Saturday 15 February 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (14) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
GAMUWAR ILIMI DA BURI

Abinda mafi yawan mutane suka sani game da ilimi ko jahilci shi ne: Mai ilimi mutum ne da ya bi tsarin karatun boko a rubuce sannan ya ɗan haɗa da turancinnan, in aka sami mutum bai bi wannan tsarin ba to jahili ne, bambancimmu da ƙasa mai tsarki kenan, a 'yan shekarun baya an yi wasu shahararrun malaman muslunci, sun koyar da ɗaliban jami'un ƙasar alhali ba su taɓa wuce makarantun sakandare ba, tunda har waɗanda suka bi tsarin karatun daga Furamare har gaba da digiri suna ɗaukar karatu a wurinsu, dole sai an yi wa ma'anar jahilcin gadon bawul.

Nemi Ilimi ko a Birnin Sin (China) Ne..

MarubuciBaban Manar Alkasim

Iya rubutu da karatu, ko bin tsarin boko ba shi ne kaɗai ilimi ba, a neme ka a kan abu kuma a same ka da shi shi ne manufa, duk ilimin da mutum yake da shi na kasuwanci, in zai koyar da duniyannan gaba ɗayanta amma ya kasa aiki da ilimin wurin zama babban ɗan kasuwa haƙiƙa babu alamar sifantuwa da ilimin, komai daƙiƙancin mutum ko rashin shiga makarantar boko in ya san yadda zai juya kuɗi, ya yi babban shago maƙare da kaya ya sami ma'aikata, wannan ya fi ƙarfin jahili.

Duk mutumin da zai shata gona, ya ɗibi ma'aikata ya yi lissafin kuɗin taki da na ma'aikata ya yi bankaɗeɗiyar gona, in amfani ya zo gidansa ya gyara ya sayar ya ci riba ya sake shiri don gobe wannan ya fi ƙarfin a kira shi jahili, ilimi da buri a haɗe suke ba sa rabuwa, da yawan waɗanda suke karanta ilimin injiniyanci don su zama injiniyoyi ne, haka ma wanda yake koyon kanikanci duk ƙoƙarinsa a ce yau ya zama bakanike, ma'ana dukansu ɗalibai ne, wanda ya iya isa inda yake so ya ci nasara kenan a rayuwarsa, a taƙaice dai babu jahili kamar wanda yake ganin ya yi ilimin amma bai san yadda zai yi aiki da shi ba.

Yanzu dai komai iliminka da ƙwaƙwalwarka kana buƙatar zama kusa da masu ilimi waɗanda za su taimake ka kan lamura, wannan ya sa za ka ga wani kamfani babba wanda bai da alaƙa da shari'a amma yana da mai ba da shawara ta fuskar doka da oda, wannan aikinsa kenan nuna wa kamfanin fuskar da zai bi don guje wa aukawa cikin wata matsala, idan wanda bai yi karatu ba yana da masu fuskantar da shi sai ya yi abin mamakin da wani mutumin da ya yi nisa a bokon bai yi ba, kawai abinda kowani irin mutum yake buƙata, daga kowani irin rukuni yake kuwa, shi ne: Me yake buri, yazai isa gare shi?

FUSKANTAR MATSALOLI

Akwai wasu matsaloli a rayuwarmu waɗanda duk yadda muka yi ba za mu iya kauce musu ba, wani sa'in ba ilimi ne kaɗai magani ba anan, abin kan faru ba mu san da shi ba shi, tabbas wasummu suna fama da matsaloli masu baƙanta rai, masu raɗaɗi a zuciya, ka ga mutum koyaushe cikin damuwa da ƙunci ka rasa me yake damunsa, wani ma takan kai ga hakan ya yi tasiri a cikin al'amuransa yadda ɗan abu kaɗan sai ka ga ya ɗauke shi sama da yadda ake buƙata, yana da kyau mu fahimci cewa wannan cuta ne dake buƙatar magani.

Kasa a Ranka Zaka Iya Cimma Burin Ka.. 

Koda yake hakan kan faru ne daga wani abu da aka yi wa mutum, in ya zamo bai yin shawara da kowa sai abin ya yi ta cinsa a rai har ya kai ga wannan halin, wani kuwa tsabar zato ne cewa in har wannan abin ya tabbata to shi fa ya shiga uku, daganan ya sa abin a zuciya har ta kai shi ga aika-aika a kan sana'arsa ko lamarin rayuwarsa, a ƙarshe da wahala nasarar ta samu masa kamar yadda yake zato, ka dubi mata dai yadda suke ɗaukar kishi da kishiya, sam ba sa zaton alkhairi ga kishiyar, sai su fara wasu ayuyyukai da maganganu, hakan ta kai ga amaryar daganan ita ma ta fara shirin yadda za ta fuskanci uwargidanta.

In ta shigo ba za ta gasgata fara'a da haba-habar da za ta gani ba sai ta ɗan sami lokaci ta tabbatar gaskiya ne ba shigo-shigo ba ne, ɗan lokacin da za ta ɗauka kafin ta saki jiki in ba a kai hankali nesa ba sai ka ga uwargidan ta yanke ƙauna, ta ce ta yi kaza da kaza amma ga abinda amaryar take yi mata, in shaiɗanun mutane ko ragon namiji ya shiga tsakiya shikenan lamarin ya gama ragargajewa gaba da baya, babban abinda ya jawo hakan tsoro da hukunci kan abinda baka tabbatar ba.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (12) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (13) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (15) Cikin Sauki

Zai yuwu a sami hakan in kana da shagon sayar da takalma ka ji wani shi ma zai yi a kusa da kai, sai ka yi tsammanin cewa kai kuma taka ta ƙare kenan za a koma wurinsa, daga lokacin ka rasa kasuwa kenan, ko kana da burin gina gidan buredi sai aka ce akwai kusan gidaje guda uku, ba ka duba yawan maciyan ba da yawan buƙatunsu sai ka duba gidajen buredin kawai, wannan 'yar matsalar da samu in ba a yi sa'a ba shikenan komai ya tsaya ƙila ma daga lokacin ba wani abin da za ka yi tunanin yi an riga an gula maka kissafi, bayan ga lissafe-lissafennan barkatai.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode



TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user