Sunday 2 February 2020

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (12) Cikin Sauki

Tura Wannan Zuwa
KARATU FA DOLE NE

Ko ni nakan faɗi haka, amma kuma wanne? Karatun Addini ko na Boko? Ga wanda ya san akwai bambanci kenan, ni a iya sanina ba ilimin da addini bai zo da shi ba sai dai in ba shi da mahimmanci ko amfani ga ɗan adam, ilimin rayuwannan da kake gani shi ne mafi mahimmanci a wurin kowa don haka dole ka yi shi in kana son cin nasara a rayuwarka, za ka taras wani ya yi Furamare ne ya tsaya, tsakani da Allah ba za ka haɗa shi da wanda bai taɓa taka makaranta ba, wani ya yi Sakandare ne ya ce "Nan zan tsaya".

Ka Tashi Ka Nemi Ilimi koda a Birnin Sin Ne.. 

MarubuciBaban Manar Alkasim

To irin wannan da ya tsaya a Sakandare ba za ka taɓa tunani a zuciyarka zai iya zama malamin jami'a ba, ko malamin Sakandaren da ya yi ba zai zama ba sai in ya dawo ya ci gaba da karatu zuwa gaba da Sakandaren, haka mutumin da a rayuwarsa matuƙin mota ne da ya koya a tasha ya iya, ya kwashe kimanin shekara 25 yana tuƙi rana ɗaya ba zai ce kai na gaji yanzu jirgin sama zan koma tuƙi ba, iliminsa bai kai nan ba, komai gwanancewar mutum a tuƙin keke rana guda ba zai hau babur ya tuƙa ba sai in ya koyi yadda ake yi a karance ko a aikace.

Kamar bakanike ne, don mutum ya yi shekaru yana gyaran keke ba zai ce yau na koma gyaran mota don dukansu biyu hawansu ake yi ba, kamar yadda ka san ni da kai shekarummu guda ni ina da mata biyu kai ba ka taɓa aure ba ba za ka ce masaniyarmu da mace guda ne ba, shi karatu komai kasawarsa dole sai an yi shi, in ba ka taɓa aure ba tashi guda aka ba ka mata biyu, ni kuwa na taɓa zama da su a lokaci guda matsalar rayuwa ta sa na rabu da ɗaya ko dukansu biyu dole yadda zan tafiyar da sabbin matan ya bambanta da yadda za ka yi, ba komai ne ba sai karatun da na yi a baya, sau da yawa kallon baya kan taimaka wa mutum ya san yadda zai tafiyar da gaba.

Amma fa gaba daban baya daban, mai son cin nasara a rayuwarsa kar ya taɓa raina ilimi don koya yake, a lokacin da mutum ya yi Furamare ya ce daganan na gaji kenan abokan karatunsa za su wuce gaba, Qur'ani kuma ya tambayemu a sifar ƙalu-bale ya ce: "Shin masana da marasa sani za su yi dai-dai?!" Ya ce "Ko a kwatance ba dai-dai suke ba" duk wanda ya wuce ka har abada ya sha gabanka, sai dai ka fi shi a wani abin ko ka dawo ka shiga gabansa, yadda ka san jahilan masu kuɗi ba su sha'awar su zama talakawan masu ilimi, haka talakan malami bai da burin zama jahilin mai kuɗi.

Kowa buri yake ya haɗa biyu, ga kuɗi ga ilimi, hakan kuma ba zai haɗu ba sai da karatu, duk ɗan kasuwan da yake da ilimi ya fi sanin yadda zai bunƙasa kasuwancinsa, to bare babban ma'aikaci, gwamnati kanta takan ƙimanta mutum ne da yanayin matakin karatun da ya taka, ba cewa muke kowa sai ya yi zurfi a karatun boko ba, amma iya karatun mutum iya inda zai tsaya, wanda ya tsaya a facin keke bai yalwata tunaninsa zuwa na babura da manyan motoci ba tabbas zai mutu a facin keke, domin iyakarsa kenan.

