairi da ya yi wa noman ya ƙarfafa masa gwiwa, sana'ar citta na cikin abubuwan da ake ce musu gwari, waɗanda suke ɗaga mutum can ƙololuwa, in bai yi sa'a ba su kauce su bar shi ya sha ƙasa, ya fara noman, ya sayar da abinda ya noma, har ma ya saya a wurin wasu ya sayar, ganin ribar da ya samu sai ya koma sarinta a wurin wasu yana sayarwa, kasuwar ta buɗa masa, ya canja sana'a, yau yana cikin matsakaitan da ake ganin ba su da tunanin matsalolin yau da gobe, da ya kalli yuwuwar faɗuwarta da bai fara ba, kuma tana faduwar.

Munana zato shi ne duk abinda za a kawo da wahala ka ga mutum ya yi zaton cewa sakamakonsa mai kyau ne, duk abinda aka kawo muninsa yake fara gani kafin kyawunsa, in ya yi magana sai ka ga ya karya wa mutane gwiwa, su yarda cewa abin ba zai yi kyau ba su bari, irin wannan yake damun matasa da dama, hakan kan kurɗaɗa ɓangarori daban-daban na rayuwa, misali mutum ne ya ce zai yi aure, kafin ya fara nema har wani ya ce "Kai! Kana hauka ne? Ba ka da gida ba wata ƙwaƙƙwarar sana'a ba aikin gwamnati ka ce za ka yi aure?" Akwai ma wasu 'yan boko da na ji suna zagin ƙaninsu wai da kwalin digiri ne zai ce zai yi aure?

Suka fara jero masa: "Yanzu za ka sha wahala wajen haɗa kayan auren, da ka gama a yi maganar ɗakin da za ku zauna, shi ma haya, wata ƙila ma kuna cikin zamanku maigidan ya ce zai yi amfani da gidansa ku tashi, ko ya ce zai ƙara tsara fasalin gidan, shekara ɗaya tal matarka ta haihu ga hidimar suna ga nata na haihuwa, komai ya ƙaru maka kenan, ƙila kafin ta yaye ka sake yi mata wani cikin, nan da nan a ce na farkon zai shiga makaranta, wata cacar kuɗin ta kunno kai kenan" ka ji fa! Daga shawarar zai yi aure har an yi masa lissafin shekara huɗu don dai a karya masa ƙwarin gwiwa, in ya biye tasu shikenan an gama.

Kwatankwacin waɗannan mutanen guda biyu wato mai kyautata zato da mai munanawan kamar ka sami ruwa ne rabin kwalba ka tambaye su, mai kyautata zaton zai ce maka "Akwai ruwa a rabin kwalban" mai munanawan zai ce "Rabin kwalban ba komai" kowa da fuskar da yake kallo, lokacin da ka yi niyyar yin wani abin alkhairi a rayuwarka dole ka haɗu da irin waɗannan mutanen guda biyu, gaskiya ba muganci ne ko ƙeta ko rashin sonka da arziƙi zai sa su yi maka mummunan zato a kan abinda kake son yi ba, asali wasu mutanen haka suke, duk in za a yi abu ba sa iya kallon ɓangaren alkhairi, sai dai su kalli ɗaya ɓangaren kuma su tsaya a kansa.

Na ji wanda ya zo neman aure wani gida, sai ɗaya daga cikin uwayen ya fara cewa "To idan kuma wani mummunan abu ya faru da wa za mu yi kuka?" Ba a yi auren ba, ba kuma suna faɗa da juna ne ba, tsabar munana zato har an fara maganar za a yi saki da ƙoƙarin tunano abinda za a yi in an yi sakin, wani ne ya ce zai yi shago, wani na zuwa ya fara cewa yanzu in aka yi gobara ta ina za a fitar da kayan? Sannan in ɓarawo ya zo cikin dare ya nemi yin kisa ya za a nemi masu taimako? Sai kuma ya ƙare da cewa biyan kuɗin haya kansa matsala ne, duk dai maganganun ba na yabo.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (13) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (14) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (16) Cikin Sauki

In ka ci karo da masu mummunan tunanin ka riƙa fassara shi da alkhairi nan take, hakan zai sa su ji a jikinsu su canja, na ji wani yana tambayar abokinsa game da wata ƙatuwar rukoda da take ɗakinsa, ya ce "Ina ka kai ƙatuwar rukodannan taka?" Sai ya ce "Ta yi abinda kake so" da buɗe bakinsa sai ya ce "Ta lalace?" Ba burinsa kenan ta lalace ba, amma fassarar da ya yi wa maganar kenan, ya munana mata zato, in kana son fara sana'a ko faɗaɗata ka ji masu munana zato kar ka damu sosai, yi maza ka yi mata fassara mai kyau kawai ka nemi yardar Allah (S.W.T).

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user