Wanda yake ganin yana da kayan facin keken ƙila yana buƙatar inji ne kawai da manyan sifanonin da za su taimake shi wurin kwance tayar mashin, sai ya fara tara kuɗin inji, ya sayi kayan aiki tabbas wata rana za ka ji ya fara facin babur, ƙila kuma ya bar wa yaransa facin keke, daganan zai fara saka wa mota iska ana biyansa masu motoci su fara zuwa a tsammaninsu har faci yana yi, daganan zai fara tunanin to me zai hana ya fara facin ma? Ƙila ya fara tattauna wasu batutuwa da masu facin mota ɗin, wata rana sai dai ka ji ya fara sayo kayan aiki, kafin ka ankara sai dai ka ga motoci har ya fara facin tayoyinsu, ya faɗaɗa tunaninsa kenan.

Duk abinda mutum yake sha'awa a rayuwa ya yi karatu kawai, kar ya damu da abinda yake karantawa idan ya saki layi tun farko, ya fara tunanin yadda zai kai ga burinsa kawai matuƙar yana tunanin cewa rayuwarsa ba za ta yi masa daɗi ba sai da cikan burinsa, na san wani babban ɗan jarida wanda kimiyar noma kawai ya karanta sai ga shi ya sami kansa a fagen jaridar da ya jima yana haƙilo, na san wanda addinin muslunci ya karanta, ba harshe ba bare a ce suna kusa, shi ma dai ya zama babba a harkar jarida yana gogayya da manyan 'yan jaridu a yau, na kuma san wanda ya karanta aikin likita kuma yana da buri game da harkokin addini, shi ma yau ɗaya ne daga cikin manyan mutanen da ake alfahari da su a duniya ta fannin ilimin addinin.

MAKALOLI MASU ALAKA:

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (9) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (10) Cikin Sauki

Karanta Hanyoyin Samun Nasara a Rayuwa (11) Cikin Sauki

Duk waɗannan sun cimma burinsu ne ta wajen karatu koda kuwa abinda suke nema bai yi dai-dai da karatun da suka yi ba, sai dai kuma karatun ya ba da gudummuwa gwaggwaɓa wurin cimma burinsu na samun abinda suke so a rayuwa, shi karatu ko ba ka riƙe biro ba, ba ka zauna a aji ba sunansa karatu, ba kuma za a taɓa haɗa ka da wanda bai yi ba har abada, kusan kowa ya san haka, shi ya sa in mutum ya yi kwaɓa za ka ji ana cewa "Ka ji, wai Dr kenan!" Duk kuwa da sanin cewa kwaɓar da ya yi ba a fanninsa ba ne, ma'ana karatun da ya yi bai taimaka masa da komai ba a wannan wurin.

Zamu Ci gaba Insha Allah.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin daɗin ku.

MURYAR HAUSA24 Kamfani ne mai zaman kansa domin bunƙasa harshen Hausa a duk sassan Duniya.

Burin Shafin MURYAR HAUSA24 zama babban shafi a Duniya da zai samu amincewar al'umma don Ilimantarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne da yake ƙunshe da abubuwan da suke da alaƙa da harshen Hausa da Al'ummar Hausa, sannan shafi ne da yake tafiya da Zamani da kuma tsarin Gargajiya na Iyaye da Kakanni, don Ilimantarwa da Kuma Faɗakarwa.

MURYAR HAUSA24  Shafi ne a Yanar Gizo da yake gabatar da shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla, cikin sa'o'i ashirin da huɗu Dare da Rana (24 Hours) ba tareda kakkautawa ba.

Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda Ku Kasance a faɗin Duniya.


MURYAR HAUSA24 Mun ƙudiri aniyar bunƙasa harshen Hausa  a sassan Duniya batare da nuna ƙabilanci ba, ta hanyar rubuce-rubuce da kuma sauraro (Audio) gami da kallan hoto mai motsi (Video).

Zaku iya aiko mana da Labari, Faɗakarwa, Tunatarwa, Ilimantarwa, Nishaɗantarwa, Wa'azartarwa da sauran su ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan adireshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

MungodeTURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user